← Book details Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 78

Sashe 40

Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Misalin 5 na yamma inno Suka karasa garin yola. gidan Alhaji Ibrahim Suka nufa gida mai tsohon tarihi da nagarta. Cikin farin Ciki da doki Inna Nafisa ta taresu. Cikin lokaci kankani iyalan Inna Nafisa Suka karaso gidan.nan Aka Zauna Anata firar yaushe gamo. Bayan Sunci Abinci Anhuta Yusuf Y yashirya domin komawa kaduna. Inna Nafisa ita ta dakatar dashi da Cewa Haba Dan nan Kamar Ana korarka Yanzu idan ka Kama Hanya kaduna dare Zai maka Sosai Kai baka tsoro garin nan ne? Sosa Kai Yusuf yayi Inna gobe inada Aiki Sosai A Office Shiyasa. Likita bokan turai kayi dai hakuri Xuwa gobe koda da Safe ne Saika tafi. Shikenan inna nabari Allah ya kaimu. Amin Inna Nafisa tace yayin da tashiga neman babban jikanta Kabeer (My Siriki😜) Akan ya Sama ma Yusuf wajen Kwana. Karasowa Kabeer yayi Cikin ladabi ya gaida Inno da fara'a ta Amsa yayin da ya juya ya mika ma Yusuf hannu.gaisawa Sukai Cikin girmamawa tunani Yusuf yashiga yi Cikin Ranshi" wannan Shine Kabeer din kenan. Ba laifi ya hadu daka ganshi kaga mai ilimi, gashi da kyau kasancewarsu Fulany, Ammaa Gaskiya nafison feenah ta Auri yazeed domin wlh sunfi dacewa Kuma ni inaganin Alkairi Cikin Aurensu." Katse shi Kabeer yayi muje ko. Ok.Ok. Yusuf Y fada Suka fita. Inno fira Suke Sosai da inna irin firarsu ta tsofaffi. Inno Cikin Ranta taso ta bar maganar daya kawota Xuwa gobe Amma Ina batajin Xata iya daurewa maganar takai gobe. Nikuwa Nafisatu wannan Shine kabeer din Dan wajen Naziru? Eh Shine Kinga yayi Saurin girma Halan, Haka yayan Zamani Suke Kiga tabarakallah da Anhaifosu Lokaci kankani kiga Sun girma. Gaskiya Kam Ainima mamakin danake Kenan, Shine Za'a Aura ma Takwarar taki kenan? Eh Shine da Zasuzo Nan da jibi kan maganar, Amma dazun Naji Nazirun yana cewa Zaiyi tafiya dan haka Abari Zuwa Nan da Sati biyu, Kinga Zuwa lokacin takwarar tawa ya Rage Saura Sati daya ta Kammala karatun nata. Kallonta Inno tayi Au kina Nufin yanzu Sun daga tawowar? Eh Sun daga ta. Madallah inno ta fada Cikin Ranta domin Abubuwan Suna Xuwa mata Cikin Sauki. Afili cewa tayi Ai kabir din daga ganin shi yaro mai Hankali ne,ga natsuwa Amma bansan me yasa me Sunanki bata Sonshi ba! juyowa inna tayi tace bata Sonshi Kamar ya? Wato basu fada miki gaskiya ba Kenan ko? Inno fadamun kinsan yaran nan basu dau tsowo da Muhimmanci ba. Aa kedai Nafisatu inaganin gara kiji daga bakinsu domin Abun ya shafeni Sai Aga Kamar Nayi Shishshigi. Kai Aminiyata Dan Allah kada kirufemun mana. toh shikenan bari kiji wannan komawar dasu Nafisatu Sukayi karatunsu, Kafin Su tafi tazo ta Sameni Tana kuka,lokacin ta dagamun hankali na matuka,Na tambayeta ko lafiya.Shine take cemun dan Allah na Sanar da mahaifinta ita batason Kabir tanada wanda take So, Nayi mamaki data fada Amma kinsan yaran Zamani idan basa son Abu Aka tilasta musu Nan da nan Saisu kama ciwo, dan haka nace mata toh waye takeso Wanda ya wuce dan uwanta. Budar bakinta tacemun wai yazeedu jikana dan Wajen Amadi! Nayi Salati nace ni bazan iya tunkarar Mahaifin ta da maganar ba domin Za'aga kamar Dan yazeedu jikana ne Shiyasa nakeson kashe maganar wancen Auren. Alokacin tagama magiyarta nace badaniba tayi hakuri ta Sanar da Umar da bakinta.toh kinji bansan ko tasanar dashi dinba. Haka yazeedu yanachan duk ciwo yake Anrasa gane Kanshi Saini dana san ciwon Son Nafisatu yake, dana fada ma iyayenshi Cewa Sukai ba haka bane wai Nafisatun da an tsayar da magana da dan'uwanta tayaya Za'ai haka. Dan haka na Sharesu ban kara magana ba Allah yasa Aurenta da kabeeru Shine mafi Alkairi ba shikenan ba! Sauke Ajiyar Zuciya innah tayi ikon Allah Ashe maganar da Nazir karami yazomun da ita kwanaki Gaskiya ce????yazo y fadamun cewa Nafeesat nada wanda takeso Alokacin nan banzatar da Zancen nayi. Allah Sarki inno ta fada Mai yuwuwa lokacin danace ta same iyayenta da maganar Shine ta kasa fada musu,Shine ta fada ma dan'uwanta. Da Sauri innah tace toh Aikuwa bazaiyu ba,Kafin Alhaji Ibrahim ya Rasu Saida ya gargadeni da kada nayarda ko bayan Ransa Ayima jikokinshi Auren dole, Hanya mafi Sauki gobe Zan Samu Naziru da maganar Asan yanda Za'ayi. Aa kedai Aminiyata tunda Anyi niyar Abu Kawai Amusu Aurensu. Aa inno ban yarda Ashiga hakkin yarinya.....Kabir daya Shigo yanzu ya katsesu. Xama yayi gefen kakarshi.inna da inno Naji Abinda kuke tattaunawa, Nima dama Nazo nafada muku damuwata, tun lokacin ina karatuna A London muka hadu da Wata yarinya Saida nasa Akaimun bincike Akanta kafin nafara Soyayya mai karfi da ita, dan Allah kutaimakeni ni ita nakeson Aure,nadade dasanin Feenah bani takeso ba domin wani Xuwa da baba yasani nayi naganta tare da yazeed dan haka banma karasa Ciki ba nadawo garin yola. Inno dakejin Kamar ta tashi ta taka Rawa tace haba kabeeru kuyi ma iyayenku biyayya Ku auri juna,Zakuga Albarka Abun Agaba. Inno inada wacce nakeso Kuma itama feenah tanada wanda takeso kuyimana adalci kuba Kowa Wanda yakeso dan Allah.dafashi innah tayi ka kwantar da Xuciyarka indai ina raye Sainaga burin kowannenku ya Cika. Tashi kaje ka kwanta.tashi Kabir yayi yana fadin Allah yakaro muku lfy. Amin innah tace ta dubi inno kinga Abun yazo da Sauki tunda Shima yaron yanada Matar Aure,kafin Naziru yatafi gobe Xan Sanar dashi komai. toh Ai Shikenan tunda kin matsa inno ta fada tana kokarin tashi,bari naje Na kwanta.Allah ya bamu Alkairi. Washe gari tunda Safe innah tasa Aka kira mata kawo Nazir babu Abinda ta boye game da maganar inno,takara dacewa Shima Kabir Ashe yanada wacce yakeso Achan turai Ya hadu da ita,Shiyasa tun lokacin banga yana murna da Zancen ba. Kaga Nazir kuma lokacinku babu wanda ya takuraku kan Auren dole Dan Haka Nakeson Yaran nan Abasu Zabin Xuciyarsu Suma. Shiru kawo yadanyi na lokaci daga bisani yafara dacewa.Innah ai hakan yayi daidai tunda yaran duk Sunada wanda Suke So, yanzu Xan fada ma Shi Kabir din yashirya kaimu gidan Su yarinyar domin Banason ya wuce nan da Sati Uku din dana Saka mishi. Shikuma Umar inaganin Kada ku fada Mishi Sai idan Lokacin Xuwansu yayi Sai Asanar dasu komai. Da Sauri inno tace Hakan yayi,idan Sukazo Sai kuce Kabeer yana da mata Shiyasa ka yanke hukuncin hada Nifisatu da yazeedu domin daman Anfada maka masoya ne. Toh Shikenan Mamah Inno Allah yakaimu lokacin yasa haka Shine Alkairi. Amin inno da Innah Sukace yayin da Kawo Nazir yamusu Sallama ya fita. Yusuf ne Yashigo domin yimusu Sallama bayan ya gaidasu yace ni Xan koma kaduna din. madallah Dan Albarka innah ta fada yayin data hadomai tsaraba Su man Shanu ta bashi yakaima Iyayenshi.godiya yamata Sosai. Yusuf Ai inaganin mukoma tare domin Ai na'isar da Zumunci dama Dan naga Mun dade bamu haduba yasa Nazo. Kai Haba Ya Zakice zaki tafi keda Zakimun Sati guda. Ni yar Sati Inno ta fada kedai dabakinson Zaman kaduna Ai Shikenan. Yazanyi naje na Zauna A kaduna bayan jikokina na nan Sunfi yawa. Toh Ai shikenan tunda Ni kinbarmin Umar yazama Nawa. tashi inno tayi ta hada kayanta! Kardai tafiya Xaki da gaske. Ah ah ha tafiya Xanyi mana. Toh Ai shikenan Sai idan nazo innah ta fada Yayin da ta hadoma inno Shatara ta Arziki. Sallama Sukai Cikin farin Ciki da kewar Juna. Yusuf yakama Hanyar kaduna. Cikin Mota Yusuf ya kalli Inno.Inno harkin gamane kika fasa Kwana biyu din?? Ahaf inno cefa Ai nagaya maka komai yazomun da Sauki yaron ma ya fada Cewa yanada Wacce Zai Aura,Kasan harcewa yayi yataba Xuwa kaduna yaga Nafisatu da tsaka suna Zance,Ashe dama Sundade Suna kulle kulle yaran nan! dariya Yusuf yayi yace bana fada miki ba Inno.Aikuwa Xanyi maganin munafurcin Su saidai Suji Ance inno ta hada Aranar Xan nuna musu Nasan duk kulle kullen dasuke. Uhum Yusuf yace."Cikin ranshi kuwa cewa yayi kodai ni nake musu kulle kullen ba" Fira Sukayi tayi inno da Yusuf irin girmamawa da kakar Nafisat da karamci irin na fulanin yola Abun sai San barka kawai.
Chapter 40 · 0% Book details