← Book details Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 15

Sashe 4

Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari da safe ta koma asibitin, aka sake yi mata scanning, aka tabbatar mata da ya fita babu komai yanzu, sannan aka yi mata faɗan ta kiyaye abubuwan da za ta dinga sha ko amfani da su, ta koma gida tana yi wa kanta barka. Tun daga nan sai ta tsorata da duka maganin mata, ta jingine shi a gefe guda, babu jimawa kuma mijinta ya koma gidan jiya, tare ɓa da sabon salon da ba ya yi mata, yanzu haka kawai saa ya tsiri yi mata faɗa, musamman akan rashin tsaftarta da rashin iya girki, abun yana damun shi sosai, zai yo cefane haɗaɗɗe amma a kwaɓa masa abinci kamar a gidan yari, wanke-wanke sai a samu na kwana uku a gidan, kitchen har tsami yake yi saboda lalataccen abinci, ga shi sam ba ta damuwa da kwalliya, idan ka ganta fess to fita za ta yi.

Haka suka cigaba da zama har ta sake wata haihuwar, zuwa yanzu ta saba da halinsa, domin neman matansa a bayyane yake, ta sha yi masa laɓe a ɗakinsa sai ta ji yana waya da mace, tun tana daurewa har ta fito suka hau sama suka faɗo akan wannan wayar, ta cw kar ya sake yi mata waya da mata a gida, rai dai ya ɓaci amma sam bai fasa ba, tana yawan jin labaran an gan shi da wata, hatta ƴan'matan unguwarsu bai ƙyale ba.

Maganin matan dama shi ta riƙa a matsayin makaminta, to kuma yanzu ta daina don ta tsira da lafiyarta.

Sosai take damuwa da wannan halin nasa, yanzu ya ma rage zama da ita sosai, ya koyi wani tsare gida da ƙananun wulaƙanci, idan ka ga dariyarsa to waya yake yi. Wataran ta same shi har da hawayenta tana tambayarsa me take yi masa wanda ya sa duk ya canza mata? Ya yi banza da ita yana danna waya, cikin kuka ta ce"Don Allah baban Mu'az me nake yi maka? Gabaɗata ka tsane ni ka jingine ni a gefe, yau na ji an ganka da wannan gobe an ganka da waccen, ni ba mace ba ce ba wai? Me matan wajen suka fi ni ne?"

Ya ce"To me nake yi miki ne wai? Ci nake hana ki ko sutura?"

Ta ce"Ba ka hana ni su ba, amma ai ka san ba iya su kaɗai nake buƙata ba, har da kulawarka, ba macen da za ta so a ce mijinta yana neman wasu a waje, kana ta zubar mini da ƙima, yara ƙanana suna ganina a banza a hoto, a wacce ba ta gamsar da mijinta".

Ta sassauta murya ta ce"Don Allah mu tattauna mu gyara, zan daina duk wasu abubuwa da ba ka so wallahi, me nake yi maka ne?"

Ta ba shi tausayi, ba wai son ta ne ba ya yi ba, kawai dai shi wannan son matan ƙaddararsa ne, yana jin Fatima ta yi masa kaɗan ita kaɗai, don haka yakr haɗawa da na wajen, duk da ya san wannan ba hujja ba ce, yana da niyyar ƙara aure, amma ba yanzu ba, sai ya gama lissafin da yake yi. A tsanake ya ce"Ni fa ba wani abu kike yi mini ba, kawai wannan ƙazantar taki ce ba na so, ke kenan ba za ki gyara jikinki ba? Gidana duk kin dafar mini da shi, komai ya fita daga hayyacinsa? A ce falo ma ba kullum za ki share ba, banɗaki zarni, sai dai na wanke nawa, wannan wace irin rayuwa ce? Sannan batun girkin nan, zan siyo komai na ajiye amma ke ba za ki sarrafa yadda ya dace ba, sai ki yi abinci babu fasali, wataran kamar cikina zai yi ciwo, na rasa ya ma kike ki yi wanj kaɗon, ki kwakkwaɓa abinci tun daga ido babu kyaun gani, ballantana kuma an kai baki, yanzu wannan jollop ɗin wake da shinkafar da kika yi yau tsakaninki da Allah a ido ba za a ce fate-fate ba ne? Kina yin adalci kenan? Wallahi ina son gayyatar abokaina cin abincin gidana, amma saboda gudun jin kunya sai na haƙura na share, idan na je gidan abokai na ga giriki kamar ba a ƙasar nan ba, kuma wallahi ba fi na yin cefane suka yi ba, kawai dai iyawa ce".

Ta ce"Duk na ji, kuma na karɓi laifina, amma mene ne zai haɗa waɗan nan abubuwan da neman matanka?"

Ya ce"To ban ganki fes ba kullum ke ga ki nan kamar dusa me zai hana na ga wata a waje na yi sha'awa? Ni fa zan fara gina wannan babban filin nawa, ina kallamawa aure zan yi in sha Allah!".

Fatima ta ji kamar ya caka mata kibiya, ta fara share hawaye kafin ta ce"Don Allah ka daina wannan maganar, wallahi zan gyara indai iya wannan ne matsalata na yi alƙawarin zan gyara".

Ya ce"To Allah Ya sa, idan kin gyara ni kuma na yi alƙawarin zan daina yin komai".

Sai kuma ya yi murmushi ya ce"Kenan saboda kin ji batun kishiya ne za ki gyara ko?"

Ta ce"A'a".

Ya ce"To sau nawa ina faÉ—a akan wannan abubuwan, amma kullum babu canji?"

Ta ce"Ni dai tun da na ce zan gyara shikenan, a bar maganar kawai".

Ya ce"Allah Ya ba mu ikon gyarawa".

Tun daga washegari ta fara ƙoƙarin gyarawa, ta cire ganda ta gyara gidanta tsaf, sannan ta cire girman kai ta kira yayarta a waya ta yi mata zancen rashin iya girkinta, ta ba ta shawararwarin da za su amfane ta, kamar na daidaita ruwan sanwar da kuma kula da magi, da rage yawan juya abinci, sannan ta ce mata duk abin da za ta dafa ta dinga faɗa mata da kuma adadin yawan ita kuma za ta dinga koya mata yadda za ta yi. Cikin ƙanƙanin lokaci hannunta ya fara faɗawa a girki, kuma tana kula da gidan da jikinta, don haka zaman nasu da Usman ya fara saituwa, shi ma ya ce mata ya daina kula mata, kuma ta yarda har zuciyarta, saboda ya canza takunsa, amma a zahiri bai daina komai ba.

08028966015
[28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/KHaNhtgfrBoAKxQ6GGKFyq

*WANI ZAMAN*

BY
SADIYA ABDULRAZAK

Marubuciyar
Sandar dukan uwargida
Ranar kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Matar shige
Iya ruwa
Wani auren da sauransu

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS

Labarin ya ƙunshi
Kishi
Kissa
Makirci
Cin amana

PAGE 4

Da farko da ta yarda cewar ya daina sun samu fahimtar juna, hankalinta ya kwanta sosai, suna zaman lafiya, kuma ɓangaren tsafta tana ta ƙoƙarinta. Da yake da kuɗi da kuma niyyar ƙara aure a ransa, babu jimawa ya kammala ginin sabon gidansa babba mai kyau, tun ranar da Fatima ta ga gidan nan hankalinta ya tashi, sam ba ta yi farinciki ba, saboda ganin ya yi gini mai ɓangare uku, wanda ko bai faɗa ba ya nuna dole yana da ra'ayin ƙara aure nan gaba, wanda take ganin ba zai taɓa yiwuwa ta yarda ta zauna da kishiya ba, a yadda ta tsani kishiya take kuma jin kishin mijinta ta saka a ranta ko za ta yi yawo tsirara sai ta hana shi ƙara aure, ko da kuwa za ta kauce hanya ne.

Usman jikinsa ya yi sanyi ganin yadda ta nuna ba ta yi farinciki da ganin sabon gidansa ba, ya ce"Amma Nana sai na ga kamar ba kya murna, ko gidan bai yi miki ba ne?"

Ta ce"Ya yi mana, kawai dai ban ganewa tsarin ginin ba ne".

Ya ce"Kamar ya?"

Ta ce"Daga ni sai kai da yaranmu me yasa za ka yi gini mai ɓangare uku?"

Ya yi murmushi ya ce"Nana kenan, kin san dai ina da ra'ayin zama da mata biyu ko? Wannan na farkon ɓangarena ne, babban falo ne wanda nakr fatan ya zama general, nan gaba idan na ƙara aure shi ne wajan zaman fira dukanku don a samu shaƙuwa da haɗin kai tsakaninku da yara bakiɗaya, ga ɗakin gadona a ciki, ga kuma banɗaki, sauran kuma kowanne babban falo ne da ɗakuna biyu da banɗaki, sai kitchen kin gansa a waje yake, ga store can a kusa da kitchen, ina fatan komai ya yi".

Zuciyar Fatima ta kumbura, ba ta san lokacin da hawaye ya sakko mata ba, ta ce"Au wai dama da gaske dole sai ka ƙara auren? Don Allah me nake yi maka? Na zata tun da mun sasanta tsakaninmu na daina abubuwan da ba ka so shikenan".

Ya ce"Haba Nana, ai ban ce yanzu kina yin wani abun ba, shi auren ra'ayina ne, zan yi ne ba don kin gaza ba, don haka ki kwantar da hankalinki, kina ɓangarenki tana nata, shiyasa na bari sai da na gina wadataccen gida".

Ta ce"Wai yaushe za ka gane ba zan taɓa iya zama da kishiya ba? Ni fa ba zan juri ganinka da wata ba, ka ga duk abin da kake buƙata wanda ya sa za ka ƙara auren ka faɗa mini, ni zan san yadda zan yi na gyara, na dinga yin yadda kake so".

Ya ce"Nana kenan, za ki iya zama mace biyu? Ina nufin za ki rabu gida biyu? Kuma kowacce kalarta da ban, surarta da ban? Ni biyun kawai nake so ba É—aya ba".

Ta ce"Shikenan Allah Ya ba ka iko".

Ta gama ganin gidan rai duk babu daÉ—i, suka tsayar da ranar tariya sati biyu, saboda a yi shirye-shiye cikin nutsuwa.

Tun da ta ji ra'ayinsa akan auren nan shikenan ta shiga damuwa, amma tana ta dannewa, ba ta som nuna masa zaƙewarsa akan ƙara aurensa, ta yadda zai gane tana da wani shiri a kai ya ɗauki mataki, ba ta manta abin da ya faru da wata ƙawarta ba, da ta dage ta hana mijin ƙara aure, ƙarshe sai ya yi mata lamfo ya yi kamar ya fasa, sai da ta kwantar da hankalinta ta yi zaton ya janye, rana ɗaya kawai ta ji labarin an ɗaura aurensa, kuma ya ɗakko wacce ta fi ta gogewa, haka ta zauna da kishiyar don dole, don haka take tsoron ita ma hakan ya faru da ita.
Chapter 4 · 0% Book details