Sashe 47
Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Mutuwar tsaye Su Abba Sukai A wajen.Sundai Ga bakin feenah na motse Amma babu wanda yasan me take fada. da Ker Abba yasamu yace mukoma Ciki,dukkansu Sukai Ciki banda Leemah daketa faman daukan Su feenah pic,ganin feenah ta tawo yasa itama tayi Ciki. Yazeed da idonshi ya kada yakoma jaaaa kasa motsa kafarshi yayi,gaba daya feenah ta kashe mai jiki,bangare daya yana jin Nauyin Hada ido da iyayenshi,yarinyar nan ta kasheni,ta Aikata laifi ganinsu Inno gaba daya tamaida laifin Kaina.da ker yasamu yaja kafarshi yayi parlon Cikin fargaba.Shiga yayi ya Zauna kamar yanda yaga kowa A Xaune. Saida Shiru ya biyo baya nadan lokaci daga bisani Abba ya kalli Mamy kutashi mukaisu Airport din ko. tashi Sukai gaba daya inno ba karamin Haushi tajiba ganin Ba'Ayi maganar data so ba. ita tafara yin gaba tana fadin Oh ni Inno yaran Zamani Saidai Abarsu Idan Sunason junansu da Aure iyayensu Suka kasa fahimta Sai lalata ta biyo baya. Sumbatar juna ikon Allah. Gaba daya wajen kunyar maganar da inno take Sukeyi,Amma ba wanda ya'isa ya tanka dan Sungane Su take Azauna Ayi maganar. Dan haka Suka Nufi harabar gidan tana fadin Anan fa Suka tsaya Ana Sumba Ni inno kada dai Suje Suyi Aika Aika. Yazeed da gaba daya inno ta gama Kular dashi kusan Atare Sukaja tsaki tare da feenah. Aikuwa kamar jira inno take kunma iyayenku tsaki tun farko Saida nafada muku Ku fadi Gaskiya Baku fadi ba.yanzu kuna Sumbatar juna Ai Abinda Zakuyi Nan gaba Saiya fi haka. durkusar da kai kasa feenah tayi tana data Sanin Abinda ta Aikata,Sai yanzu ta gano Cewa inno wani Shirin ta mata yasa daxun tazo tana lallabata. babu wanda yakula inno haka tarinka Sababinta. Mota biyu Sukai Zuwa Airport. Motar Abba ne Agaba inda ya dauki Mamy Agaba baya kuma feenah,Kausar,Leemah Sai Twins. Motar Dad dake baya kuma inno ce Agaba Sai Mum,Nazeer,yazeed Sai yusuf Ahaka Suka karasa babban airport dake garin kaduna. Suna karasawa baifi da minti30 ba Akafara kiran Suna. yusuf dariyar mugunta yake domin yasan yanda ya hada Zaman Cikin jirgin. Kausar Akafara kira tashiga bayanta Yusuf ne. Inda Suka Zauna Awata kujera ita tana Ciki wajen window yayin da Yusuf ke gefenta. Kallonshi tayi My Yusuf Kaine kashirya Hakan ko? Murmushi ya mata ya lakaci hancinta yes my wife Sabida muyi fira Sosai nayi Hakan.ba'a wani juma ba Leemah da Nazir Suka Shigo.dayan bangaren Suka Zauna inda Suke seat daya dasu yusuf.Murmushi duk Suka sakar ma junansu. Akasa Najiyo inno nafadin Amma yan Company din nan Basuyi hadin nan daidai ba Amadi,! Karfa tsaka ya matse Nafeesatu a lungu Gara kusan Abunyi.tsaki Yazeed yaja yayi Shigewarshi Cikin jirgin.yayin da feenah tabi bayanshi. Chan karshe ta wuce kowa taje ta Xauna. Saida Akai wasu mintuna wata mata tazo kusa da feenah,Sister idan bazaki damu ba Zance miki wanann wajen Zamana ne. Kallonta feenah tayi tace Ok tashi tayi tana neman Wajen Xama Amma duk da mutane.gashi lokaci daya Aka fara Sanar da jirgi xai tashi. Ba yanda Xatai takoma kusa da yazeed ta Xauna. Tabe baki yayi lokaci daya Kuma ya tashi tsaye ban hanya ya fada rai Abace.matsawa tayi da Sauri Amma duk da haka Saida ya taka mata kafa da karfi.Runtse ido tayi tanajin Xafin wajen,dallah malama Shiga Ciki kiban Nan. Matsawa tayi Ciki hawaye Na Xuba kan face dinta. Ahaka duk Suka Saka belt jirgi yatashi. Allah ya tsare duk yan wajen Suka fada banda inno dake daga ma jirgin Hannu tana fadin tsaka yatafi. Da Haka Suka koma Cikin motoci Sukabar airport din. Su Abba na karasawa duk Suka Zube a parlo.dama Alhaji Umar Faruk Abinda yasa nace kada kuhuce Ku biyo ta nan inason Nace maka kashirya gobe Muje Yola Kan maganar feenah da Kabeer. Kwarai Nima nayi tunanin Haka dad ya fada. Da Sauri inno tace Ku kuwa kunada Hankali? Bakuga Abinda yaranku Suka Aikata daxu bane da bazaku basu Abinda Suke So ba.ko Kuma haka Akai muku? Toh indai n.a. isa daku kubi Xabin yaranku ba Son Ranku ba.daga Haka tayi gaba tabar parlon. Kallon dad Abba yayi Kada kadamu Alhaji Faruk Kasan girma yazo mata.murmushi dad yayi yace Allah dai yakaro musu tsawon Kwana mai Albarka.Amin duk Sukace daga bisani Su mum Suka tashi.Toh Fatima Zamu tafi.Kai Hafsat kibar Twins mana Su Kwana biyu. Kuma Ai ban kawo musu kaya ba.kada kidamu yanzu Xan fita Nasiya musu. Toh Ai Shikenan gasu nan Asha hutu lfy.