Sashe 9
Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ce"Wallahi ko za ka kwana kana musawa ba zan yarda da kai ba".
Ya ce"To ai shikenan, sai ki É—auki matakin da kika ga ya dace, amma ba zan É—auki shirme ba. Ya fice daga É—akin
ÆŠakinsa ya shiga ya zauna, ya kira wayar Zahran, ko gaisawa ba su yi ba ya ce"Ke dama kin zo kin yaudare ni ne don ki haÉ—a ni da matata?"
Gabanta ya faÉ—i ta ce"Me ya faru my love?"
Ya ce"Kar ki sake kirana da wannan sunan, domin na rufe babin soyayyarmu daga yau, ta ya aka yi matata ta san na siya miki gwal? Alhalin kin ce ko Æ´an gidanku ba za ki sanarwa ba?"
Ta ce"Wallahi ban faÉ—awa kowa ba, sai dai..."
A tsawace ya katse ta da faÉ—in"Sai dai me? So kike ki sa mutuncina ya zube a idon duniya da Æ´an unguwa ko?"
Kamar za ta yi kuka ta ce"Ka yi haƙuri".
Ya ce"Ke kin ga, haƙuri ke ya kama ba ni ba, kuma daga yau kar ma ki sake nuna kin san ni, kawai mun rabu har abada!".
Ta ce"A'a don Allah, ba mu yi haka da kai na fa, mun yi alƙawari..."
Ya ce"Ke da alƙawarin kun ci ubanku! Wallahi idan kika sake nuna kin san ni sai na tona miki asiri, sai na hana ki aure a garin nan".
Daga haka ya katse wayar, ya saka ta a black list, ya kuma yi alƙawarin ya bar ta har abada, ai babu laifi ya more ta sosai kamar matarsa, a tsakanin nan ta taimake shi sosai, ba ya kula kowace mace sai ita, don haka yanzu sai dai ya canza sheka ita dai ya gama da ita.
Washegari sai ya wuni jiki a mace, saboda ya ga Fatima ta ƙi sakin jiki da shi, sai ɓata rai take yi, duk da ba ta sake tada masa da zancen ba amma abun ya dame shi, don haka da daddare ya ɗakko kuɗi dubu ɗari biyu ya ba ta, ta kalli kuɗin tana cewa"Wannan kuma fa?"
Ya ce"Kawai ba ki na yi ko za ki sayi wani abun".
Ta ce"Ok kenan na toshiyar baki ne ko? Tun da na san ka siyawa kwartuwarka gwal".
Ya ce"Haba Nana, ke me yasa kike haka ne? Da ba na ba ki kuÉ—i?"
Ta ce"Kana ba ni amma ba mai yawa haka ba".
Ya ce"Kuma kenan ba kya so na fara ba ki".
Ta ce"Ni dai ka ji tsoron Allah".
Ya ce"To in sha Allah, amma fa wallahi wannan sharri aka yi mini".
Ta ce"Ni dai a bar zancen kawai, raina ƙara ɓaci yake".
Ta É—auki kuÉ—inta ta je ta adana.
Tun daga lokacin magana ta mutu, Fatima ba ta sake zuwa gidan Umma ba, ta ɗauke ƙafa cak ta daina kai yaranta, tun Umma tana yi mata aiken ko lafiya? Har ta fara zuwa da kanta, sai Fatima ta yi ta sha mata ƙamshi, ko kuma da ta shigo saa ta ce mata fita unguwa za ta yi, hakan ya sa Umma ta rabu da ita, suka yanke alaƙa gabaɗaya, ita Fatima gani take ƙarya ne a ce Umma ba ta sani ba, haɗa baki suka yi kawai suka yaudare ta, ita kuma Umma tana ganin ba ta yi mata komai ba akan me za ta canza mata fuska? A haka suka rabu.
Babu laifi hankalin Fatima ya kwanta, tun da bai sake tada zancen aure ba, sannan ya rage yin waya da mata a gabanta da firarsu, sai ta yi zaton shikenan ma duka ya rabu da su, suka cigaba da zama cikin zaman lafiya, suna farantawa juna, a haka har ta samu wani cikin ta haifi É—anta na uku, shi ma namiji ta haifa.
Tun da cikinta ya tsufa take gudun Usman, ta rage ba shi hakkinsa, haka zai ta bin kanta yana kiranta tana ƙin zuwa, har dai ya jingine ta a gefe ya daina kiranta, ya koma harkarsa ta neman mata, dama ba dinawa ya yi ba, ya dai rage ne kawai saboda yana so ya daina ɗin, sai dai idan ya ji marmarin wata sai a ɗan taɓa, amma tun da ta fara gudunsa sai ya koma ruwa tsundum.
Ranar suna aka yi taro aka gama lafiya, kowa ya watse sai ƙanwarsa, yayarta da ƙanwar babarta da suka zauna za su kwana a gidan, don suyar naman suna washegari.
A ranar ne kuma Usman ya haɗu da wata yarinya, wacce abokinsa ya yi masa hanya, har ya biya kuɗi za ta zi gidansa su kwana tare, don ita a ƙa'idarta ba ta zuwa hotel sai gida, tun a waya yarinyar ta gama ruɗa shi, duk ya susuce ya matsu dare ya yi ya ɗakki ta, hankalinsa a kwance yake, saboda ya san babu mai shigo masa ɗaki, tun da dai Fatima ta daina shiga tun kafin ta haihu.
Ana idar da sallar isha'i ya dawo gidan, yarinyar tana bayan motarsa, haka ya ajiye motar ya fito, sai dai ransa ya ɓaci ganin mutane a tsakr gidan, don ba a ɗora naman kai da wuri ba, ba a gama dafa shi ba.
Ya shiga É—akin Fatima yana cewa"Ni Fatima me ake dafawa haka da tsohon daren nan?"
Ta ce"Naman kai ne, ba a babbako shi da wuri ba".
Ya ce"Amma babu gas ne da za a zo a tisa murhu da daren nan kamar wasu aljanu?"
Ta ce"Akwaa gas, kawai dai ganin ga icen nan, ga kuma murhun da aka yi girki É—azu shiyasa aka É—ora a nan É—in".
Ya ce"Gaskiya ni ba na son haka, a ɗauke shi a mayar gas kawai ko a haƙura sai gobe a ƙarasa".
Ta ce"Ya kusa dahuwa fa".
Ya ce"To amma zaman me suke yi a bakin murhun? Su dawo É—aki mana".
Cikin ƙosawa ta ce"To idan sun zauna mene ne? Iska suke sha".
Ya ce"Ya ga Ac a É—aki ki ce mini wai suna shan iska?"
Ta ce"To ka je ka faÉ—a musu su bar maka tsakar gidanka".
Ya ce"Ni dai ba da wata manufar na faÉ—a ba, kawai gani na yi a ce mata kun wuni aiki kun gaji kuma dare ya yi ba za ku kwanta ku huta ba?".
Ta ce"Sai kuma ka yi".
Ya koma motar ya shiga ya rufe, yarinyar ta ce"Ni fa na gaji da zaman mota, wai ya ake ciki ne?"
Ya ce"Yi haƙuri kin ga ba su bar tsakar gidan ba ne, amma sun kusa gamawa".
Ya fito ya shiga ɗakinsa, yana leƙe ta windo, yana ganin sun shiga ɗakin ya fito ya shiga ɗakin, suka sake gaisawa yana cewa"Sannunku, kun gama aikin ko? Kun sha aiki, akwai lemo a firjin nan kuwa? Bari na ɗakko muku ba falona ya fi sanyi".
Ya juya ya tafi ɗakinsa ya kwaso musu lemo ya kawo, ya ce"Ai kun gama da tsakar gidan nan duka ko? Ku dai rufe ƙofar ɗakin nan don Allah a saka sakata, Allah Ya tashe mu lafiya".
Suka amsa da amin, ya sake shiga ɗakin Fatima ya ce"Ga lemo can mai sanyi na kwaso muku daga firjina, ba kya buƙatar komai dai ko? Ki kwanta ki huta na san duk kin gaji".
Fatima ta ce"To".
Sai dai tana mamakin wannan kulawar da yake nuna mata, a iya saninta haushinta ma yake ji, saboda gudunsa da take yi, har jiya ba ya sakar mata fuska, amma ta ga yau komai ya canza.
Ta fito falon inda suke kasa naman, kamar an ce ta leƙa ta windo, ta hango shi yana ta hange-hange kamar mai neman wani abu, sai kuma ta koma ɗaki, kawai sai ta ji ba ta yarda da shi ba, don lokacin har ya shigar da yarinyar ɗakin, yana son ta babbatar da babu wanda ya ganta ne.
Aka zuba naman Usman ta ɗauka ta haɗa da abincinsa za ta kai masa, lokacin yana wanka, bai fiya rufe ƙofa da wuri ba, amma yau da ta tura ta ji ta a rufe, ta ƙwanƙwasa ta ji shiru gabanta ya fara faɗuwa don kai tsaye ta fara zarginsa, ta dinga bugawa babu ƙaƙƙautawa, bai ma gama wankan ba ya fito, gabansa yana faɗuwa ya ja hannun yarinyar ya kai ta ɗakin gado ya janyo ƙofar, sannan ya je ya buɗewa Fatima, yana cewa"Lafiya? Me kike yi ba ki yi bacci ba?"
Ta ce"Abincinka na kawo maka".
Ya ce"Ni wallahi a ƙoshe ma nake, na tsaya a gidanmu na ci fa".
Ta ce"Ka dai ƙara".
Ya karɓa don kar a ja maganar, ya koma ciki ya rufe ɗakin tana ji ya saka sakata, hakan ya ƙara ƙarfafa mata zarginsa, saboda idan ta kai masa abinci ba ya karɓa sai dai ta shiga ciki ta ajiye, kuma yana so ma ta shiga ɗakin nasa ta zauna yana ci suna fira, sannan sai dare ya yi sosai yake rufe ƙofa.
Ta koma ɗaki ta kasa nutsuwa, can anjima ta kira ƙanwarsa gefe, da yake suna da kyakkyawar alaƙa ta su ta zo ɗaya, kuma sun saba firat neman matansa da ita, sai ta faɗa mata ita fa tana zargin da wata a gidan nan, Hasana ta ce"Tabɗijan! Da mace a gidan nan? Kuma har kika iya tsayawa kina ba da labari ba ki ɗauki mataki ba?"
Fatima ta ce"Ai na kira ki ne don ki taya ni ɗauka, amma za ki laɓe daga nan, idan kika ji na yi kabbara to zargi ya tabbata sai ki shigo mu ƙaddamar musu".
Hasana ta ce"Bari na ɗakko taɓarya, ke kuma sai ki riƙe muciya".
Fatima ta ce"A'a ba kashe ta za mu yi ba, rufa min asiri, ki É—akko muciyar dai ni kuma ki ciro mini wayar jikin TV".
Hasana ta je ta ɗakko, sannan Fatima ta nufi ɗakin nasa, ta ƙwanƙwasa, lokacin yarinyar tana zaune tana cin abincin da aka kawo masa, shi kam ba shi da nutsuwar ci, burinsa ta gama ci su hau aiki kawai.
Ya ce da yarinyar"Shige cikin ɗaki, ƙila matata ce"
Yarinyar ta yi tsaki ta ce"Amma dai wannan matar taka an yi Æ´ar wahala wallahi".
Tana tsaki ta É—auki kwanon naman ta shiga É—akin gadon ta zauna ta cigaba da ci hankali kwance.
Shi kuma ya je ya ce"Wace ce?"
Ta ce"Ni ce mana".
Ya ce"To mene ne?"
Ta ce"Lemo za ka ba ni".
Ya ce"Wane kala?"