← Book details Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 15

Sashe 5

Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin tsakanin nan ta linka kulawar da take ba shi sosai, wai ko hakan zai sa ya fasa, sannan tana yawan jansa da firar ƴan matan nasa ko za ta ji a inda batun auren ya kwana da kuma kalar wacce zai aura, amma ba ya babta fuskar da za su yi firar, a haka har sati ukun da suka tsara za ta koma sabon gida ta yi, duka ya canza mata kayan ɗaki, ya siya mata wanda suka fi nata tsada da kyau, sannan ya ba ta kuɗi ta ƙara wasu kayan kitchen ɗin, ta tare a sabon gida tana farinciki sama-sama, ƴan'uwa kowa ya ga yanayin ginin sai ya ce mata ta shirya zuwan ƙanwa, wato kishiya, sosai hakan yake sake hasala ta, amma tana da daurewa tana nuna ba komai ba ne a shirye take. Kullum daidan ta kalli part ɗin da amarya za ta zauna sai ta ji kamar ta rushe ginin, saboda yadda zuciyarta take yi mata ƙuna, amma abun da sauƙi tun da dai ta ga bau sake tada zancen auren ba.

Komawarta sabon gidan nan ya zama wani cigaba a rayuwarta, saboda unguwa ce ta masu kuɗi, kuma akwai yaran mata masu irin shekaratunta, wayayyu ƴan gayu, hakan ya sa ta shiga cikinsu tana ta samun ilimin zama da miji, da kuma sirrikan girki da na gyaran jiki, nan da nan ita ma ta waye sosai ta zama gogaggiya, yanzu Fatima babu batun ƙazanta tana gyara kanta da gidanta sosai, tun tana yi don kar ƙawayenta su rainata har ta fara yi don kanta, saboda ta saba, kuma sosai hakan yake yi wa Usman daɗi, don yana son tsafta da gayu, amma sam hakan bai sa ya ji wai zai fasa ƙara aure aure ba, don wannan ra'ayinsa ne.

Akwai wani gida da ta fi sabawa da su, matar gidan za ta haife ta, don tana da manyan yara, ta fi zuwa gidan, su yi fira kuma dayake ta shiga islamiyyar ta magriba, can take kai yaranta Mu'az da Khalil, sai su zauna har ta dawo daga makaranta, don sun saba da gidan.

Sai da ta sakankance ya bar zancen auren, rama ɗaya kawai ya zo ya zaunar da ita, yake cewa"Nana kamar yadda a baya na sanar da ke ina da niyyar ƙara aure, to yanzu maganar ta tashi, ina son yin aure, amma don Allah ina so ki kwantar da hankalinki, na faɗa miki wannan auren kawai ra'ayina ne, ɓangarenki da ban, nata da ban, don haka ban ga abin da zai haɗa ku faɗa ba".

Fatima ta jinjina masa kai alamar gamsuwa.

Ya ce"Ba ma ƴar garin nan ba ce yarinyar, wallahi a status ɗin abokina na ganta, ƙanwarsa ce, rabo dai kawai na ji ta yi mini, zuwana zance biyu sai ta waya muke gaisawa, to jiya an ce na tura iyayena, nan da kwana huɗu in sha Allah zan tura, za a tafi da kuɗin auren a saka rana kawai, tun da na shirya ba wani tsayawa ɓata lokaci".

Fatima ta ce"Hakane Allah Ya sanya alkhairi".

Ya ce"Amin, na ji daÉ—i da kika fahimce ni".

Ta yi murmushi ta ce"To ai ya zama dole na fahimce ka, tun da ba ka yi mini rufa-rufa ba".

A ranar bacci rabi da rabi ta yi, ta gama yanke hukuncin da za ta ɗauka tun kafin zuwan ranar nan, akwai ƙawarta maƙociyarta wacce tasu ta zo ɗaya sosai, ita ce ta ba ta shawarar da za ta bi, ta faɗa mata ita Malaminta ne ya hana mijinta ƙara aure, aikinsa kamar yankan wuƙa yake, duk auren da ya ɗakko tana zuwa wajen malamin nan cikin kwana biyu magana take lalacewa, a haka har ya gaji ya daina neman, don haka ita ma ta yanke hakan za ta yi, domin a ganinta ba ta da sauran dabarar da ta wuce wannan ɗin, saboda alƙawari ta yi ba za ta zauna da kishiya ba.

Washegari da safe yana fita, ta shiga gidan ƙawarta, har da kukanta ta zayyana mata komai, Zulaiha ta fashe da dariya ta ce"Kuma ke maman Mu'az mene ne abun kuka? Ko dai ba ki shirya zuwa wajen Malamina ba ne?"

Fatima ta ce"Wallahi tun kafin na ji Malaminki ni ma ina da niyya dama, don na zauna da kishiya gara a ce na kauce hanya, ai Allah gafurur-rahim ne".

Zulaiha ta ce"Ƙwarai kuwa, da zarar kin yi istigfari shikenan, don haka ki ɗaura belt, yaushe za mu je?"

Fatima ta ce"Ai ni ko yau ma na shirya wallahi, ba na so ma a kai ga kai kuÉ—in auren, gara a fasa tun kafin manya su shiga ciki ya ji kunya".

Zulaiha ta ce"Da fatan dai kina da kuÉ—i ko?"

Fatima ta ce"Ina da shi, mu je kawai".

Nan suka tashi suka kama hanya, cikinsu babu wacce ta tambayi mijinta. Babu wani nisa tsakanin gidan malamin da unguwarsu, kuma gidana ne gidan aurensa da matansa biyu, ɗakin da yake aikinsa kuma yana farkon gidan cikin zaure, suka shiga da sallama, yana ciki a zaune cikin shigarsa ta alfarma mai tsafta, ɗakin ma komai tsaf babu kayan haukan nan na manyan bokaye, sai farantin ƙasa a gabansa, wannan ne karo na farko da Fatima ta je wajen Malami da sunan neman taimako, kuma ta san a bayyane yake shirka ce za ta aikata, don haka ta shiga fargaba da faɗuwar gaba, amma fa babu nadama a zuciyarta, domin ita biyan buƙatarta kawai take nema.

Suka gaisa da malamin a mutunce, Zulaiha ta gabatar masa da Fatima, ta yi masa bayanin matsalarta, Fatima ta É—ora da faÉ—in"Malam don Allah ka taimake ni, ni kawai ba na so ya yi auren ne, na fi so ya daina son kowa ya zauna da ni ni kaÉ—ai".

Malam ya ce"An gama, taimako ne za a ba ki da yardar Allah maganar auren nan za ta ruguje, ko aure dubu zai nema sai magana ta lalace, da haka har ya gaji ya daina".

Ya buga ƙasa ya yi zane-zanensa, ya yi murmushi ya ce"Na gani a ƙaddarar mijinki akwai ƙara aure".

Rasss! Ƙirjinta ya yi mummunar bugawa, ta ce"Kenan dole sai ya yi?"

Ya ce"Wane mutum inji mutuwa? Mu za mu iya canza komai, ai tun da kika zo nan to kukanki da wata fargaba ya ƙare".

Ya tambayi sunan shi ta faɗa masa, ya tambayi sunan buduruwar ta ce ba ta sani ba, ya ce"To babu damuwa, zan ba ki maganin da za ki zuba masa a cikin abinci, indai ya ci sau uku shikenan magana ta ƙare, ko tashin zancen ba za ki sake ji ba".

Fatima ta yi godiya, ya ba ta maganin ya ce kuÉ—insa dubu hamsin ne, ya ba ta account ta yi masa transfer, suka koma gida ranta fess. A abincin dare ta barbaÉ—a masa maganin, zuciyarta tana bugawa saboda rashin sabo, Usman ya dawo ya ci abinci hankali kwance, kuma ko a ranar sai da ya yi mata zancen auren nasa, a ranta ta ce"Sai dai ka yi a lahira".

Kwana uku a jere tana saka masa maganin, kullum cikin jiran sakamako take, a ranar da ya kama za su je kai kuɗin auren, a ranar maganin ya yi tasiri a kan shi, domin haka kawai ya ji ya fasa auren, gabaɗaya yarinyar ta fita daga ransa, da sassafe waliyinsa ya kira shi don jinsa shiru, saboda sun yi da shi sassafe zai zo da mota ya ɗauke su su tafi, shiyasa ya tuntuɓe shi don tabbatar da tafiyar, Fatima ta shigo ɗakin don ta wanke banɗakinsa ta ji yana waya a kasalance yana cewa"Baba ina ganin fa babu tafiyar nan, auren ma kawai na fasa".

Wani farinciki ya lulluɓe ta, har murmushi ya kufce mata, ta shige banɗakin shi kuma ya cigaba da wayar, yana bayanin shi ma bai san dalili ba, kawai dai ya ji ya fasa auren ne.

Tun daga nan Usman bai sake tada zancen ƙara aure ba, hakan ya farantawa Fatima rai sosai, suka cigaba da zaman lafiya, babu jimawa kuma ta tsiro masa da zancen ya siya mata gwal, saboda ƙawayenta na cikin unguwa mutum uku duk suna da shi, ita har kunya take ji sabga ta zo ta je da normal sarƙa, amma Usman ya nuna ba shi da wannan kuɗin, duk da ta san yana da shi, ba ta sare ba dai tana ta bin kansa don ya siya mata ko ƙarama ce.

08028966015
[28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/KHaNhtgfrBoAKxQ6GGKFyq

*WANI ZAMAN*

BY
SADIYA ABDULRAZAK

Marubuciyar
Sandar dukan uwargida
Ranar kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Matar shige
Iya ruwa
Wani auren da sauransu

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS

Labarin ya ƙunshi
Kishi
Kissa
Makirci
Cin amana

PAGE 5

Wata biyar da fasa aurensa, suna zaune lafiya, sai dai ta koyi halin roƙo, duk da yana ba ta kuɗi haka kawai ma, amma ta koyi roƙonsa yanzu, ta yi ta ƙaryar za ta yi abu kaza, wanda ajiye kuɗin kawai take yi, burinta ta tara kuɗin da za ta sayi gwal ɗin nan, don ra fita kunya wajen ƙawayenta ƴan gayu. Duk a zatonta ta kashe bakin tsanya, babu sauran batun ƙara aure a lamarinsa, kwatsam sai ya sake zuwa mata da batun wata bazawara, sai a ranar da aka kai kuɗin auren ma ya faɗa mata, da daddare sun gama cin abinci yake ce mata"Nana yau fa na yi miki laifi, laifin da yake halal amma" Ya yi maganar yana dariya.

Ta ce"Laifi kuma na halal? Ban gane ba".

Ya ce"An kai kuÉ—in aurena yau, an saka rana wata uku in sha Allah".

Damm! Ta ji ƙirjinta ya doka da ƙarfi, ta ce"Wata uku!?"

Ya ce"E in sha Allah, dayake ita ma yarinyar iyayenta a shirye suke, kin ga ni ma na shirya, don kuÉ—in haÉ—a lefen ma yana nan a ajiye a gefe guda, lokaci kawai ake jira, shiyasa na ce ya kamata a saka kaÉ—an É—in".

Takaici ya kama ta sosai, har ƙwalla ta kawo idonta, ta ce"Yanzu baban Mu'az kana da kuɗin haɗa kefe a gefe amma ba ka da na siya mini gwal ko?"
Chapter 5 · 0% Book details