Sashe 2
Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari Fatima ta kasa fitowa daga ɗakinta, saboda ba ta so ma ta yi ido huɗu da mijinta, sam ba ta san ganin shi, saboda kallon shi ba zai haifar mata da komai ba sai ɓacin rai, shi kuma tun asuba da ya dawo daga masallaci yake zaune a falo, jira yake yi ta fito ya ba ta haƙuri su fahimci juna, duk kunya da nadamar abin da ya aikata sun ishe shi, ganin har bakwai takwas ba ta fito ba, sai ya tashi a sanyaye ya shiga ɗakin, ya tarar da ita kwance a gado amma ba bacci take yi ba, ƙarar buɗe ƙofar da ya yi ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, ta juya ta kalle shi, kawai sai zuciyarta ta hasko mata hoton da yake kafe a cikinta, wanda take ganin ba zai goge ba har abada, ta hango shi ɗauke da Lami a cinyarsa hannunsa a cikin rigarta, zuciyarta ta sake kumbura, ta rutse ido hawaye suka sakko, ji take har gara a ce kama ta ya yi ya lakaɗa mata duka akan wannan abin da ya yi mata, da muryar kuka ta ce"Don Allah ka fita, ba na son ganinka!".
Ya ƙaraso ya zauna a bakin gadon, ya ce"Ki yi haƙuri, na san ban kyauta miki ba, amma wallahi ba halina ba ne, sharrin shaiɗan ne da ruɗin zuciya, da kaidin mace, yaudarata ta yi wallahi, kuma ita ta zo ta zauna min, sannan jiyan ne kawai abun ya taɓa faruwa".
Fatima ta ce"Wallahi ba zan taɓa yarda da kai ba, tun da har ka gwada a cikin gida na tabbata ka saba yi a waje, idan ka cuce ni Allah Ya saka mini".
Ya ce"Don Allah ki yi haƙuri, na karɓi laifina na yi nadama, kuma in sha Allahu na farko na ƙarshe".
Ta juyat da kai gefe, ya matso yana shafa yatsun ƙafarta yake cewa"Kin haƙura? Don Allah ki yi haƙuri, wallahi na yi nadama".
Ta ƙi cewa komai. Ya ce"Ki fito mana don Allah, kin ga yau sassafe na so na fita, amma na kasa saboda na san ranki a ɓace yake".
Ta yi banza da shi. Ya tashi ya fita, sai ya samu kansa da shiga kitchen, ya haɗa musu abun karyawa, ya ɗakko ya kawo mata, har lokacin tana kwance, ya zauna a ɗakin ya ci nashi, ya sake ba ta haƙuri da nuna nadama sosai kafin ya ce"Yanzu me kike so? Mene ne babu a gidan? Me zan taho miki da shi?"
Ta ce"Ba na buƙatar komai naka, ka je ka cigaba da bawa matan wajen".
Ya ce"To na ji, amma dai don Allah ki yi haƙuri, idan kin sake kama ni sai ki yi mini komai ma".
Ya ce"Ki ci abincin, ko za mu fita ki ci a gidan cin abinci?"
Ta yi masa wani kallo mai kama da harara, don tana yawan roƙonsa kan su je gidan cin abincin musamman idan ranar tana jin ganda, ko kuma tana son yin fafar a ganta da mijinta ɗan gayu, amma sai ya ƙi ya ce bai ga amfanin haka ba, ga kayan abinci ya ajiye ba zai je ya siya a waje ba, shi ne yau da ya san ya cuce ta ya guma mata baƙinciki zai ce ta zo su je, ta ce"Don Allah ka tafi, wannan borin kunyar taka ya ishe ni haka".
Ya ce"A dai yi haƙuri, kuma don Allah ba ruwanki da Lami, idan kika ce za ki kula ta kamar kin daɓawa kanki wuƙa ne, kin ga kanmu za ki tonawa asiri ko?"
Ta yi kamar ba ta ji ba, ya fice daga gidan yana cewa"Sai na dawo".
Yau ta kasa ce masa a dawo lafiya.Da zai ya dawo ya yo mata uwar siyayya, kayan ciye-ciye da na amfanin gida, ta ji daɗi amma ba ta nuna ba, sam ta ƙi sakar masa fuska, shi kuma duk ya takura, suka shafe kwana uku a haka, kullum da abubuwan da zai siyo mata, sannan kullum sai ya ba ta haƙuri da nuna nadamarsa, ya siyo mata babbar wayar da ta daɗe tana faɗa masa tana so, wannan ya sa ta huce gabaɗaya, ta saki jiki ta daina nuna masa komai, sai dai fa wannan abin da ya yi yana nan maƙale a ranta, don ba ta jin za ta manta da shi.
Tun da ta haihu ta yi tsarki ba ta koma ɗakinsa da kwana ba, sai take tunanin ko har da wannan kewar tata a bada gudunmawa ya aikata wannan abun, don haka ta yanke za ta gyara jikinta sosai ta koma masa, tun tana amarya dama ba ta wasa da maganin mata, duk inda ta ji indai da kuɗi a hannunta za ta siya, sai ta sayi maganin mata ba ta sayi humra ba, don haka yanzun ma ta nemi kuɗi a wajensa, babu musu ya ba ta, dama can ba ya yi mata rowa, ballantana yanzu kuma da yake neman ta yarda da shi, ta shirya ta ta je gidan mai maganin da ta saba siya, ta haɗa mata magunguna masu kyau, kwananta uku tana sha, ita kanta ta ji sauyi sosai a jikinta, don haka ta shirya gobe za ta koma ɗakin baban Mu'azzam, da safe ta fito cikin shirinta,sun yi da shi tun jiya yau zai kai ta gidan gyaran jiki, dulka za a yi mata da kitso da ƙunshi, ta fito riƙe da ɗanta a kafaɗa da jakarata a hannu, ya kalle ta yana murmushi ya ce"To da me zan taimaka? Ɗan ko jakar?"
Ita ma murmushin ta yi tana kallon yadda shaddar jikinsa ta haska shi ya yi kyau sosai, ta ce"Za ka zuba mini kuÉ—i a jakar ne?"
Ya ce"To me zai hana?"
Ta miƙa masa jakar, ya karɓa ya rataya a kafaɗa kamar mace, hakan ya sa ta tuntsire da dariya ta ce"Shi kenan ka zama mijin Hajiya mai riƙe mata jaka".
Ya ce"Ba wata Hajiya, yanzu fa kika gama kafa sharaÉ—in zan zuba miki kuÉ—i a jaka, Hajiya ai ita take zubawa mijin kuÉ—i a aljihu ko account".
Ta ce"Ai kuwa idan hakane ni ba hajiya ba ce, ka ga ba ni jakata".
Ya ce"A'a mu je dai na riƙe miki, amma babu batun mijin hajiya ki soke shi".
Suka shiga mota suka tafi, suna ta fira cikin raha da dariya, suka ƙarasa wajen, ya ce"To ya za a yi? Zan jira ki ne ko sai an gama ki kira ni na dawo na ɗauke ki?"
Ta ce"Ai gara ka je É—in, kar a zaunar da kai, duk da safiya ce ba lallai a samu layi ba".
Ya ce"To shikenan mu je na raka ki sai na ji kuÉ—in".
Suka shiga a tare har lokacin yana riƙe da jakarta, suka tarar da matar mai wajen da yaranda suna kintsa wajen, da alama ba su daɗe da buɗe shagon ba, tun da suka shiga idon Usman ya sauka akan wata yarinya, surarta ta tafi da imaninsa, nan take ya ji gabaɗaya kansa ya fara hayaƙi, yana ta kokowa da control ɗinsa, ya kafe ta da ido yayin da Fatima take yi wa matar bayanin abin da ya kawo ta, sanda ta juyo don ta yi masa magana har sai da ta yi mamakin ganin saɓ hankalinsa ba ya kansu yana kallon can gefe, ta bi wajen da kallo, ta ga yarinya ce buduruwa tana ta goge-goge, babu ko mayafi a jikinta sai riga t-shirt wacce ta bayyana halittar ƙirjinta da siket, gabanta ya faɗi, zuciyarta ta tsinke ta yi baƙi nan take, don ta gane ita yake kallo, da ɗan ƙarfi ta ce"Baban Mu'az!".
Ya É—an dirirece kafin ya ce"Na'am".
Ta ce"Mun gama magana, ka je kawai, idan an gama zan kira ka a waya".
Yana satar kallon yarinyar ya ce"Ai kawai zan zauna na jira ki É—in, babu damuwa ma".
Ta ce"To ka je daga mota ko?"
Matar ta ce"A'a ga kujera nan ya zauna".
Kafin ma ta rufe baki ya ja kujera ta zauna, yana sauke numfashi, idonsa kafe a kan yarinyar nan har suka gama saita komai ta zo ta fara yi wa Fatima ƙunshin. Shi kaɗai ya san halin da yake ciki, ji yake zai iya ba wa yarinyar nan ko nawa ne indai za ta yarda da shi ko na minti talatin ne, ya daɗe bai ga macen da ta ruɗa shi kamar wannan ba, sai kallonta yake yi, so yake su haɗa ido ya yi mata alama ko da ido ko da hannu, idan ya dace ƴar hannu ce sai su san dabarar da za su yi su yi musayar lamba, amma hankalinta yana kan ƙunshin da take yi, yana ta chart a wayarsa yana kallonsu har aka gama, wata tana yiwa Fatima kitso, ganin wasu sun zo ya sa shi fita waje ya koma ƙofar wajen ya zauna, zuciyarsa tana ta azalzalarsa, ji yake idan bai samu ya taɓa yarinyar nan ba kamar yau ba zai iya bacci ba, ya saƙa wannan ya kunce ya ƙulla wancen shikaɗai, ana dab da gama mata ya koma cikin shagon, Fatima da ta gama lura da kallon da yake yi wa yarinyar nan duk kishi ya kama ta, ta ce"Ai an gama ma, ka he wajen ka jira".
Ya ce"To kawo Mu'az É—in, sai kuka yake".
Ba a cire mata lallen ba, don haka ita wannan yarinya da ta soki rayuwarsa da kibiya, ita ce ta ɗauki ɗan ta tafi miƙa masa, idon Fatima yana kansu, ganin yadda ya narke ido yana kallon yarinyar kamar tsohon gwarto har wani lashe baki yake yi, dama ta san wannan halayyarsa ce, ko ita ce ya matsu da ita haka yake lasar bakin nan, don haka ta gama fahimtar inda ya doda game da yarinyar, ita kuwa yarinyar da zuciyarta ɗata take miƙa masa yaron, Usman ya ga wannan damar idan ta wuce shi ba, don haka ya kai hannunsa kan ƙirjinta kai tsaye, ya taro yaron da ɗayan hannu, saukar hannunsa tarr a cikin idon Fatima, wacce ta ji zuciyarta ta yi dokawar da ba ta taɓa yin irinta ba, sai da ta ji kamar numfashinta zai ɗauke.