← Book details Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 78

Sashe 43

Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tasowa Kausar tayi daga inda take da'alama itama kukan tayi game da jawabin Leemah.Sallama tayi irinta addinin musulunci, gaba daya jama'ar wajen Suka Amsa. Tafara dacewa Abinda Malama Halimat Ahmad ta fada tafadi gaskiya,kuma ta kara Zaburar damu.dama ba wani Abu bane yake Rudarmu Mu Mata illah Rashin hakuri da dangana, da kwadayi dakuma Son kyalekyale na duniya. Shi yake Shagalatar damu harmu manta Xamu koma ga Ubangijimu. Wlh malama dazaki fita kiga Yanda mata Suke A hanya ke kya Rantse kice ko babu Sauran mace Acikin gida. Ayanzu Saiki Kasa gane wacece matar Auren wacece Mara Auren,domin Zaka gansu Sunci ado kuma babu lullubi Atare dasu.Toh mai tsira da Aminci Allah Su kara tabbata Agareshi yace!( mace tanada Sutura guda biyu.mijinta dakuma kabarinta) Amma Saika ga Uwa A zamanin nan tasaka yarta Agaba tana mata huduba wai don mijinta ya hanata Xuwa biki, Suna, ko Zuwa gida wankan jego😤toh wannan Hadisin Saiya tunamun da Wani babban Sahabin Manzon Allah S.A.W. yakasance Shi dakanshi yake ma yarshi Aure ya kaita gidanta,yayi Sallama da mijin nata yace ga yata Nan nakawo Maka Amana,kekuma idan kika fitoh kabarinki Za'a kaiki.Kuma tashiga ba zaka taba ganin tafito ba. Amma wannan Matan namu na Xamani dazaran Ka gansu Ahanya,kai Amarya Zasu,ko party,Ko Hinin Suna, ko kamun Ango.Wlh most especially batare da izinin mazajensu Suke fitowa ba.Toh yar'uwa mai tsira da Amincin Allah yace(duk mancen data Saba ma mijinta tsinuwar Allah da Mala'iku data mutane gaba daya ta tabbata Agareta) yar'uwa kodan wannan Abinda Allah ya fada ai kya Rage Wani Abu daga Cikin Halinki. MANZO YACE KUMA (Duk matar data mutu mijinta yana Mai yarda da ita Allah S.W.A Zai sakata Agidan Aljannah) Sannan manzo yana maiyimana gargadi Akan Kada mufita batare da izinin mazajenmu ba. ga dai Abinda yace (dukkan matar data fita daga gidan Mijinta batare da izininsa ba ta kasance tana Cikin fishin Allah S.W.A. har saita dawo ta nemi daya yafe Mata kuma ya yafe matan) Wlh wani Abu dayake Kara cimun tuwo A kwarya Shine,Saikaga maza Sun fita da dadi ba dadi Suna nema ma iyalansu Abinda Xasu ci,Kosu daura,ko suba yaransu,Amma su Rasa wanda Xasu ha'inta Sai mijin nasu,idan basu ha'inceshi ta wajen cefane ba Xasu ha'inceshi ta Wajen fita Un'guwa. Abin bakin Ciki Ayanzu Uwa Ita ke kashema yarta Aure,toh Dan Allah menene Rivar,Saikiga Andawo gida Anzauna Anajiran bazawari yazo mata,daga Anji Shiri na lokaci Saikiji anfara Xuwa Wajen boka, Wlh Malan yatace tunda Aurenta ya mutu har yanzu bata Samu Wani Mijin ba, inaganin tsohon mijinta Shi yayimata Asiri. Shikuma boka Dan iska makiyin Allah saikiga ya karkace yasata Ahanyar karyace karyace Kawai dan ya karbi Abin hanunta. Wai yaushe mata Zamuyi Hankali ne?kiduba mazanjenmu Xasu kawo mana kayan Abinci Kamar su Shinkafa,masara,wake da dai Sauran Su, Amma Saikiga mace ta iba tana boyewa wai dan kada mamarta tazo tarasa Abinda daxata bata wannan ai Sata ne Wlh.domin laifi kikaima Allah Sa'anan shi mijin Naki. Allah ya sawwake yasa mufi karfin Zukatanmu. daga haka kausar takoma ta Xauna. Wata daga Cikin daluban ta taso tayi gdy daga bisani tace Malama Khadija bisimillah.

Kallon feenah Kausar tayi Ashe Malan khady yasamu dayar? toh nimadai sai yanzu nagani Kausar.tafff bari Naji me yabata ta fada. Sallama itama khady tayima jama'ar wajen kamar Yanda taga Saura Sunyi.gaba daya taron wajen Aka Amsa.ta daura da Cewa Ni bansanma Mai Xanfada ba domin duk wa'inan malaman sunriga Sungama kwance mana Xani Akasuwa. Kallom Kausar Leemah tayi sukayi dariya,Lallai Malan Abinda yabata ta yayi daidai da yanayinta ne. Cigaba tayi Ku'inaganin bakusan Halin mazan Nan bane bawasu wanda Xa'a dauka Ayita tarairayarsu bane, da Zarar kinama Namiji ladabi da biyayya Abinda ma Xaifara Shiga tsakaninku Raini ne da wulakanci Harma yayi nufin yayi miki kishiya.kuma dakuke ta Wani fadin kar mufita kar mufita mu Zauna Adakin mazajenmu,Sukuma Mazan dasuke yawonsu Cikin gari fa? Har kuke kawo Hadisi da Aya wannan hadisan da Ayayoyin Ai bada matan wannan Xamanin Ake ba da matan Sahabbai ko Annabawa Ake. Kuma idan mace bata fita ta Neme yancinta ba yaushe Xata nema? Kullum tana daka Akulle kamar wata wardrobe waye Xai Santa? Kuduba Matan Sauran kasashe wa'inda kansu ya waye,inda Zakiga mace a Shugaban kasa ko Governor,kuma kuduba matanmu na wannan kasar Suma nan Zakiga mace a minister ko C M N,Ko Kuma Shugabar wata ma"aikatar. Amma kwa hada matan nan daku Wanda kanku yake Aduhu haryanzu baku waye ba?Ku bakusan duniya ta chanza ba kuna yawo cikin lullubi kamar wasu Munafukai😤wlh nidin nan dakuke gani n.a. tsakanina da namiji babu wata Amana domin shi ba dan goyo bane ba,ke matukar ma Naga Zaimun wata gargada sainace Ya Sakeni nikuma na bidi Wasu ga mazan Nan suna Yawo Kamar janfer a jos. Ni iya Abinda zan fada Kenan. Mai gabatarwan ce ta Amsa toh Allah ya kyauta Zan'Iya cewa kawai Anan. Malama Feenah Umar Faruk bisimillah. Yazeed da kanshi ke durkushe besan Sanda ya dago yana kallon yanayin yanda take tafiya Kamar batason taka Kasa.Subhanallah 1yr danayi kadai banga yarinyar Nan ba kalli yanda takara girma da Kyau dan tsaki yaja inama Ruwana da ita. Cikin natsuwa ta karasa Wajen..Sallama tayi Cikin Xaxxakar Muryarta Wanda ta dira Cikin kunnan yazeed! " She is So Cute nd She have a Nice Voice" Cikin Ranshi yayi maganar Amma Sai yaji Yusuf yace Allah ko? Kenan Afili Nayi maganar. Kallon Yusuf yayi yace yes kallitafa nadade inason wakokinta wayarshi ya Nuna mai Wata mace.dariya Abun yaba Yusuf Sosai yace Kawai ka Aureta. Tsaki Yazeed yaja yabar maganar. Magana feenah tafara. Haba malama Khadija Koda yake bakibani mamaki ba domin Kowa yasan Halinki da tarbiyarki. Wainan Abun da yan'uwana suka fada aiba kwance Xani a kasuwa bane, Gyara kayanka Ai baya Xama Sauke mu Raba.dakike cewa bamu San halin mazan nan ba toh kinsan duk Namijin dayake sonka baxai wulakantaka ba.domin Manzo S.A. W. Yace (duk Wanda baya kishin matarsa bazai Shiga Aljannah ba) kuma dakike maganar kishiya ai Allah bai Hana mutum ya Auri mace fiye da daya ba. Saurara kiji Abinda Allah S.W.A. ya fada Cikin Al'Qur'an *FAMKIHU MAZADA LAKUM MINAN NISA'I MASANA WA SULASA WA RUBA, FA IKIFTUM ALLAH DA'ADILU FA WAHIDATA AU MA MALAKAT AI MANUHU*! ( ku Auri Abinda yamuku dadi nadaga mata biyu biyu,ko uku uku,ko hudu hudu.idan kunsan bazakuyi Adalci Atsakaninsu ba toh ku auri guda daya kokuma Abinda hanunku ya mallaka na daga kuyangi) dan haka Malama Khadija Kinji Allah be hanasu Auren mata hudu ba,
Sadai idan bazasuyi adalci atsakaninsu ba.kuma dakike magana Akan fita har Kina cewa wai muhada kanmu da matan Annabawa kona Sahabbai! Kwarai kuwa dole mutun musulmi yayi koyi dasu, domin sudin iyayen Mumunai ne Kuma Su tsarkaka ne. Sayyidina Aliyu Allah yakara mishi yarda yace.... (babu yadda Za'ai mace tafita daga Dakin mijinta batare da wata babbar lalura ba,kuma idan ya kasance ma Xata fita tanemi Xanin baiwarta ko maiyi mata wanke wanke ta daura tayanda babu Wani namiji dazai ganta yayi Sha'awarta)Amma saikaga Matan Xamanin nan Idan Zasu fita unguwa Ansha ado Abinda batamawa mijin nata.
Kuma maganar dakike kan Sauran matan Kasashen dasuka Cigaba inda Xa'aga mata a Governor Ko wasu mukamai ai Manzon Allah yace duk jama'ar dasuka Shugabantar da mace baxasu Rabauta ba Ranar Alkiyama.kuma kince tsakaninki da namiji babu wata Amana dayayi Miki gargar Saikice yabaki takarda toh wannan Kuma Sai idan Kinyi Auren. Allah yasa mudace.daga haka takoma ta Xauna. Masha Allah jama'a suka rinka fadi yayin da Wata malama ta taso ta Rufe taron da Addu'a Su feenat Sun Samu kyauta masu yawa Dan Har kujeron maka Aka basu.daga Haka taron yatashi Cikin farin ciki. SU mammy Sun dau hanyar komawa Yayin dasu Leemah Sai Xuwa gobe.

Page...44
Chapter 43 · 0% Book details