← Book details Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 78

Sashe 3

Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Page.....4
feenat ce daure da towel gawani karami A hannunta tana goge gashin kanta da Alama daga wanka tafitoh wajen makeken bed din dake tsakiyar Dakin ta nufa, Leemah Leemah tashi kishiga nafitoh. Haba Feenat kaina Sai yayi ciwo ni kibarni da Asuba Nayi Leemat tafada cikin muryar bacci Feenat bata Kara bi takanta ba ta dakko wata doguwar Riga tasaka tajawo darduma tafara gabatar da nafilfili Raka'a 4 tayi ta daga hannu Sama tana kwararo addu'oeh take! Abinda ta Aikata dazun ya bijiro mata Azuciya kuka mai tsanani tashiga Rairawa Tana, Ya Ubangiji ka gafarceni Kan Abin nan danake Aikatwa ya Allah Kasani Nauyina kan iyayena yake wajibine Su magancemun matsala ta Amma Suka banzatar Dani gashi nafada kan turbar Shedan Ina Aikata Abu mafi muni Agareka, ya Sarki mabuwayi mai Shiryar da bawaYayin da yaso ya Allah Kashiryar da Zuciya ta Nasani nidin mai girman Zunubice gareka Ubangiji ya Allah badan niba ka gafartamun Zunubaina kakuma ganar da Mahaifana,,,,, ya Allah narokeka Dan girmanka Dan Albarkacin fiyayyen Hallita Ka yaye mun yawan Sha'awar nan Ka Kara daurani kan Hanya maidaidaciya......wani Kuka ne ya kwace mata 😵😵kuka take Sosai na nadama Abinda take Aikatawa,,,, Haba Feenat wan nan wani irin Abune kin Hanani bacci da ihun kukanki Leemat tafadi Rai Abace... Dan Allah Leemah kitaso Muyi magna feenat tafada cikin dashashshiyar murya Kinga ni ba'inda Zan Sakko kibarni nayi baccina tunda ke kika Jawoni, Abinda Zaki fada din yawuce kice kinyi Nadama Kuma Sau nawa kina Alkawarin kin bar lesbian,,,,,,wannan kukan naki dashi Gara babu ki tsaya idan Nadamar gsky Zaki kikai Zuciyarki nesa,,,,,,,,bare kuma Nasan ba nadamar bace Dan Wanda besan Halinki ba Shi Za'a ba labari. Toh nima dai NADEEYA ban San Halin Feenat ba kuma masu karatuma Zasuso Suji wacece feenat.......
SHIN WACECE FEENAT NE
Alhji Ibrahim dattijo mai dadtaku Tare da matarsa Nafisa Asalin fulanin yola ne Suna Rayuwarsu cikin jindadi da ganin girman Juna Sunada yawan Arziki SHANU RAKUMA da dai wani dabban kiwo na fulani Allah ya Azurtasu da haihuwar Yara 3 Nazir Shine babba Sai Aishatu Sai Sukai Auta Umar daga nan haihuwar ta tsaya musu, kusan kansu duk daya dan ita Nafisa Akai Akai take haihuwar ta, duk da cewa Fulanine Iyayen su basuyi kasa a quiwa wajen ganin yaran nasu Sunyi Karatun Islam dana Zamani ba, Sun taso da hazaka Nazir da Aishatu Aji daya Suke Inda suka wuce Umar da Aji daya,,,,,,, bayan Su Aishatu Sun Kammala Secondary dinsune Tasamu miji tayi Aure Anan yola inda yarage Nazir da umar wanda tun tasowarsu suke Son junansu Ahaka Nazir yaki ci gaba da karatunshi cewa Sai Umar ya Zana jarabawarshi ta Secondary Sucigaba tare,,,,,,,,,Masha Allah bayan lokuta Sun Samu addimetion Suka tafi makaranta a .A. B .U . Zariya,,,,, Hutu ke kaisu garin yola Suna matukar temakon iyayensu duk dacewa babu Abinda Suka nema Suka Rasa hutun Karshe dasukai Suka koma yola Anan ne Nazir yasamu mata yayi Aure yacigama da business Alokacin Aishatu tana da yara 4 duk Maza Anso Umar yafito da mata Ahadashi da Dan uwanshi yace Shifa Ina karatu mai Zurfi yake So yayi inda yasha banban da Sauran yan uwanshi kenan,,,,,,,Alhji Ibrahim bai cika takuraba indai wajen karatune Shiyasama ya Amince da Hakan, Umar kaduna yakoma don cigaba da karatunshi wanda da ker Nafisa ta Amince da Hakan yakanje ya dubasu Akai Akai, karatu yake Sosai wanda yasamu degree har biyu Anan ne ma ya yake Shawaran yafara business gun Wani Mahaifin Abokin Shi Alhji Aminu,,,,,,,,Suna gudanar da komai cikin Amana da gsky lura da Hakan ne watarana Alhji Aminu ya kirashi...... Umar badon komai na kiraka ba Nalurada irin Amanarka da Iliminka Da nagartarka Sannan Kwanakin baya dakuje yola da Sulaiman yabani labarin irin mutumcin iyayenka,,,,,,,,Don Haka na yake Shawaran Zan baka Auren Yata "Hafsat" Sai Asan nan Umar yadago Kai yace duk Abinda Ka yanke daidaine Baba Nasan bazaka taba cutar daniba Nayi matukar farin ciki duk dai Nasan cewa daman bazanji Kunya ba. Kaje Zanje yola muyi magana da Mahafinka Kafin nan Zaka fara Zance da Hafsa dan kufahimci Juna Yace toh Baba Alhji Aminu yaje yola Mahaifan Umar Sunyi farin ciki matuka Duk dacewa Sunso dan nasu yayi Aure a yola cikin yan uwanshi, Amma basu nunaba Sabida Alhji Aminu dattijon kwaraine bayan wata biyu Umar da Hafsa An fahimci juna inda Suke gudanar da Soyayya mai tsafta abinka da masu ilimi Acikin watan kuma Aka Saka Aurensu Ranar Wata juma'a misalin Karfe 10:00 dunbin mutane Suka Sheda Auren Umar Ibrahim da Amaryarshi Hafsat Aminu, Su Aishatu dasu Nazir duksunzo kaduna Kasancewar Agidan Alhji Aminu Ake gabatar da komai Hatta Su Hajiya Nafisa da Matar Nazir data haifa yara biyu mace da na miji duka suka dungumo Anci Ansha Anyi komai cikin Mutumci. Wani katafaren gida da Umar yagina A Unguwar Dosa Nan Aka kai Hafsa Gidane kato nagani nafada komai yayi👌

Bayan Shekara daya
Hafsace Zaune da katon Cikinta Tana duba wasu takaddu Sai rintse ido take tana cije baki daga dukkan Alamu batajin dadi Abun taga Saici gaba yake tayanke Shawaran kiran Mijinta Awaya. tana Sanar dashi yatawo Dan dama banisa yake da gidaba Sabi da ita kasancewar Soyayya Suke Sosai danko Sharokan Sai Haka lol Hafsa machace yar boko Ga Kyau Kota'ina ta hadu Ga iya Zama da miji Shiyasa Suke cin karansu ba babbaka. Yana ganin Halin da take Ciki ya temaka mata Suka Shiga mota Sai Asibti Cikin mintuna da bazasu wuce5 ba Aka fito da jariri Kato farisol kyakyawa dashi. Wayyo zokaga murna wajen masoyan nan biyu dama duk Wasu masoya nasu. Ahaka Aka Sallmesu Suka wuce gida cikin farin ciki Aishatu Ita tazo ta Zauna da Hafsa har'akai Suna Ranar Suna yaro yaci Suna NAZIR Sunan yayan dadyn shi kenan. Bayan watsewar taron Suna da dare yana Zaune Suna fira Ga yaronsu sun rungume daga yau dai Hafsa kin koma "Mumy" murmushi tayi tace kai kuma "daddy" ba Ahaka Zamansu yacigaba da tafiya... yaron yanada wayo Sosai Dan haka yana Cika 3years Suka Sashi makaranta dama gaba dayansu Burinsu Kenan yana kokari kuwa matuka Bayan yacika Shekaru biyar ne Mumy ta tashi da wani Zazzabi mai tsanani Ai ba bata lokaci Suka wuce Asibiti gwajin farko ya nuna tana dauke da Ciki Wata 4 Murna Sukai Sosai dawowarsu kenan daga Asibiti Aka kirashi daddy A waya cewa Allah yama maihafinshi Rasuwa gaba daya Nima danake Typing Saida naji Ajikina Kasancewar tsowo mai Mutumci yarigamu gidan gsky😵 Tuni Suka Shirya Suka dunguma yola Harda iyayen Hafsa watoh Alhji Aminu da Hajiya Amina mahaifiya gun Mumy Kenan. Sunje inda Achan wasu Sukayi dan koke kokensu bayan Kwana bakwai Kowa yadawo Akabar Inna Nafisa Achan Haka Suke kiranta. Sundawo gida lafiya inda mumy tacigaba da Rainon Cikinta daddy yana kula da ita.
Chapter 3 · 0% Book details