← Book details Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 15

Sashe 12

Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam ya ce"Kuma kin juye masa duka wannan maganin ya cinye a abinci?"

Ta ce"Wallahi ya cinye".

Ya ce"To zan ba ki wani da za ki yi matsi da shi, idan kin yi ki tabbata kun keɓe a ranar, idan za ki yi matsin ki dangwalo maganin a ɗan yatsanki, ki kira sunan shi sau bakwai, ki tofa a jiki, sannnan ki rufe idonki kina ambatar sunan shi kina cewa ya fasa auren nan har sau bakwai, sannan ki yi amfani da maganin, idan kuka gama kawai ki kalle shi kai tsaye ki yi masa umarni da fasa auren, duk taurin kansa ba zai yi miki musu ba".

Ya ba ta maganin a wata ƙaramar kwalba, ya ce mata dubu hamsin ne, ta yi masa transfer, ta yi godiya ta tafi, tana ta jimamin yadda take ɓarnatar da kuɗinta, wanda tana tarawa ne don siyan gwal, amma ta wani fannin ta san dabara ta yi, don idan ba ta yi yadda ta yi an fasa auren ba, ko ta sayi gwal ɗin na banza ne, don ita a nata ganin a ce kana da kishiya shi ne babbar gazawarka a rayuwa, don haka ko za ta yi yawo tsirara sai ta hana auren nan.

Ƙarfe goma na dare ta gama komai, ta fesa wanka, ta ɗakko maganin nan ta dangwalo shi, ta kira sunan Usman sai bakwai, sannnn ta rufe ido ta ce"Usman ka fasa auren nan, Usman ka fasa auren nan". Haka ta maimaita har sau bakwai, sannan ta yi amfani da shi, ta haye gadonsa ta kwanta tana jiran dawowarsa.

Sanda ya dawo ya gama abin da zai yi ya kwanta, ya matso kusa da ita har wata ajiyar zuciya ta sauke, saboda ta gama yarda yau burinta zai cika, tun da har zuciyarta ta yarda da maganin nan, bayan sun gama mu'alar ita ce ta fara yin wanka, kafin ya fito daga nashi wankan, ta zauna a gefen gadon tana ta kintsa kanta, da auna maganar da za ta yi masa ɗin, tare da taraddadin karɓuwarta ko akasin haka.

Ya fito ya shirya zai kwanta, ta kalle shi ta ce"Ina da magana".

Ya ce"To ina jinki".

Ta saka idonta a cikin nasa gabanta yana faÉ—uwa ta ce"Usman ka fasa auren nan".

Shi ma ji ya yi gabansa ya faÉ—i, mamakinta ya kama shi, sai ya ji kamar ma kunnuwansa ne ba su ji daidai ba, don tabbatarwa sai ya ce"Me kika ce Nana?"

Ta ce"Usman ka fasa auren nan".

Ya ce"Ikon Allah! Na fasa aure kuma? Me yasa?"

Zuciyarta ta tsinke, don ta san wannan karon ma aikin bai yi ba kenan, ta ce"Saboda ba na so, ni Fatima ina yi maka umarnin ka fasa auren nan".

Ya fara yi mata wani kallon ba ki da hankali, kafin ya ce"Ke Fatima uwata da kika haife ni, ko ke Fatima da kika auro ni kike ci da ni?"

Zuwa yanzu kam ta sare, kawai ta saddaƙar aikin bai yi ba, don haka ta fara hawaye ta ce"Ba haka ba ne, amma wallahi zuciyata zafi take yi, ba zan juri ganinka da wata ba, don Allah ka janye auren nan, ka faɗa mini matsalata, na yi alƙawarin zan gyara".

Usman ya nemi waje ya zauna, ya tausasa murya ya ce"Haba masoyiyar matata, wai me yasa kika kasa fahimtata ne? Na faÉ—a miki fa zan yi auren nan ne ba wai don kin gaza ba, na faÉ—a miki dalilina ina da ra'ayi ne, kuma mun gama magana da Zainab sai na dawo na ce ba haka ba? Ki kwantar da hankalinki za ku zauna lafiya, zan yi wa kowa adalci".

Gyaɗa kai kawai ta yi, ta fita a guje ta koma ɗakinta, yana ta kiranta ba ta dawo ba, ta saka sakata ta kwanta a falo ta saki kuka sosai, kuka biyu take yi, da na baƙincikin aiki bai yi ba, da na takaicin asarar kuɗinta, ta yanke ta bar wannan malamin za ta nemi wani kawai.

Washegari ta shiga gidan maƙociyar nan tata, hankali tashe take faɗa mata aikin nan fa bai yi ba, ta yi asarar kuɗinta, Zulaiha ta ce"Daɗina dake gajen haƙuri".

Fatima ta ce"Kin ga babu wani gajen haƙuri, abin da ya ce nan take zai yi aiki, ai ya kamata na ga aikinsa a lokacin idan mai kyau ne, ni dai idan akwai wani malamin ki haɗa ni da shi kawai".

Zulaiha ta ce"Akwai su, akwai mutum biyu da yayata take aiki da su, sai na haɗa ki da ita ƙila a dace".

Fatima ta karɓi lambar yayarta, nan take ta kira ta, suka yi mata bayani, suka yanke gobe Fatima za ta je gidanta sai ta raka ta. Washegari ta tambaye shi za ta je gidan yayarta, dayake gidan da nisa shiyasa a wannan karon ta nemi izininsa, don kar su kai dare, ya ce yana da uzuri da ya kaita, ya ba ta kuɗin mota ta tafi.

Kafin su je ta shirya Fatima kawai take jira, suka gaisa, suka tafi, a hanya tana ta ba ta labarin aikin malamin nan yadda yake da kyau kamar yankan wuƙa, Fatima ta ji hankalinta ya kwanta sosai. Bayan sun je wajen ta yi bayanin so take a fasa auren, shi ma ya yi dube-dubensa ya ce zai iya, ya ba ta wani magani kala biyar ya ce za ta samo zuciyar rago ta dafa ta da wannan maganin ta cinye ta shanye romon, gabanta ya faɗi ta ce"Zuciya kuma Malam?"

Ya ce"Ƙwarai kuwa, amfanin hakan shi ne kamar kin cinye zuciyarsa ne, ke kaɗai zai ji yana so har abada, kuma da ke kaɗai zai iya rayuwar aure, sannan zai ƙara son ki, zai dinga bin umarninki sau da ƙafa, zai manta ko hanyar gidan su yarinyar nan ma".

Fatima ta ce"Amma Malam ban san wanda zan sa ya siyo mini zuciyar ba".

Ya ce"Idan kika ba da kuÉ—in babu damuwa, ni zan saka matata ta dafa miki".

Fatima ta biya kuɗin, ta yi godiya suka fita daga gidan yayar Zulaiha tana ƙarfafa mata gwiwa. Washegari aka dafa zuciyar rago, aka kai gidan Zulaiha, ita kuma ta aikawa Fatima, tana buɗe kwanon ta ji ƙyanƙyami ya kama ta, ba komai take iya ci a nama ba, amma yau saboda gudun kishiya sai ga shi ta zauna za ta ci zuciyar rago.

"Zuciyar Usman zan ci, bayan na ci zan mallake shi, zai dinga bin umarnina, zai daina son kowace mace sai ni, da ni kaÉ—ai zai yi rayuwar aure". Ta faÉ—a kamar yadda aka ce ta faÉ—a kafin ta fara ci.

Tama ci tana runtse ido, haka ta daure ta cinye ta, ta shanye romon duk ɗacinsa, tana fatan ƙarshen wahalarta kenan.

Bayan sati ɗaya ta ji shiru Usman sai ma shirye-shiryen bikinsa kawai yake yi, yanzu ya ma rage zama da ita su yi fira, hankalinta bai tashi ba sai da ta ji an kai kayan lefensa, kuma wai bikin saura sati ɗaya, a maimakon sati biyu, don rage sati ɗaya aka yi, a ranar ji ta yi kamar za ta haukace, ko tambayarsa ba ta yi ba ta je gidan malamin nan, ta yi masa bayani, ya buga ƙasa ya ce mata aikin ya wuce zatonta, babba ne, idan za ta iya ba da dubu ɗari biyu zai yi mata abin da za a fasa cikin kwana biyu.

Gabaɗaya dubu tamanin ne a account ɗinta, don haka ta ce masa za ta dawo. A ranar da daddare ta tuntuɓi Usman da zancen kuɗin kayan lefenta, nan take ya saka mata dubu ɗari biyar ya ce ita da yara, ai kuwa washegari ta je ta kaiwa malamin nan ɗari biyu, ya ce ta je gida za ta ga aiki nan da kwana biyu.

Kwana biyu ta yi, babu wani canji, aure saura kwana biyar, hankalinta ya tashi sosai, ta je tana yi wa malamin nan kuka, ya ce mata zai sake ƙaimi wajen aikin, amma zai shiga wata halwa, kar ta dawo sai bayan kwana uku.

Cikin kuka ta ce"Ai lokacin saura kwana biyu auren".

Ya ce"Kar ki damu, ko saura minti biyu ne mu za mu canza komai".

Ta bar gidan jiki duk a mace, sam ba ta yarda da cewar aikin nan zai yi ba, ta biya ta gidan wata ƙawarta wacce suka yi makaranta tare, suka gaisa take tambayarta ya ta ganta a cikin damuwa? Fatima ta faɗa mata halin da take ciki, na kishiya da za a yi mata.

Ƙawar tata ta ce"Ai kuwa kin ga mijin Saddiƙa Habibu malami ne, yana ba da taimako, da kin gwada zuwa wajen nashi".

Fatima ta ce"Me zai hana? Don Allah ba ni lambarta".

Ta ba ta lambar, ta kira ta a waya suka gaisa ta ce mata za ta zo gidanta, ta yi mata kwatance, duk da ta ji da nisa amma sai ta ji dole ta je a yau ɗin, don haka ko gida ba ta koma ba ta wuce gidan ƙawar tata.

Shi ma gida ne mata baje a wani ƙaton ɗaki masu bin layi, shi kuma yana wani ɗakin a zaune, ta shiga ɗakin ƙawar tata a ranta tana mamakin ita kuwa Saddiƙa me ya kai ta auren boka?

Sai da ta yi awa uku a gidan, a hakan ma tsallaken layi aka yi ta ga Malamin, saboda Saddiƙa ta roƙa mata alfarma.

Fatima ta zayyana mata buƙatarta, ya buga ƙasa ya share, ya ɗago ya kalle ta ya ce"Hajiya ke ƙawar matata ce, kin san ko ina cuta ke ba zan cuce ki ba saboda albarkacin matata ko?"

Ta ce"Haka ne, kuma na gode sosai".

Ya ce"To a gaskiya sau ɗaya nake buga ƙasa na ga sakamako, na buga kuma abin da ta nuna mini babu daɗi".

Zuciyarta ta buga da ƙarfi, kamar za ta yi kuka ta ce"Me ka gani?"

Ya ce"Na ga cewar wannan auren tabbatacce ne, babu makawa sai an yi shi, domin har hango ta na yi a cikin gidanki a zaune da Æ´aÆ´anta".

Fatima ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku, yanzu babu wani abun yi?"
Chapter 12 · 0% Book details