← Book details Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 15

Sashe 8

Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali suka samu shaƙuwa sosai, ta yadda ita ma kanta wannan soyayyar ɓoyen ta ishe ta, don haka ta yarda da tayin da Usman yake ta yi mata na cewar su dinga haɗuwa a gidansa, ranar da ta fara zuwa da magriba ne Fatima ta tafi makaranta, a ɗakinsa suka zauna a nan falo suka yi firarsu mai tsafta, ana fara kiran sallar isha'i ta tafi, tun daga nan sai Usman yake dawowa da wuri, idan ya dawo saa ya laɓe a unguwar sai ya tabbata Fatima ta tafi makaranta sannan ya yi wa Zahra waya ta zo gidan, tun suna firar arziƙi har Usman ya yi nasarar yaudararta da kalaman ƙarya da nuna mata ai ita bazawara ce don ta ba shi kanta ba wani abu ba ne, kuma ma ai shi ne zai aure ta, ta yarda saboda son da take yi masa, da kuma yawan kyautar da yake yi mata musamman ta kuɗi, suka ɗinke suke ta sheƙe ayarsu, suna gamsar da juna sosai, domin Zahra har maganin mata masu mugun kyau take siya kamar wata matar aure, kawai don ta farantawa Usman, don haka komai ta ce tana buƙata babu musu yake bata shi, amma sam babu niyyar aurenta a ransa.

Ko da wasa Fatima ba ta taɓa hasashen akwai matsala a gidanta ba, rana ɗaiɗai ne ba ta shiga gidan su Zahra, ko ba ta shiga ba ƴaƴanta za su shiga, wataran suna fira da Umma zancen gwal ɗin nan ya tashi, silar wata da ta gani a tiktok ta sha gwala-gwalai tana rawa da ƙawa, ta yi ƙwafa ta ce"Hmm! Allah kai damo ga harawa".

Ta ƙara da faɗin"Wai ban da lalacewar zamani a ce mutum yana da kuɗi ba zai biyawa matarsa dukkanin buƙatunta ba?Wallahi Umma Usman yana da kuɗin da zai siya min gwal ɗin nan na miliyoyi ma, amma na ce masa ko ƙaramin ne ina so, duk da haka ya kafe, idan bai siya mini ba wa zai siyawa?"

Umma ta ce"Gaskiga dai, amma ki bi shi a hankali da kyautatawa sai ya siya miki ko ba yanzu ba".

Suna ta tattauna zancen, Zahra tana jin haushin Fatima, kuma ta saka a ranta za ta gwada roƙonsa gwal ɗin ta gani, tun da ya sha faɗa mata ta fi Fatima daraja a wajensa, idan kuwa ya siya mata ɗin gaskiyarsa ta tabbata.

Kamar wasa ta faɗa masa tana son ya siya mata gwal ko ƙarami ne, ya ce babu damuwa, ba ta taɓa zaton da gaske yake ba, sai ga shi bayan sati ɗaya ya kawo mata ɗankunne da zobe na gwal ɗin, a ranar ta ji ta ƙara son shi sosai, farinciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, ta kuma sake raina Fatima don ta gama yarda hoto ce kawai a wajensa, kuma ta sake sakin jiki ta yarda da gaske aurenta zai yi.

Sati ɗaya da siyan gwal ɗin nan Fatima ta samu labarin wannan alaƙa tasu, domin bakin Zahra bai iya shiru ba, sai da ta faɗawa ƙawarta wata buduruwa a layin mijin maman Mu'az ya siya mata gwal, har ma ta nuna mata shi, ita kuma abun ya ba ta mamaki ta san da alaƙarsu, ta sana haɗuwa a gidan Fatiman suna yin harkarsu, amma wannan siyan gwal ɗin ya sa ta ji tana yiwa Zahra hassada, a ce ita tana buduruwa bai ce yana sonta ba sai bazawara? Ta yi niyyar tona mata asiri, don haka ta samu mahaifiyarta ta sanar mata, babar Shamsiyya da farko ƙaryatawa ta yi, sai da ta dinga yi mata rantsuwa sannan ta yarda, ai kuwa a ranar ta saka hijjabinta ta shiga gidan Fatima, duk da ba ta shiga gidan amma ta ji dole ta shiga ta sanar da ita halin da take ciki.

Suka gaisa da Fatima, ta kwashe komai ta faɗa mata a tsanake, sosai hankalinta ya tashi ta fara kuka, don tabbas ta san mijinta zai aikata, kuma ta yi mamakin cin amanar da Zahra ta yi mata, da ma duka ƴan gidan bakiɗaya, don ba za ta taɓa yarda da cewar babu sanin Umma ba, tun da har abu ya kai ga siyan gwal, ita fa siya mata gwal ɗin nan har ya fi kawo ta cikin gidan da yake yi zafi a wajenta. Kasa ɗaukar shawar maman Shamsiyya ta yi na cewar ta fake su ta kama su da hujja, kawai ta yanke a yau za a yi ta, ta ƙare.

08028966015
[28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt

WANI ZAMAN*

BY
SADIYA ABDULRAZAK

Marubuciyar
Sandar dukan uwargida
Ranar kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Matar shige
Iya ruwa
Wani auren da sauransu

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS

Labarin ya ƙunshi
Kishi
Kissa
Makirci
Cin amana

PAGE 7

IMZEEDVENTURE
Duniyar kayan kitchen ƴan yayi dake maida mata ƴan ƙwalisa a gidajensu.

Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa?

Kayan yara masu kyau unique na yan gayu?

To shiga link din grp na Imzeedventure🥰🥰🥰 Kisha mamaki🗣️ idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo!

Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi🥳🥳.

IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar ƙyale-ƙyale ce da ƙayatarwa da mata sukafi buƙata musamman ƴan ƙwalisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu.

Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link É—in namu dai domin ganema idanunki.

https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1.

Koki tuntuɓemu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_*

Muna da account a Instagram @imzeed _venture.

Karku bari ayi babu ku,😘😘😘😘😘 Nima Sadiya Abdulrazak tuni na antaya🏃

Fatima ta cika ta yi fam tana jiran dawowarsa, bayan ta gama cin kukanta, har ɗakin nasa ta shiga ta tsaya kawai take kallo da tunanin wai da gaske yana kawo mace ɗakin nan? Ta hau kan gadon da ita ma take hawa? Ashe dole Zahra ta dinga yi mata wani gani-gani, Zahra ta ba ta mamaki sosai, ba ta taɓa zaton za ta iya yin haka ba, kuma da mijin maƙociya, abun ya ma wuce a haɗu a wani wajen wai har cikin gidan aurensa saboda rainin hankali, ita kam me baban Mu'az ya ɗauke ta ne?

Usman ya dawo gida ana idar da sallar magriba, hankalinsa kwance, har da tsarabar gasassun kaji, wanda ya siyo su da sunan Zahra, domin sun yi da ita yau za ta shigo, da ya tarar da ita Fatima a tsaye a falon sai da ransa ya ɓaci, ya ce"Nana me ya hana ki zuwa makaranta yau?"

Ta zabga masa harara ta ce"Ok ka so ka zo ka ga ba na nan ko? Ka so ka kawo wacce ka saba kawowa ku aikata masha'arku ko? To ai a gabana ɓa za ku iya yi, tun da har ka iya kawo mace cikin gidan aurenmu ai kuwa saura ƙiris ka fara yin iskancinka a gabana, to yanzun ma me ya rage?"

Tun da ta fara magana gabansa yake faɗuwa, kuma sam bai yi mamaki ba tun da dama ya san wannan harƙalla da suke yi tsakaninsa da Zahra riski ce, komai zai iya faruwa, musamman da abun ya yi nisa sosai a tsakaninsu, amma ya dake ya aro suffar mamaki ya shimfiɗa a fuskarsa har da haɗe gira ya ce"Ke me kike cewa ne? Me kike nufi? Zargina m kike yi?"

A hasale ta ce"Ai ya wuce zargi, ashe Zahra kake kawowa gidan nan kuna cin amanata? Wai abun ya kai har ma ta samu darajar da ka siya mata gwal?"

Ya ce"Anya yau ba ki sha wiwi ba kuwa? Ni ne nake kula wata har nake kawo ta gidan nan? Wace ce kuma Zainab?"

Ta ce"Zahra na ce! Kar ka raina mini hankali mana, wallahi ba za a yi maka ƙarya ba, yau da a ce neman mata ba halinka ba ne da zan yarda, to amma na riga na san halinka ko me aka ce ka yi akan mata ba zan musa ba wallahi, don haka ka aikata!".

Sai ta fashe da kuka ta ce"Amma baban Mu'az har cikin gida? A gadon da muke raya sunna? Abun naka har ya kai haka? Ka cuce ni ka zubar mini da ƙima a idon duk wanda ya sani, dama kai ba ka da sauran mutunci..."

Ya ce"Ke dalla dakata a nan haka, ban gane ba fa, ke anya ba ki da aljanu kuwa? Uban waye ya ce na taɓa kawo mace gidan nan? Wace ce Zahra? To ki wuce mu je wajen munafukar da ta faɗa miki wannan ƙaryar, wallahi sai na yi shari'a da ita!".

Ta ce"Wannan borin kunya kake yi wallahi, na saa halinka don haka kp maƙiyina ne ya kawo min labarin nan zan gasgata shi, kawai ka aikata, kuma ban yafe maka ba, har da siya mata gwal wai? Ni ta gida ina ta naci ka ƙi siya mini sai ta waje ko? Yau ka sake tabbatar mini da ba ni da sauran daraja a idonka!". Sai ta zauna ta kifa kanta a kujera ta rushe da kuka.

Jikinsa ya fara yin sanyi, ya san dai dole ta sani, amma haka ya kafe ya ƙi karɓar laifinsa, sai dai ya daina kumfar bakin, ya sanyaya murya ya ce"Nana ki ɗago mu yi magana".

Kamar ba ta ji ba, amma ta tsagaita da kukan.

Ya ce"Wallahi ƙarya ne, duk wacce ta faɗa miki wannan kawai ta yi ne don ta haɗa mu, na san ina da son mata, amma abun nawa bai kai na kawo mace har cikin gida ba, kuma yanzu ma Allah Ya taƙaita mini fa na daina".

Ta É—ago ta ce"Wallahi duk da ban gani ba na yarda, don na san za ka aikata, wai don Allah mene ne ba na yi maka? Kullum ina zuwa É—akinka fa, ko ba na gamsar da kai ne? Ai sai ka faÉ—a mini na gyara".

Ya ce"Ni ban ce ba, ban ce ba kya gamsar da ni ba, kin san kowane bawa da kalar ƙaddararsa a rayuwa, ni wannan shi ne ƙaddarata, kuma hakkinki ne ki taya ni da addu'a Allah Ya yaye mini, amma batun Zahra wallahi ni ba ni da wata alaƙa da ita, kuma ban taɓa kawo mace gidan nan ba".
Chapter 8 · 0% Book details