Sashe 27
Yar Lesbian Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Yusuf A birnin Zariya! besha wahalar kai kanshi gidan Su Kausar ba, Tunda dama location ta tura mishi. Kiranta yayi Ya Sanar da'Ita ya karaso. Me gadi tasaka ya Shiga dashi part din da'aka tanada dan Saukar baki, ba karamin kayata wajen Akai ba dan Yusuf tsayawa Kawai yayi yana kare ma babban parlon kallo. bama Sai angaya maka gidan Sara dubai kazoba. Zama yayi adaya daga kujerun da'aka Zagaye parlon dashi gabanshi fruits ne makil. Wata yar matashiyace tashigo Sanye da uniform da Alama Aiki take Agidan, daret wajenshi ta nufa ta mai Sannu da zuwa amsawa Yayi, Kausar din tace tanazuwa.toh yace. Tafara yayyanka mishi fruits din daga bisani ta fita. Ba'afi mintina10 ba tsakani Saiga Kausar tashigo face dinta dauke da Murmushi, Sanyi take cikin wata doguwar riga Arabic gown ce mai launin Brown, red din mayafi tasaka ta Zagaye Saman kanta dashi yayinda takalmin kafarta ya kasance Jane, dankunne da Sarkar wuyanta zuwa Abin hanunta suma duk jane.ga Wata kwalliya data tsantsara kamar Zata zaben sauraniyar Kyau...tsayawa Yusuf yayi yana kallonta Gani yake kamar ba kausar ba domin gaba daya ta chanza mishi. Iskar data hura mishi a Ido ita ta dawo dashi Cikin hankalinshi. Tashi yayi tsaye yana facing dinta. Kinyi Kyau my Kausar, Murmushi tayi tace Tnx my Yusuf. Zama Sukayi Atare tana mishi ya Hanya. Waye ya gayamiki masoyi na ganin Akwai tafiya Xuwa wajen masoyinshi. hakane kuma Sweetheart bakaci Komai ba. Inajiran kizo kibani, karka damu Soon. Kinsan yau gaba daya nazo da Shirina, domin ni Ayanda nake Ayanzu baki Adaura mana aure Ayau Natafi dake ba. dariya kausar tayi Sosai tace kacika Xumudi. Kece kike ganin haka yusuf ya fada Yana daukan Ayaba dake kusa dashi. Kawo na bare maka ko. No Indai kika bare kece Zaki bani dan haka kawai na hutar dake. Haka sukaciga da firarsu Cikin kulawa da Nuna Soyayya tsantsa, ta Yanda kowannesu yake ganin bazai iya rayuwa ba dayanshi ba. bari nakira maka Su Hajiya Ku gaisa, Kina nufin daddy ma Yana nan? Eh mana. Gyara Zama Yusuf yayi yace gara dana Saka manyan kaya kuma nazo da Shirina.dariya Kausar Ta fita tanayi. Ba'adau Wasu lokutaba Iyayen Kausar Suka Shigo Cikin parlon. Yusuf Na ganinsu ya Sauka kasa yana gaidasu, Cikin Nuna kulawa Suke amsa gaisuwarshi, yayinda mahaifin kausar yace yarona katashi ka Zauna daidai.kara durkusar dakanshi yusuf Yayi Kasa bekuma Tashi Ba.mahifan kausar Sunji dadin irin tarbiyarshi matuka.dan haka mahaifin kausar yafara magana kamar haka. Hakika na yaba da hankalinka Yusuf kuma Nayi matukar farin Ciki Game da Zaben miji nagari da yata tayi, dama nadade ina fatan Hakan. Allah yamuku Albarka gaba dayanku. Amin yusuf ya Amsa kasa kasa. Cigaba mahaifin kausar yayi, idan kashirya Zaka Auri yata katuro mun magabatanka Cikin Satin nan Asaka Ranar biki Zuwa Sanda yata Zata karasa karatunta. Wata Shida ya Rage ta karasa.koya ka Gani Yusuf? Baba Yanda kace nima haka Nayi tunani Zuwa jibi Zan Turo magabatana Ngd Allah yakara girma. Amin mahaifin kausar yace. Madallah da samun d'a nagari irinka ina alfahari dakai Yusuf mahaifiyar Kausar ta fada. Ngd mama. Tashi Sukai suka fita. Yusuf na ganin Sun fita yatashi tsaye Hannu yadaga Sama yana gdy ga ubangiji mai wanzar da farinciki Cikin Zukatan bayinsa. Ahaka Kausar ta Shigo ta sameshi Sanarda ita komai yayi Akan yanda sukai dasu Hajiya itama farin ciki tanuna Afili Ahaka Yusuf ya sanar da ita maganar su Yazeed kamar yanda ya Sanar da inno, Cikin ranshi yana rokan Allah ya yafe mishi game da karyar dayayi, So yake ya hada Sunnar mazon Allah S.A.W. tsakanin mutum biyu wanda yake hango babbar Alkairi cikin Al'amarin. Afili Cewa yayi Kausar mu hada guiwa mu hudu ni dake da Nazir da Leemah Mu hada Yazeed da Feenah aure Nasan Inno Zata Kara mana hikima shiyasa na fada Mata. tunani Kausar take ya'Akai feenah ke Soyayya da Yazeed bayan Feenah Sam Bata jituwa dashi, Kawai nasan Yusuf ne keson hada wannan Auren,toh komadai yayane nima Zanyi farin ciki da hakan Tunda ba karamin dacewa feenah tayi da yazeed ba....kikai Shiru Sweetheart! Ba Shiru Nayi ba naji dadi hakanne matuka Kuma Zamusan yanda zamuyi. Inasonki my kausar kinada fahimta. Murmushi tayi tace kamarka ba tunda kaine ka kawo zancen. Yusuff saida ya kwashi lokaci mai tsawo tukun yabar garin zariya kan Cewa jibi Zai turo iyayenshi.
Page.....32
Page.....32