Sashe 15
Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A ranar da Zainab ta tare a gidan, washegari ta ce masa ita fa ba za ta iya zama da kishiya ba, ko dai ya sake ta ko kuma ya saki matarsa. Duk da bai daina son matarsa ba, amma haka ya ji da ya rasa Zainab gara ya saki uwargidansa, uwar ƴaƴansa, don haka a ranar ya sake ta, ya ba ta kuɗin mota ta koma garinsu. Zainab ta dinga murza kambunta, tana gara kan bawan Allah, kafin danginsa su duƙufa addu'a da neman taimako, da ƙyar suka janyo shi ya zo gida, lokacin wata uku da auren, ba su bar shi ya tafi ba suka dinga yi masa maganin karya sihiri har sai da ya dawo hayyacinsa, ƙarshe ta waya ya saki Zainab tun kafin ya koma garin, amma fa a wannan watannin har filaye biyu ta siya da kuɗinsa.
Mutuwar aure sam ba ta damun Zainab, tana gama idda ta samu wani mai mata ta aura, shi ma sati É—aya da auren ya saki uwargidan, iyayensa suka tilasta masa sai da ya mayar da ita, wata biyu da auren, wataran Zainab ta yi masa barbaÉ—e a cikin abinci, tana cikin barbaÉ—awa ta ji muryarsa zai shigi falon, don haka da sauri ta juye maganin ba ta tsaya juyawa ba ta shige É—akinta.
Ranar girkin kishiyarta ne, ita ta gama jera abincin ta tafi wanka, Zainab ta samu wannan damar, mai gida ya watsa ruwa ya zo ya zauna zai ci abinci, uwargidan tana buÉ—ewa gabanta ya faÉ—i, ganin koren abu kamar kuka an barbaÉ—a akan jollop É—in shinkafar, ta kalle shi, shi ma ita yake kallo, a raunace ta ce"Mene ne kuma wannan?"
Ya yi mata kafirin kallo ya ce"Ni kike tambaya? Me kika zuba mini a abinci? Kashe ni za ki yi ko mallake ni za ki yi?"
Ta ce"Wallahi ban zuba maka komai ba, ƙalau na ajiye abincin nan, sai dai ko Zainab ce ta fito ta saka".
Ya ɗaga murya ya kira Zainab ɗin, ta fito gabanta yana faɗuwa, amma sam ba ta nuna a fuska ba, ta ƙaraso tana karairaya ta ce"Alhajina ashe ka shigo, sannu da zuwa".
Fuska a haÉ—e ya ce"Me kika zuba mini a cikin abinci?"
Ta ce"Kamar ya?"
Ya ce"Ga ki, ga ta, ga abincin nan, wallahi idan ba ku fitar da wacce ta zuba mini maganin nan ba kowaccenku a gidansu za ta kwana".
Zainab ko É—ar ba ta ji ba, saboda ita dama bayan auren ma duk ta ji ya fice a ranta, ita kuwa uwargidan sai rantse-rantse take yi, da Alhaji ya ga da gaske babu wacce za ta amsa ita ce, sai ya shiga É—akinsa, ya fito da takardu biyu a hannunsa, ya bawa kowaccensu É—aya, duk ya yi musu saki É—ai-É—ai.
Zainab sam ba ta yi sha'awar komawa gidansa ba, ita kuma uwargidan ƙarshe babarsa ta sa ya mayar da ita, ta ce ai amaryar ce ta zuba, tun da duk tsayin zamansu da matarsa haka bai taɓa faruwa ba sai yanzu da ya yi wannan auren, don haka ya mayar da matarsa suka cigaba da zama.
Daga nan sai ta dakata da auren, kawai take barikinta, har ta haɗu da wani abokin Usman, suke sheƙe ayarsu, shi kuma ya yi wa Usman hanya shi ma suka ɗinke da ita suke aikata masha'arsu, da ya fara gajiyada ita ya so zame mata sai ta nuna masa ita fa da aure take son shi, za ta shiryu indai zai aure ta, Usman ya nuna bai san zance ba, sai dai bai san ya riga ya shiga tarko ba, suka tashi tsaye suka dinga banka masa asiri har suka karkato hankalinsa ya amince zai aure ta.
Wannan ita ce Zainab, matar da za a É—aura musu aure da Usman a yau, shin Fatima za ta iya kishi da ita kuwa? Za ta iya fitar da ita daga gidan? Bayan dai bin bokaye da take yi, ita É—in rainon uwa Æ´ar bariki ce.
Daidai yadda bokan nan ya faɗa mata za a ɗaura auren nan ko mistake ɗin sakan ba a ƙara ba aka ɗaura, Fatima tana ta yaƙe a cikin mutane, sai bayan an ɗaura auren ta tuna ba ta jiƙa maganin ba, ta tashi ta jiƙa ta saka a banɗakinta ta ɓoye ta rufe da mukulli, tana ta fargabar aikin zai ci ya saki amarya ko a'a? Da magriba aka kawo amarya ɗakinta, kowa ya watse sai ƙawayenta masu siyan baki, wanda Fatima take rayawa a ranta tare za su koma gida da amaryarsu, ita ma a ƴan'uwanta babu wanda ya zauna, sai ƙanwarsa Hasana da ta ce za ta kwana biyu.
Ana yin sallar isha'i ta yi wanka da wannan maganin, ta zo falo ta zauna, tana jin shigowar motarsa ta ɗakko kwallin ta rambaɗa har ya zazzago ƙasan idonta, ta fito harabar gidan ta kame, shi da abokansa ne biyu, hango ta da ya yi ta riƙe ƙugu ya sa shi ƙarasawa wajenta, ya ce"Nana, akwai wani abu ne?"
Ta kalle shi, shi ma ita yake kallo, ido cikin ido suka kalli juna, ta ce"Usman ina yi maka umarni da ka saki amaryar nan taka yanzu-yanzu".
Usman ya ji gabansa ya faɗi, zuciyarsa ta buga da ƙarfi, ya tsaya yana kallonta.
LAST FREE PAGES!
A nan za mu dakata da free pages, akwai tirka-tirka kala-kala a gaba, za ku ji dalilin sakawa labarin ban wani zaman, sannan za ku ji yadda za a kwashe tsakanin Fatima da Amaryarta, shin wace ce mai nasara? Kowacce dai kar ta san kar! Littafin na kuÉ—i ne akan naira 500, domin jin yadda za ta kaya ki saka kuÉ—in karatunki ta nan
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay
Shaidar biya ta nan
08028966015