Sashe 6
Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya yi guntun tsaki ya ce"Wai ni kam Nana mene ne muhimmancin wannan gwal ɗin da kika ƙwallafawa rai ne? Idan kadara kike son ajiyewa ai gara ma ki sayi fili ko ginannen gida, kin ga kya saka ƴan haya, amma ke komai gwal, sai ka ce dai wani abu mai muhimmanci ga rayuwarki?"
Ta yi shiru tana jin zafin kalamansa.
Ya ce"Aure fa zan yi, ƴar wasu zan aura, kin ga na taimaja musu sun aurar da ƴarsu, sannan ita ma na taimaka mata ta zama matar aure, kuma ta zama uwar wasu a nan gaba, za a haifi zuri'ar da za su taru su zama abun alfahari in sha Allah, kuma bazawara ce da ɗanta ɗaya, na ce ma zan riƙe mata ɗan, kin ga nan ma an taimaki yaron zai rayu a gaban mahaifiyarsa cikin aminci, yanzu wannan bai fi siyan gwal muhimmanci ba? Ki duba girman gidan nan, a ce ki rayu ke kaɗa? Abokiyar zama ai tana da daɗi, ko motsinta kika ji zai rage miki wata kewar".
Fatima ta ce"Hakane, Allah Ya tabbatar muku da alkhairi".
Ya ce"Ya tabbatar mana dai. Fatima ki kwantar da hankalinki don Allah, ni ba nufina munana miki ba".
Ta ce"Ni hankalina a kwance yake, Allah Ya kai mu wata ukun".
Ya ce"Amin".
Duk da ta ga yadda aikin Malam ya ci da wuri a wancen yunƙurin ƙara auren nasa, amma sai da ta sake shiga fargaba, washegari ta nemi rakiyar ƙawarta kamar lokacin farko, suka tafi, a hanya Zulaiha take cewa"Indai bai gaji na ke ma ba za ki gaji ba, maza sai jarabar masifa, me matan wajen suka fi mu? Wallahi kafin ya bar batun auren nan gabaɗaya ke ba ki ga yadda na rame ba, saboda ko abinci rage ci na yi, ba na bacci, da ya ɗakko magana na rushe ta sai ya sake nemo wata, kamar wanda aka yi wa baki ko gorin auren, sai da na tashi tsaye gyam sannan na cire masa son abun, yanzu ba ga shi nan ba komai ya zama labari? Ke ma kar ki gaji, yanzu ma aka fara wasan, dole da mu kaɗai za su zauna wallahi, kalle ki fa me kika rasa da yake neman wata? Da kyaunki da komai".
Fatima ta ce"Namiji kenan! Ni wallahi fargabata É—aya kar ta shigo ta raba ni da shi, son mijina nake kamar na haÉ—iye shi na huta wallahi, kuma shi ne gatana".
Zulaiha ta ce"In sha Allahu ƙwalelensu, mazajenmu namu ne, can su je su nemi samari daidai su".
Haka suka yi ta fira har suka ƙarasa gidan malamin. Yau ma dai ta zayyana masa abin da ya kawo ta, tare da yaba masa akan wancen aikin farkon da ya yi mata, Malam ya yi murmushi ya ce"Idan zai yi yunƙuri sau dubu, mu za mu dankwafar da shi sai dubu, wannan ƙaramin aiki ne".
Ya ba ta irin maganin da ya ba ta a lokacin farko ya ce ta saka masa a abinci, sannan ta yi masa ƙorafin kuma ba ya sakar mata kuɗi yadda ya kamata, sai ya ba ta wani abu ɗan ƙarami a leda ya ce ta yi matsi da shi, ta tabbata ya kusance ta a ranar, wannan matsalar za ta kau, ta sallame shi suka tafi, a cikin kuɗin da take tarawa na siyan gwal ta bada kuɗin, sam ba ta damu ba tun da ta ji zai sakar mata bakin aljihu.
Ta dawo gida da farinciki, yau ma haka ta yi girki ta saka masa magani, sai da ma ta dafa masa abincin da ya fi so, ya dawo tana ta tarairayar shi, Mu'az ya zo ya zauna zai ci abincin, Fatima ta ce"Kai ba ka ci abincinka ba?Tashi dalla".
Usman ya ce"To mene ne idan ya ƙara a nawan? Ya ɗakko cokali ɗaya zai kai masa bakinsa".
Da sauri ta janye yaron tana cewa"Wannan ai ba tarbiyya ba ce ba, idan bai ƙoshi ba ne sai na ƙaro masa wani".
Abun ya bawa Usman mamaki sosai, saboda ya ga ba yau suka fara cin abinci da yaron ba, kuma ba ta taɓa magana ba sai yau ɗin".
Ya ce"Haba Nana, mene ne idan uba ya ci abinci tare da É—ansa? Kamar yau muka fara ci?"
Ta ce"Ni dai kawai ba zai ci ba, naka ne kai kaÉ—ai, idan zai ci na zuba masa nashi".
Usman ya ce"Ai kuwa ba ki isa ki hana shi ba, dole tare za mu ci".
Fatima ta ce"Wallahi ba zau ci ba" Ta É—auki É—an ta mayar da shi gefe.
Usman ya kalli abincin ya kalle ta, ya yi mamakin yadda ta haƙiƙance, duk da ba ya zarginta amma sai da ya ji ɗar a kan abincin, ya ce"To wai mene dalilinki na hana shi ci? Tun a baya ba ki hana ba sai yanzu?"
Ta ce"A islamiyya ne fa aka yi gargaɗi akan hakan, an ce wannan ba tarbiyya ba ce, saboda idan aka bar yaro yana cin abinci da babansa nan gaba sai a yi baƙo ya zo ya saka masa hannu, ka ga kuma ai za a ji kunya".
Ya ce"To ke ai sai ki sakko mu ci ko? Idan ka ci da matarka dai ai babu laifi ko?"
Ta ce"Ni ai na ci na ƙoshi kuma".
Ya ce"Lallai wannan islamiyyar ashe dai ba na biyan kuÉ—in wata da na littafai a banza, amma idan aka ci aka ragewa yaro fa?"
Ta ce"Wannan ai babu damuwa, kuma wallahi ya ma ƙoshi".
Usman ya ce"Ai shikenan" Ya ja abincin ya ci ya ƙoshi, ya rage ɗan kaɗan ya ba wa yaron.
Yana cewa"To ga shi na rage maka".
Fatima ta É—auke kwanon ta ce"Allah ba zai ci ba, sai dai na zubo masa wani".
Ya ce"Ke za ki ci wannan É—in?"
Ta ce"Ni ai na ƙoshi".
Ya ce"Ai kuwa ko ki ci ko ya ci, don ba za a yi asararsa ba, ya yaro yana son abu za ki hana shi ci?"
Ta ce"Kawai ni dai ba zai ci ba, saboda idan ya cika cikinsa sosai kashib dare yake yi mini"
Usman ya ce"Idan ya yi ki tashe ni zan wanke masa, amma Allah sai ya ci abincin nan".
Ya zo É—aukar abincin Fatima ta É—auke kular, ya tsaya yana kallonta na Æ´an sakanni kafin ya ce"To Nana ko dai wani abun kika zuba min a abincin wanda ba kya so É—anki ya ci ya cutu? Maganin mutuwa ne ko na mallaka?"
Gabanta ya faÉ—i, ta ce"Wallahi tallahi babu É—aya".
Sai kuma ta fara kuka ta ce"Kenan ma zargina kake yi ko? Ni za ka zargi zan zuba maka mugun abu a abinci? Me ka yi mini da zan kashe ka? Akan me zan mallake ka?" Ta rushe da kuka.
Ya ce"To idan ba haka ba ne ba ba ni kular nan".
Ya miƙo hannu zai karɓa ta noƙe ta, ya ce"Nana zargina ya tabbata kenan ko?"
Ta ce"Wallahi ban zuba maka komai ba".
Ya ce"To ke ki ci na gani".
Ta ce"Na ƙoshi".
Ya ce"Ko kin ƙoshi na tabbata akwai wajen da cokalu ɗaya zai zauna, don haka dole ki ci".
Ta ce"Wallahi na ƙoshi, kamar zan yi amai ma".
Usman gabansa ya fara faɗuwa, ya ce"To shikenan, bari na sanarwa mahaifiyata tun yanzu, don idan na mutu a samu sauƙin bincike".
Da jin haka sai ta ajiyr masa kular a gabansa tana sosa kai ta ce"Ni fa dama...".
Ya ce"Dama me?"
Ta ce"Dama maganin maza ne na saka maka, ka ga idan Mu'az ya ci sai a samu matsala".
Ya yi tsaki ya ce"Allah Ya kyauta, maganin maza kuma? Yanzu ni duk wannan yanayin nawa da nake ma ganin kin yi mini kaÉ—an ashe ke kallon lusari kike yi mini? Ba na kiranki yadda ya kamata ne?"
Ta ce"A'a kana kirana".
Ya ce"To akan mr za ki ƙara mini ƙarfi?"
Ta ce"Na ga aure za ka ƙara shiyasa na ce bari na fara tsuma ka, ka ga masu mata biyu ba sa iya bawa kowacce hakkinta yadda ya kamata, ni kuma ka sabar mini da jarabarka".
Har ransa ya yarda, don haka ya yi Æ´ar dariya ya ce"Ki ce dai kawai tsuma ni kika fara yi, ai kuwa indai na ga kyaunsa sai na ba ki tukuici".
Ya É—auki sauran abincin ya ce"Irin wannan ai bayani ake yi, sai na cinye duka na siÉ—e kwanon, mu ai a nan muka fi kauri".
Ta yi dariya, ya cinye abinci duka, ta fesa wanka ta yi matsi da wannan maganin ta bi shi É—akinsa.
Bayan kwana biyu tana ta zuba ido ta ga ya zo ya faÉ—a mata ya fasa auren, amma ta ji shiru, sannan ta sake tada masa da zancen siyan gwal É—in nan ya ce ba shi da kuÉ—i, shiyasa duk hankalinta ya tashi, ta fara tunanin wannan aikin dai bai yi ba, sati É—aya da yin haka ta koma wajen malamin nan, ta faÉ—a masa aiki fa bai ci ba.
Malam ya ce"Aiki ya ci, ki jira lokacin ki gani, idan an yi auren nan to sai dai a lahira, amma a gidan duniya dai wannan magana ta mutu miÉ—is".
Duk da haka hankalinta bai kwanta ba, suna zaune da shi wataran take cewa"Ni baban Mu'az aurenka saura wata biyu ko?"
Ya yi shiru kamar bai ji ta ba.
Ta ce"Magana fa nake yi".
Ya yi guntun tsaki ya ce"Auren nan fa na fasa shi tun tuni".
Wani farinciki ya lulleɓe ta, amma ba ta nuna ba, da alamaun mamaki a fuskarta ta ce"Amma me yasa?"
Ya ce"Wallahi kawai, ji na yi yarinyar ta fita daga raina gabaÉ—aya, kawai dai Allah Ya yi ba matata ba ce".
Fatima ta ce"Ikon Allah, amma abun da mamaki, to kuma ka karɓo kuɗin auren da aka kai?"
Ya ce"A'a na bar musu, tun da dai kin ga ni ne na ce na fasa, kar abun ya yi musu yawa".
Fatima ta ce"Hmm kai dai kawai kuɗin ya yi maka yawa ne, ka yi niyyar yi mata kyauta, amma ban da haka ni ina zaune ba ka ba ni ba, za ka je ka ce ka barwa wata kuɗin aure? Ka ga kenan ka nuna min ta fi ni daraja da ƙima a idonka".