Sashe 14
Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya wurga hannuwansa biyu sama yana wasu abubuwa masu kama da gurnani, da wani yare, ledoji biyu suka bayyana a hannuwan, ya wurgawa kowaccensu guda ɗaya, ya kalli Fatima wacce ta cafe ledar ta ƙanƙame, ya ce"Mun ga komai, burinki mijinki ya fasa auren da zai yi gobe, to wannan auren tabbatacce ne, za a ɗaura shi gobe da misalin ƙarfe goma da minti ashirin da biyu da sakan biyar, amma kina da mafita, idan an ɗaura auren zai iya sakinta a ranar, indai kin bi ƙa'idar wannan maganin da na ba ki, akwai itace a ciki, idan kin koma yanzu ki jiƙa shi a babban bokiti ya kwana, gobe da daddare idan an kawo amaryar kafin ya ganta ki yi wanka da wannan ruwan, sannan akwai kwalli, ki saka shi, sai ki kalle shi ido cikin ido, ki yi masa umarnin ya sake ta, nan take buƙata za ta biya! Kuɗin aikinki naira dubu ɗari da hanmsin ne". Ya ajiye mata wata baƙar ƙwarya a gabanta, ta saka kuɗin hannunta na rawa, don a firgice take.
Ya kalli abokiyat tafiyar tata ya ce"Akan maganar surukarki kika dawo ko? Burikinki ta mutu kawai yanzu ba wai ki rufe bakinta ba, to ki je gida, yau cikin dare za ta mutu a kan gadonta! Kuɗinki dubu ɗari biyu da hamsin". Ita ma ta ciro kuɗin ta saka a cikin ƙwaryar, suka yi godiya suka tashi suka tafi.
Duk irin gudun da Hajiya take zurawa a mota, ba su suka isa gida ba sai ƙarfe sha biyu na dare, a lokacin hankalin Fatima ya gama tashi, ta ci kuka ta gode Allah, saboda ta san asirinta sai ya tonu, ana can ana nemanta, ina za ta ce ta je ta kar sha biyu na dare? Ga shi ta bar yaro mai shan nono a gida, ba ta tafi da wayarta ba kuma, ita kuwa Hajiya ranta fes, don mijinta ba ya gari, yaranta kuma ta kai su gidan kakarsu, inda za a yi rasuwar kenan yau. Ƙarshe dai Fatima a gidan wannan matar ta kwana, ta ma kasa bacci saboda damuwa.
A can gida kuwa, tun safe da Usman zai fita ya tambayi ina Fatima Hasana ta ce ta fita, kuma ba ta faɗa mata inda za ta je ba, ya kira wayarta ya ji tana gida, sai kawai ya fita, da la'asar ya dawo gidan ya ga ba ta dawo ba, zuwa lokacin gida ya cika da baƙi ana ta jajanta ina ta tafi ba ta sanar ba? Kuma ta bar ƙaramin yaro, don ma ba shi da rigima, ana ta hada-hadar girkin abincin gobe, wasu suna gulmar kishi ne ya hana ta zaman gidan.
Sai da aka idar da sallar isha'i ba ta dawo ba, sannan aka fara shiga damuwa, aka dinga kiraye-kirayen waya ko'ina sai a ji ba ta je ba, zuwa ƙarfe ɗaya na dare hankali ya gama tashi, har da masu kuka, Usman ne yake ta kwantar musu da hankali, yana cewa ba ɓata ta yi ba, tun da dama ba ta faɗawa kowa inda za ta je ba, tana sane ta yi hakan, shi sam bai damu ba, gani yake haukan kishi ne kawai ya sa ta yi haka, don haka shi tsaf ma ya je wajen dinner suka sha paty da amaryarsa. Haka aka kwana kowa babu nutsuwa.
Washegari da sassafe ta tafi gidan yayarta wacce suke uwa É—aya uba É—aya, Sumayya tana ganinta ta ce"Fatima! Daga ina kike? Me ya same ki? A ina kika kwana?"
Fatima ta fara share hawaye ta shige É—akin, bayan sun zauna ta ce"Don Allah Yaya ki rufa mini asiri ki ce a gidanki na kwana".
Sumayya ta ce"Ke kuwa ina kika je? Kuma ta ya zan ce a gidana kika kwana, bayan da ni aka yi ta jajenki jiyan?"
Ta ce"Sai ki ce ni na ce kar ki faÉ—a, don Allah ki taimaka mini" .
Sumayya ta ce"To ina kika je?"
Fatima ta ce"Wallahi na kasa jurewa ne, da garin zan bari, na je na wuni a tasha na rasa ina zan nufa, tun da idan na je gidan ƴan'uwa ma na san za a tona min asiri, ina tasha har isha'i, sai na yi gidan ƙawata na kwana a can, kawai ji na yi kamar kar na koma gidan nawa wallahi, zuciyata zafi take yi".
Sumayya ta ce"Assha! Haba Fatima, ke kuma ta haka za ki nuna naki kishin? Wannan dai ba hali bane gaskiya kar ki sake yin haka, yanzu abu na taro kowa ya ji ba ki kwana a gida ba, yanzu idan na ce kina gidana a nan kikw kwana ba kowa ne zai yarda ba wallahi".
Fatima ta ce"Ba komai ki ce haka É—in dai".
Ta ɗauki waya ta kira Usman ɗin, suka gaisa, ta ce masa Fatima fa tana gidanta a nan ta kwana, ta ƙi faɗa ne kawai saboda Fatiman ta roƙe ta akan ta ƙyale ta a nan ɗin, gidan ya yi mata zafi. Ran Usman ya ɓaci ya dinga faɗa yana cewa shi me ya yi mata na jin zafi da za ta zaɓi barin gidan ta bar ƴaƴanta? Sumayya ta ce ya zo gidan dai su sasanta.
Kafin ya zo Fatima ta yi wanka ta saka kayan yayarta, ya zo gidan yana ta haÉ—e rai, ya ce"Fatima me na yi miki? Tun da na faa zancen auren an na zage ki ko na ci zarafinki?"
Ta girgiza kai alamar a'a, ya ƙaraci faɗansa ba ta ce komai ba, tun da ta san tana da maganin iskancinsa a hannunta, komai zai yi kafin anjima ne, sanda za ta yi masa umarnin ya saki amaryar da yake ta rawar kai akanta, kuma dole ya sake ta ɗin. Tare suka koma gidan, a motar babu wanda ya tankawa wanh har suka ƙarasa, ƴan'uwa ana ta yi mata nasiha da faɗa, ta ɗauki ɗanta ta shige ɗaki.
WACE CE ZAINAB AMARYAR USMAN?
Zainab irin kangararrun yaran nan ne da suka taso da rashin ji, sannan ba ta samu isasshiyar tarbiyya ba, shekararta biyar a duniya mahaifinta ya rasu, tana da yayyu mata guda biyu, ragamar kula da su duka akan mahaifiyarsu take, ita ce cinsu da shansu, komai nasu ita ce, tun sanda mahaifinsu na da rai take tsaye akansa, ta mallake shi ta hana shi sakat, ta hana shi ƙara aure, domin ta shahara ta bunƙasa ta fannin bin bokaye, har kwanan kan bishiya ta yi don neman biyan buƙata, ta zura hannu a kabari ya fi mini talatin, ta yanka hannunta ta tari jinin ta kwaɓa magani da shi, za ta iya yin komai saboda buƙatarta ta biya, bayan rasuwar mijinta ta auri maza har biyar, kowacce auren ba ya cin Talata ballantana Laraba, saboda tijararta da rashin haƙuri, ba ta taɓa yin aure ta bi miji gidansa ba, nan dai gidan ƴaƴanta da marigayi ya bar musu gado a ciki mijin yake zuwa ya iske ta, har yanzu da shekaru suka ja Hanne ƴar gayu ce, dama kyakkyawa ce, kana kallonta ka ga ƴar bariki, a yanzu haka tana da wani wanda ba a san ma me za a kira shi ba, mijinta ne ko kwarto? Matashi ne ta girme masa, ya aure ta suka tare a gidanta, yau faɗa gobe daɗi, a haka har aka yi saki biyu, ashe matarsa ba ta taɓa sanin ya yi auren ba, a ranar da ta sani ta zo har gidan ta saka shi a gaba ta ce sai ya sake ta, nan take ya cike saki na ukun, Hanne tana son Baba ƙarami don haka ta shiga ta fita ta ɗaure shi ram, ya zama babu auren amma ba su rabu ba, kwana ne kawai ba ya yi a gidan, zai zo ya wuni, suna shiga ɗaki su kwashe awanni su biyu, sannan kullum sai ya ba ta kuɗin cefane, idan faɗa ya tashi haka za su yi a gidan, suna maganganu da zage-zage irin na ƴan bariki, kuma tana da wasu samarin da suke zuwa zance, haka za su shiba ɗaki su ƙule, ko kuma ta ci kwalliya ta ce ta tafi neman na kanta, haka za ta wuni bin office-office ɗin zawarawanta, sai dare ta dawo niƙi-niƙi da kaya, da uwar kuɗinta a jaka, babu ruwanta da kunyar buduruwar ƴarta Zainab dake gidan, sauran sun yi aure, kuma dayake tariyya ta Allah ce cikin yaran Zainab ce kawai ta kafe halayen Hanne, su sauran kafin aurensu har nasiha suke yi mata.
Zainab tun tana shekara sha huɗu mazan layi marasa tarbiyya suka fara buɗe mata ido da kuɗi, ake ɗan taɓata ana ba ta kuɗi, bayan ta gama secondary kuma abun nata ya shahara, take bawa maza kanta ana biyanta, har wani saurayinta ya yi mata ciki, daga nan ya ɗauke ƙafa, Hanne ta zubar da cikin, don wannan ba baƙon abu ba ne a wajenta, ita kanta kafin ta yi aure sau biyu tana zubar da ciki, sannan bayan rasuwar mijinta ma ta zubar da ciki, ta kai sunan saurayin wajen boka aka kafe shi tsaf, sai da ya aure ta, wata biyu da auren Zainab ta ce ta gaji da auren, saboda yawan faɗan da suke yi, sannan ji ta yi auren ma duk takura ne kawai, ta matsa masa da rashin mutunci, na safe da ban, na dare da ban sai da ya sake ta.
Tana gama idda ta samu wani mai kuɗi a nan maƙotansu, bai daɗe da tarewa ba, don ba ƴan gari ba ne, aiki ne ya kawo shi garin, ya zo da matarsa ya kama hayar babban gida, tun da Zainab ta ƙyalla ido ta gan shi ta ji tana son shi, kuma kai tsaye ta tunkare shi da maganar so, amma ya nuna ba ya sonta, tama faɗawa mahaifiyarta damuwarta, ta tashi tsaye ta yi iya yinta, sai ga wannan mutumin ya zo da kan shi ya ce yana son Zainab, duk ya gigice, auren ma sati huɗu aka saka, kuma shi ya yi mata komai na kayan ɗaki, duk abin da ta ba shi umarni ba ya tsallakewa jiki na rawa zai yi mata, matarsa ta shiga tsanani da ƙunci sosai tun da ya fara shirin auren nan.