Sashe 11
Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka suka sake kwashe sati biyu suna wannan zaman, ta sha zuba kofuna a bola sabofa ya taɓa, idan ya zauna a waje ya tashi sai ta goge kujerar da ruwa ta fesa turare, har kyautar kuɗi ya ba ta wai ko za ta huce, ta ƙi karɓa ta ce ya je ya kai wa matan waje kamar yadda ya saba. Abun duk ya dame shi, yana neman sasanci, ga buƙatuwa ta sako shi a gaba, tun bayan abun sau biyu kawai ya keɓe da wata a hotel, don haka yau ya zaunar da Fatima ya ce"Kin ga Nana magana za mu yi ta fahimta, kin yi arba'in har kin wuce amma kin ƙi dawowa ɗakina, me kike nufi? Kuma wannan wulaƙancin da kike yi mini a gaban yara ya ishe ni haka".
Ta ce"Ai kai ne ka ja, kuma tun da ya ishe ka me zai hana ka É—auki mataki?"
Ya ce"Ni fa ba fitina nake nema ba, ai na san na yi laifi, kuma na yi nadama, shiyasa nake neman sulhu, don Allah ki yi haƙuri, na gaji da wannan zaman".
Ta ce"Kanka ake ji, ni dai ba zan sake haÉ—a jiki da kai ba, tun da ni ban ishe ka ba, ka je waÉ—anda suke isarka su baka".
Duk yadda ya so su yi sulhu ta ƙi, ta botsare masa, don haka kawai ya kira yayarta a waya, suka gaisa ya faɗa mata shi fa ya yi wa Fatima laifi kuma ta ƙi ta haƙura ta ƙaurace masa, yayarta ta kira ta tana ta yi mata faɗa, kuma shi da itan duk sun ƙi faɗa mata laifin da ya yi, ta yi mata faɗa da nasiha sosai.
Fatima ta yarda sun zauna zaman sulhu, amma ta faɗa masa ba za ta sake zama a kan kujerar da karuwa ta zauna ba ballantana kuma kan gado, a takaice dai ba za ta sake shiga ɗakinsa ba, ta ce sai dai ya canza kayan ɗakin, haka kuwa aka yi duka gadon da kujerun ya canza, hatta zannuwan gado sai da ya bayar da su duka ya sayi wasu, kuma ta ce ya ba ta dubu ɗari biyu za ta yi gyaran jiki, ya ba ta, daga nan aka samu maslaha, ta sayi magunguna masu kyau da inganci, kuma ta bi ƙa'idar amfani da su, zamansu ya gyaru suka koma kamar da.
Sai dai tafiya ba ta yi nisa ba Usman ya zo mata da zancen zai ƙara aure, da raunin murya yake cewa"Kin ga ni mabuƙaci ne, idan na ce da ke kaɗai zan rayu sai na ga kamar zan dinga cutar da ke, kuma ko ba haka ba ma ina da ra'ayin ƙara auren ne, ga ginin mata biyu na yi".
Ta ce"Ka saka Æ´an haya mana".
Ya ce"Auren dai zan yi in sha Allah, akwai wacce muka daidaita".
Ta ce"Allah Ya ba da sa'a".
Ya ce"Amin, bazawara ce ma, don haka ba da yawa za a saka ba".
Ta ce"Allah Ya kaimu".
Wannan karon ba ta wani damu ba, tun da tana da tsayayyen malamin da zai ruguje maganar, hmm Fatima ta manta da maganar nan da aka ce 'Idan jurinka sammako wani a tafe ya kwana'.
08028966015
[29/05 18:31] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/DqC9XDRW7ee7y5JtVxNqGr
*Zoki mallaki kayan kitchen cikin saukii,Adashen kitchen(weekly)ðŸ¤ðŸ‘Œ*
*Duk kayan kitchen dakikeso zaa siya maki da kudin adashenki…Kikwashi kayanki tamkar kyautaðŸ¤ðŸ’ƒðŸ’ƒ*
*Gold kitchen Adashe dinmu ba wasa aciki! 100% aminci, 100% sauki !*
*WANI ZAMAN*
BY
SADIYA ABDULRAZAK
Marubuciyar
Sandar dukan uwargida
Ranar kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Matar shige
Iya ruwa
Wani auren da sauransu
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS
Labarin ya ƙunshi
Kishi
Kissa
Makirci
Cin amana
PAGE 9
Ta yi masa shiru tana jiran ya gama shiryawa ya tsayar da zancen auren, sannan ta ziyarci malam. Bayan sati biyu da maganar sai ga shi ya zo mata da zancen auren, abun ya taso gadan-gadan, ya ce mata gobe za a kai kuɗin aure, kuma sati shida za a saka, sao farinciki yake yi yana ba ta labari, da alama dai yana zumuɗin auren nan, don haka ta shiga damuwa, washegari ta shirya ta tafi wajen Malaminta, a wannan karon ita kaɗai ma ta je, ta zayyana masa komai, ya buga ƙasa ya baje ya sake bugawa ya baje ta, ya ɗago ya kalle ta, ya ce"Wannan yarinyar da zai aura ita ma ba a zaune take ba, kuma na ga cewar wannan auren tabbatacce ne, sai an yi shi".
Fatima ta ji tashin hankali ya dirar mata, ta ce"Na shiga uku! Sai an yi kuma? Yanzu babu wata mafitar? Wallahi ba zan iya haÉ—a miji da wata ba".
Ya ce"Haka dai ƙasa ta nuna, amma mu muna iya canza komai ai, don haka zan yi iya yina don ganin komai ya wargaje, sai dai fa aiki ne da yake buƙatar kuɗi da kuma kula wajen gudanar da shi".
Fatima ta ce"Zan ba da ko nawa ne, ni dai don Allah ka taimake ni".
Ya ce"Za mu yi yanka don a bawa aljani jinin, shi ne zai yi aikin tarwatsa taurarinsu, sannan ya saka masa wasi-wasi akan ita yarinyar da ma auren gabaÉ—aya, sannan kuma zan ba ki maganin da za ki saka masa a abinci wanda zai sa ya dinga bin umarninki, idan kika ce ya fasa auren zai daina"
Fatima ta ce"Duka nawa kenan?"
Ya ce"Dubu É—ari biyu za ki ba da, tun da an zama É—aya".
Nan take ta yi masa transfer ta account É—insa, ya tabbatar mata da za a yi yankan, sannan ya ba ta wanda za ta saka a abinci, ya faÉ—a mata amma yana da É—aci, kuma duka za ta juye a lokaci É—aya, don haka ya ba ta shawarar ta yi miyar shuwaka.
Ai kuwa daga nan kasuwa ta zarce, ta yi cefanen miyar shuwaka, ba ta taɓa yi ba ma don ba ta sonta saboda ɗacinta, haka ta yi tuwo da miyar, iya cikinsa ta yi ta zuba masa a kula, dayake ba ya garin ma, amma dai zai dawo komai dare, ita ta yi girkinta suka ci da yara. Wajen goma na dare ya dawo lokacin har ta gaji da jiransa, ya dawo da gasassun kaji, ya zauna tana yi masa sannu, yana amsawa, ta kawo masa abinci ya ce"Ai kuwa a ƙoshe nake, don mun ci abinci da magriba, ga kuma kaza nan".
Ta marairaice ta ce"Amma dai ai ka san da na gidanka ko? A kan me za ka je ka cika cikinka a waje?"
Ya ce"To kuma abin da ba yau na fara ba?"
Ta ce"Ai yau girki na musamman na yi maka, ni dai sai ka ci".
Ya ce"To me kika dafa? Kawo na yi ko cokali biyu ne".
Fatima da bugar ciki ta ce"Ko dai wajen amaryar ka tsaya ka ci?"
Ya yi murmushi ya ce"A'a wallahi, na dai tsaya na ba ta tata kazar".
Fatima ta ce"Ka kyauta kuwa, ya sunanta ne?"
Ya ce"Zainab ce, wannan karon Zee baby na É—akko".
Fatima ta je ta É—akko abincin ta ajiye masa tana cewa"Allah Ya sa dai ita ba yaudararta za ka yi ba".
Ya ce"Yaudara kuma?"
Ta ce"To ai na ga idan ka É—akko mahanar auren haka kawai sai ka zo ka ce ka fasa".
Ya ce"Hmm ni kaina abun yana damuna wallahi, haka kawai sai na ji na fasa ba na son yin auren, amma dai wannan jikina yana ba ni abun ya zo ƙarshe".
Ta ce"Allah Ya sa".
A ranta kuwa cewa ta yi'Nan da kwana uku sai dai ka yi wata maganar ba wannan ba'.
Ta zuba masa tuwon ta miƙa masa, ya ce'Kuma tuwo kika yi? Yadda nake a ƙoshen na na sake ɗora tuwo?"
Ta ce"Kai dai ka ci idan kana son yi mini adalci".
Ya kai lomar tuwon ba tare da bisimillah ba sai cewa da yake yi"Wannan miyar alayyahu ce?"
Yana ci ya yamutse fuska ya ce"Ya É—aci haka?"
Ta ce"Miyar shuwaka ce".
Ya ce"To mene ne amfanin yinta? Ni ba na son sabgar miya mai É—aci".
Ta ce"To ai magani ce, ka daure dai ka ci tun da ka fara ci, idan ya kwana sai a yi asararsa, ni na ci har ya min yawa".
Haka ya daure ya ci tabin tuwon ba don ya yi masa daɗi ba, duk tadda ta so ya cinye ya ƙi, ya ce ya ƙoshi.
Bayan kwana uku ta zuba ido tana jiran ta inda zai fara ce mata aure ya fasu, amma ta ji shiru, bayan sati É—aya sai ta tambaye shi don ta ji halin da ake ciki, lokacin bayan sallar isha'i ne, ya yi wanka zai fita taa ce"Amma dai wannan wankan na amarya ne ko?"
Ya washe baki ya ce"Hasashenki ya tafi daidai, don kuwa can zan je".
Fatima ta haÉ—iyi wani yawu ta ce"A dawo lafiya, a gaishe ta".
Ya ce"Za ta ji". Ya fice daga gidan.
Tun daga ranar abun duniya ya fara damun Fatima, domin ta ji zancen fasawa shiru, sotari Amaryar da ya kira da Zainab ɗin tana yawan kiransa a gaban Fatima, sai ya tashi ya fita waje ya gama wayarsa ya dawo. Auren ya rage sati uku ya zo mata da zancen kayan faɗar kishiya, ya ce"To kin ga dai duk da bazawara ce lefe zan yi mata, ke kuma ki zaɓa lefen zan yi miko ko kuɗin kayan zan ba ki?"
Wani baƙinciki ya kamata sosai, amma dai ta dake ta ce"Kuɗin dai, saboda na zaɓi kalar da nake so". Don a ganinta idan ma ta karɓi kayan na banza ne, tun da auren dai fasuwa zai yi, ba yi za a yi ba.
Ya ce"To shikenan zan tura miki kuÉ—inki".
Suka yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce"Gida ya kusa cika dai, na gaji da ganin ɓangaren can babu kowa".
Fatima ta ce"To ai ga shi saura ƙiris".
Ya ce"In sha Allah".
Da fargaba ta kwana a ranta, don ta ga alamar wannan karon aikin malamin nan bai ci ba, don haka washegari da safe yana fita ta tafi gidan Malam, ta gurfana kamar mai neman gafara tana kuka take cewa"Malam wannan karon fa aikin nan bai ci ba, wallahi yana nan akan bakansa, bai fasa ba, aure saura sati uku".