← Book details Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 15

Sashe 1

Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

[28/05 13:02] Mai Zafafa: *WANI ZAMAN*

BY
SADIYA ABDUKRAZAK

Marubuciyar
Sandar dukan uwargida
Ranar kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Matar shige
Iya ruwa
Wani auren
Da walakin
Wutar ƙaiƙayi.

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS

Labarin ya ƙunshi
Kishi
Kissa
Makirci
Cin amana

PAGE 1

Kowane mata da miji a farkon aurensu ne suke gina yadda tsarin rayuwarsu zai kasance, wannan lokacin amarcin shi ne babbar damar mace, wanda idan ta sarrafa ta yadda ya dace bisa adalci babu son rai sai a kafa kyakkyawan tubalin da zai samar da rayuwa mai inganci a wannan gidan har abada, idan kuwa aka samu akasin haka tun daga nan sai mace ta rasa damarta, gida ya rushe ya ruɓe, namiji ya dinga yin yadda ya so da rayuwarta. Haka ce ta faru a gidan Usman, sun yi auren soyayya da matarsa Fatima, kuma ƴar'uwarsa ta jini, da farko suna zaune lafiya gwanin sha'awa, kafin komai ya caɓe musu dalilin rashin ginawa gidansu tubali mai inganci, yana son matarsa yana kyautata mata daidai gwargwado, ita ma tana kyautata masa shi da danginsa, amma hakan bai sa ya ɗauke idonsa daga kan matan waje ba, son mata da sha'awarsu a jininsa yake, kuma wannan shi ne babban rauninsa a rayuwa.

A halittar Fatima tana da zafin kishi sosai, sannan Usman yana , tana mugun son shi, don haka ta ɗaura ɗamarar hana kowace mace raɓar shi, domin gani take ita a yanzu da Allah Ya yi mata gyaɗar dogo ta samu miji na nunawa sa'a kuma gwarzo, son kowa ƙin wanda ya rasa to fa Allah Ya mallaka mata shi ne domin ita kaɗai da ƴaƴanta, shi ne komai nata, kuma duniyarta sannan tsanin samun lahirarta, don haka dolenta ta yi iya yinta don ganin wata ba ta ƙwace mata shi ba.

Usman ɗan gayu ne sosai, mai tsafta da ɗaukar wanka, yana da shiga rai sosai, ga shi matashin ɗan kasuwa wanda ake garawa da shi, ƴan canji suka zauna masa, yana kasuwancin kaya kala daban-daban, sannan yana siyar da motoci. Sai dai ita Fatima tana da rauni a ɓangaren tsafta, ba ta damu da gyara gidanta yadda ya kamata ba, komai a hargitse, sannan ba ta iya girkin fita kunya ba, tana da sakaci dai ta wannan fannin, haka dai suke gudanar da rayuwarsu har ta yi haihuwar farko, ta haifi ɗanta namiji, mai suna Ibrahim ana kiransa da Mu'azzaman.

Tana zaune da Usman da zuciyarta ɗaya, ba ta taɓa zarginsa da aikata wani abin da bai dace ba, idan zai fita ya bar wayarsa a gida ko kallo ba ta ishe ta ba, saboda yadda ta yarda da shi, ashe dai idan ana cin ɓaure ba a tona cikinsa, akwai wata rana da ba za ta taɓa mantawa da ita ba, domin a ranar ne ta san wane ne mijinta, ta san wata ɓoyayyiyar ɗabi'arsa da ba ta san yana da ita ba a baya.

A lokacin ba ta daɗe da yin arba'in ba bayan haihuwar Mu'azzam, akwai wata a maƙotansu, buduruwa ce, amma irin manyan ƴan'matan nan ne, ta daɗe a gida ba ta yi aure ba, don ta girmi Fatima sosai, sunanta Lami, kuma irin mutanen nan ne da ba ka san ma taƙamaiman addininsu ba, to su dai ba sa yin sallah kuma ba sa zuwa coci, suna mutunci sosai da iyayenta, kuma tana shigowa gidan su yi fira da Fatima.

Watarana ta shigo da daddare suna cikin fira, sai ga baban Mu'azzam ya dawo gidan, suka gaisa, Lami ta tashi za ta tafi, yana murmushi ya ce"A'a ki yi zamanki, ko dai ba kya so na ji gulmar da kuke yi ne?"

Duka suka yi dariya, sai kuwa ta zauna, can sai Mu'azzam da yake ɗaki yana bacci ya farka, hakan ya sa Fatima ta tafi ɗakin don ta lallaɓa shi ya koma bacci, abunka da jikin jego gajiyayye, ga shi an wuni ana kujiba-kujibar tsakar gida, don haka daga lallaɓa yaron bacci ya kwasheta, tun ƙarfe takwas ba ta farka ba sai wajen sha ɗaya, da fito falo ta tarar Lami ta tafi, ta koma ta kwanta.

Tun daga ranar kullum sai Lami ta shigo da daddare, ta ce ta zo fira, shi kuma baban Mu'azzam sai ya tsiri dawowa da wuri, sannan kamar abun almara ita kuma Fatima kullum sai Mu'azzam ya farka, idan ta je ta lallaɓa shi sai bacci ya ɗauke ta, kasancewarta mai nauyin bacci. Fatima ta zauna ta yi karatun ta nutsu, ta fara tunanin me yasa Lami take zuwa kullum da daddare? Me yasa shi ma mijinta ya canza lokacin dawowa? Sannan ta fara zargin wannan baccin da take yi ba ta sanin lokacin da Lami take tafiya anya alkhairi ne kuwa? Anya ba ta yin wauta? Hakan ya sa yau ta ce dole za ta fake su ta ga idan da matsala ko babu.

Yau ma kamar kullum Lami ta shigo, riga ce bes a jikinta duk hammata a waje da siket, tun da ba musulma ba ce ba ruwanta da hijjabi, ta zauna suka fara hira, babu jimawa baban Mu'azzam ya dawo, ya miƙo mata leda ya ce"Fati ga kaza".

Ta ce"Bacci nake ji wallahi, sai da safen zan ci".

Ta bar ledar akan senter table ta shiga ɗakinta, ta tsaya tana safa da marwa, ta bada tazarar mintuma goma sha biyar, sannan ta lallaɓo a hankali ta buɗe labule ta leƙo, ƙirjinta ya yi mummunar bugawa sakamakon baƙin ganin da ta yi, Lami ce zaune a kan cinyar baban Mu'azzam, hannunsa ɗaya yana cikin rigarta, ɗayan kuma yana bata kaza a baki, hankalinsu a kwance tamkar dai ma'aurata, Fatima ta daskare tana kallonsu ƙirjinta yana bugawa, sun shagala ba su taɓa tunanin tana kallonsu ba, idan ya ba ta kazar sai ya yi kissing ɗinta, can dai ta ga ya ɗage rigarta, ko bireziya babu a jikinta, yana ƙoƙarin kai bakinsa ƙirjinta, Fatima ta ji zuciya ta ciyo ta yi wani ihu ba, ta yi tsalle ta yi kansu, tana zuwa ta wanke shi da mari, Lami ta zabura ta miƙe tsaye, ai kuwa Fatima ta yi kukan kura ta hau ta da duka, tamkar sa'arta, tana ta zaginta tana"Matsiyaciya maci amana, mai warin Hamata".Lami ta fizge ta gudu Fatima tana ta zaginta.

Zuciyar Fatima kamar za ta fashe saboda kishi, ta dawo kan Usman da duka, yana ta riƙe ta yana ba ta haƙuri, ta fizge ta shige ɗaki da gudu, ta saka sakata, duk bugun da yake yi ba ta buɗe ba, ta kwanta tana ta kuka, da tunanin wai dama haka mijinta yake?

Ya girgiza zuciyarta sosai ya raunata ta, ya shammace ta, ashe dai da gaske ba a shaidar miji? Ta raba dare tana tunanin dalilinsa na ƙyalle ido a matan waje, duk hankalinta ya tashi, domin ta san duk namijin da zai zo gidan aurensa ya aikata wannan abu da maƙociyarsu to fa tabbas dama ya saba, ko fargabar za ta iya fitowa ba ya ji saboda idonsa ya rufe? Ta yi kuka mai isarta kafin bacci ya ɗauke ta mai cike da ƙunci.

A ɓangaren baban Mu'azzam kuwa da ya lura ba za ta buɗe ƙofar ba sai ya haƙura ya tafi ɗakinsa ya kwanta, nadama duk ta kama shi, bai so a ce Nana ta san da wannan halin nasa ba, domin ya san dole zai rage ƙima a idonta, shi kansa wani lokacin yana takaicin halinsa, amma yana rasa yadda zai yi, saboda abun kusan ya zame masa jini, idan ya ga mace ƙafarsa har rawa take ɗauka, ya rasa saitinsa, amma tun da yanzu matarsa ta san halinsa dole ya yi taka-tsan-tsan.

Ya ɗakko wayarsa ya kira Lami, tana ɗagawa ta ce"Ka ga abin da ka ja mini ko? Wannan ƙaramar yarinyar har ta samu damar dukana da zagi saboda kai ko?"

Ya ce"Ki yi haƙuri..."

"Ai dama ka so tozarta ni ne, ka ce na dinga zuwa ba za a samu matsala ba, yanzu ga shi nan ai za ta yaÉ—a ni a unguwa na yi ta jin kunya".

Ya ce"Ba za ta yaÉ—a ki ba in sha Allah, kawai dai shikenan kar ki sake zuwa".

Ta ce"Yanzu a ina za mu dinga haÉ—uwa kenan?"

Ya ce"Don Allah mu bar shi haka, tun da ta sani shikenan za ta saka ido a kanmu, a haƙura kawai, ki turo min acconut number na sallame ki".

Kamar za ta yi kuka ta ce"Don Allah Usman kar ka yi mini haka, wallahi ina sonka, ina son kasancewa da kai ko sau É—aya ne".

Ya ce"Babu wannan damar ki turo min kawai na sallame ki".

Ta ce"Nu ba kuÉ—inka nake so ba ai kai nake so".

Ya yi tsaki ya ce"Zan saka ki a blacklist ne fa, idan ba kya son kuÉ—in shikenan".

Da jin haka ta katse wayar ta tura masa, ya saka mata dubu hamsin ya yi block É—inta, haka ya yi bacci cike da tunanin yadda zai shawo kan matarsa.

08028966015
[28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/IqwGrPcKXM47271YQuTB2R

*WANI ZAMAN*

BY
SADIYA ABDULRAZAK

Marubuciyar
Sandar dukan uwargida
Ranar kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Matar shige
Iya ruwa
Wani auren da sauransu

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS

Labarin ya ƙunshi
Kishi
Kissa
Makirci
Cin amana

PAGE 2
Chapter 1 · 0% Book details