← Book details Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 78

Sashe 42

Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

duk girma da fadi irin na makarantar tasu feenah be Hana dandazon Matan Arewa Cikata ba. Matane Kota Ina daker kake Samun wajen dazaka Ratsa ka Shiga,Kasancewar taron gaba daya na matane,Inda daluban Xasu Shirya TAMSILIYYA(Drama) domin Su fadakar Akan Zaman takewar Matan Aure Agidan mazanjensu da irin kishin dasuke nunawa na Hauka kan kishiya. Kutsawa narinka yi domin Nasamu wajen daya dace na dauko muku yanda taron Zai kasance, Kai da dama ma live video Naso nai muku join Amma yawan mutane Inaaaa. Gaba gaba Nayi ganin tawarga Su mamy yasa Naja burki Anan kusa da inno na raba na Zauna,juyowa tayi tamun wani irin kallo ganin haka nai Saurin cewa Inno banida Alaka da Mufeeda fa. Murmushi tamun tace yanzu naji batu matso kusa domin kitayini fira Kafin Afara gudanar da jawabi. Matsawa Nayi kusa nace Inno banga yazeed ba ko lafiya.Tabe baki Tayi Yazo kin ganshi chan. daga kai nayi na hangoshi tsakiyar Nazir da yusuf fuskar nan a daure daga gani Hayaniyar da Ake ita ta takura Shi. Bangare guda kuma manyan malamai ne Na Sunnah wanda Ake jidasu afadin najeria, irinsu "Shek fantami, kabir gombe, Asadussunah da Sauran Su. Ayya inno yanzu kenan....Kafin nakasara ta dagamun Hannu Alamar ya isheta, Nima Shan kamshi Xan fara irin Nasu tsaka da feenah,Kafin Sudawo Nagama koya domin Abun da Sukemun ya isheni.ganin haka Nayi gum da ba kina Ina jiran Naga yanda Xa'a fara Abun. daga Kai nayi jin Ana kabbara Su feenah na hango jere kusan Su8 farin material dinkin doguwar Riga ne Ajikinsu, yayin da Suka daura dogon farin hijaf har kasa Masha Allah. Sun hasku kuwa. Tun kafin Su Xauna Naga feenah ta dafe kanta,Leemah ta tambaya besty lfy ko kanki ke ciwo? Wlh Leemah mutanen nan Sunmin yawa Anya Xan'iya tashi jifa mutane ga Hayaniya. Sorry besty Ki daure nan da 1h mun gama Insha Allah. Kada Kai feenah tayi Alamar toh. Cikin kan kanin lokaci wani malami yazo yafara bude taron da Addu'a. ya yaba kwarai da Hazakar Su feenah bangarin Boko,da islam Acewarshi be taba ganin babbar makaranta da'aka ware bangaren islam ba Sai wannan, Nan dai yagama Sanar da Abin da zeyi daga bisani ya Ambaci Leemah Amatsayin wacce Xata fara fadakarwa. fitowa Leemah tayi Anatse ta karasa tsakiyar wajen ta karbi Speaker. Nazeer na hango Sai wani Murmushi yake Ko mai yake fadi Aranshi Oho. da Sallam ta fara bayan Jama'ar wajen Sun Amsa tacigaba. (UMIRNA AN NAKIFA AMAMAKUM) " An umarceni dan na tsaya Agabanku, domin Nayi muku wani Dan jan hankali/wata yar Nasiha da Abunda naga matan Aure Sun fara mancewa ko kuma Sunakin Aikata Maganar Allah S W A da Abinda ya Aiko mazonsa Annabi Muhammad S A W dashi. Ayanzu mafi Akasirin matan Aure Sune masu Aikata babban laifi,Toh bari nafada miki yake yar'uwata kada Ki bari Azugaki kirinka dagawa ki tsaya Amatsayin da Allah ya Ajiyeki,ki Zauna dakin ki kada kifiye yawan yawo Kamar yadda Allah S.W.A. Yake Cewa (wakarna fi biyuti kunnah wala tabarrajina tabarrijal jahiliyatal Ula) MA'ANA kuzauna Adakinku kada kufiye yawan yawo irin Na Matan jahiliyya na farko. Ai wannan Abunda Allah yai mana gata yayi mana Kuma darajarmu Allah ya daukaka.domin Alokacin Jahiliyya mata ke biyan Sadaki,matan da da muke yawo tsirara wanda da birnesu Ake da Ransu,Alokacin Jahiliyya Mata Su Suke nemoma mijinsu Abinci,Alokacin Na miji yanada ikon ya Auri mace dari ko dubu,Alokacin jahiliyya mace Saita Sadu dana miji20 ko30 koma fiye da haka, har saita haihu Sannan Asamo wacce tasan kama da Sifa Sannan Atara Samarin nata Sannan adauko jaririn yana Hannu Anatafe Ana kallon Fuskar Samarin nata duk wanda yayi kama da Wannan yaron toh Shine uban Dan dashi Za'a durama Uwar yaron Aure! (MA'AZALLAH) "wannan kazanta har ina" Amma da Zuwan musulumci ya Ruguza yin hakan,yace mace yar'gata ce Kai Namiji kai Zaka nemo mata Abinci,Sutura,ilimi,lafiya da makamantansu.kuma Akace Shi Namijin Shine Zai bata Sadaki kuma Akace ta lullube jikinta ba'ayarda ta nuna tsiraicinta ba. Toh Mata kuna nufin Allah bai iyaba,Mazon Allah bai iyaba kuma musulunci bai iyaba??? Sai Ayanzu ne Wasu tsinanu, Fasikai, fajirai Zasu fitoh da mata suce Wai A inganta Rayuwarsu,Ai wannan Raini ne da wulakanci,Sai Ayanzu wasu Zasuce wai Asama ma mace kaykykyawar Rayuwa, wai duk Namiji ya Auri mace daya Kawai ta isa!😡 Toh Akwai Rayuwar data fi ta Allah da manzon Sa ne??? ko kuwa Akwai Rayuwar datafi ta musulumci? Abun bakin ciki Mu mata Shagalar tamu tayi yawa muda Akace kada mu bayyanar da adonmu ga mazajen daba namuba,Amma yanzu mata dazarar Zasuje unguwa,Zaka ga Sun dauki jan baki,jagira,hoda,eyeshadow, da dinki na Rashin mutumci mai matse jiki, Waishi Show me! ko follow me da mayafinta Akafada. ( wannan Sai a Instagram Zakaga mata da Shigar Nan kaya ya matsesu Ana juyi Ana daukar Video domin mutane Sugani Asan Ita mai kyauce) Toh Mazon Allah S A W yace( Nau'i biyu daga yan huta banga kamarsu ba! Wasu mutane ne Atare dasu Akwai bulalai kamar kunnuwan Shanu Suna dukan mutane da ita.da kuma wadansu mata da tufafinsu Amma matsairaita ne karkatattu idan Suna tafiya masu karkatar da hankulan mutane izuwa garesu,kawunansu kamar tozon Rakumi bazasu Shiga Aljannah ba,bama Zasuji kamshinta ba kuma kamshinta Ansamu ne daga tafiyar kaza Zuwa kaza.) Bama Wannan ne yafi bani haushi ba kamar yanda mata yanzu Suke illata mazajen Su,wasu Su kashe su,wasu Su konasu wai duk Dan Sabida basa Son kishiya! Toh wallahi tallahi idan muka yarda da Wannan Muna Aikata Son Ranmu muna Cikin bala'i da Musiba Mai girma. Dan haka manzon Allah S A W yace ma Sahabbanshi (kaifa bikum iza daga'imatikum Wa fasaka Shababikum) "yaya Zaku kasance idan matanku Suka rinka dagawa da Shishshigi, Samarinku Suka Zama fasikai?" Sai Sahabbai Sukace (Aya kuna Zalika ya Rasulullah?) "Shin haka Zai kasance ya Ma'Aikin Allah?" (Sai manzo yace musu fiye da haka ma Zai kasance)
Yau gashi muna gani maganar Mazon Allah S A W ta tabbata. domin gashi muna gani matanmu Na yanzu Saidai muce INNALILLAH WAINNAH ILAIHIR RAJI'UN! domin mace ce Zaka ganta ta tawo mayafi Akafada tasaka Chewingom Abaki tana tafiya tanaci Har Wani karairaya Zakaga tanayi tum barin Idan tazo majilisar maza har wani fari da ido Zakaga tanayi Wa'iyazubillah😭 kuma matar Aurece Zakaga taje gidan biki tacire dan kwali tana tikar Rawa Ita da yarta Ai wannan babbar musibace. Uwa'Uba yanzu mafi yawan Akasirin mata dabi'ar lesbian ita Suka maida Kamar Ruwan Sha! Leemah na kaiwa Nan kuka ya kwace mata, Saida tadanyi mai isarta tacigaba, da Matan kasashen waje Su Akasani da Wannan dabi'ar Amma yanz matanmu Na Hausawa Su Suke Aikata hakan musamman idan kahau Twitter Anan Suke Xuba video's dinsu idan Ka gani kai ka Rantse kace ba yaran Hausawa bane Innalillah Saidai kawai muce Allah ya gyara ya Shiryar da Xukatanmu. Daga Haka ta Ajiye Speaker ta bar wajen da dan Hawayenta. Malamar dake gabatarwa ta taso Masha Allah tubarakallah Malama Halimatu Ahmad mungode Allah yasaka da Alkairi. mata iyayenmu da yayyenmu da fatam kun gane Cewa Zafin kishi Hauka ne,domin ada mata bamuda Wani yanci Saida musulunci ya kawo mana, toh Kuma Dan Allah ya hallata ma maza Auren mace fiye da daya,muce bamu yarda ba Anya Munma kanmu adalci Anan???? Allah ya kyauta. Malamarmu ta gaba itace Kausar Hafiz malama bisimillah... domin nasan Kema bazaki Rasa Abin fadi ba.
Chapter 42 · 0% Book details