← Book details Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 15

Sashe 13

Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ce"A wajena dai babu, kuma bari na faɗa miki gaskiya, duk wajen wanda za ki je ya faɗa miki zai iya wani abu to kuɗinki zai ci, ina ba ji shawarar ki ajiye komai ki haƙura, idan an yi auren za a iya nakasa ta ta wani fannin, amma aure dai sai an yi shi".

Ta share hawaye ta ce"To na gode".

Ta ciro kuɗi a jakarta ba ta ma san nawa ba ne ta ajiye masa, yana ta yi mata magana ta zo ta ɗauka ba ta juyo na ma, ko sallama ba ta yi wa Saddiƙa ba ta fice daga gidan, tana kuka kamar an yi mata mutuwa.

Sai a lokacin ma hankalinta ya dawo jikinta, har an idar da sallar magriba, ba ta cewa kowa a maƙota ga ajiyar yaranta da za su dawo daga makaranta ba, ƙaramin dai yana goye a bayanta.

LITTAFIN NAN NA KUÆŠI NE AKAN NAIRA 500 KACAL, ZA KU IYA TURA KUÆŠIN KARATUNKU TA NAN
8028966015
Sadiya Abdulrazak opay

Shaidar buya ta nan
08028966015
[30/05 17:50] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/DqC9XDRW7ee7y5JtVxNqGr

*Zoki mallaki kayan kitchen cikin saukii,Adashen kitchen(weekly)🤭👌*

*Duk kayan kitchen dakikeso zaa siya maki da kudin adashenki…Kikwashi kayanki tamkar kyauta🤭💃💃*

*Gold kitchen Adashe dinmu ba wasa aciki! 100% aminci, 100% sauki !*

*WANI ZAMAN*

BY
SADIYA ABDULRAZAK

Marubuciyar
Sandar dukan uwargida
Ranar kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Matar shige
Iya ruwa
Wani auren da sauransu

FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS

Labarin ya ƙunshi
Kishi
Kissa
Makirci
Cin amana

PAGE 10

Ta buÉ—e gidanta ta shiga, tana ganin motar da ya fita da ita a gidan ta san ya dawo gidan, ta shiga da sallama a sanyaye, ta gan shi zaune da yaran, don da ya dawo da su ya fara cin karo a layin suna wasa da yaran unguwa, ga kuma unifom a jikinsu, kuma lokacin bayan la'asar ne, ya haÉ—a kan yaran ya buÉ—e gidan yana tambayarsu ina babarsu? Suka ce sun dawo daga makaranta sun ga ba ta nan, ya shiga ya ga ba ta nan É—in, suka zauna ya ce"Kenan ko abincin ba ku ci ba ko?"

Suka ce sun ci a gidan maman Sadik, ya yi musu wanka ya canza musu kaya, suka fita tare ya siyo abinci ya dawo suka ci, ya yi zaman jiranta, dawowarsu daga masallaci kenan sai ga ta ta shigo, yana kallon yanayinta ya ga babh nutsuwa a tare da ita, ta zo ta wuce ta gabansa tana cewa"Sannu da gida".

Bai amsa ba, murya a dake ya ce"Daga ina kike?"

Ta ce"Gidan Mama Binta".

Mama Binta Æ´ar'uwarsu ce, wacce take uwa a wajensu, ya ce"Da izinin wa?"

Ta yi shiru.

Ya ce"Me kika je yi da za ki tafi babu neman izini? Ki bar yara a titi suna gantali, ana sammu su abinci a maƙota, me kika je yi?"

Ta ce"Kawai ji na yi ina son zuwa, kuma ban san zan daÉ—e ba".

Ya ce"Kar ki sake yi mini haka daga yau, don za mu samu matsala!".

Ba ta ce komai ba ta shige É—akinta, wanka ta yi ta, ta yi sallah ta fito za ta shiga kitchen, ya ce"Ki dafa iya cikinki, don mu mun ci na siyarwa".

Sai ta fasa shiga kitchen ɗin, ta koma ɗaki ta zauna, hawaye suka fara bin kuncinta, idan gaskiya mijin Saddiƙa ya faɗa mata cewar auren nan tabbatacce ne, tabbas tana cikin masifa, ta ya za ta iya raba mijinta da wata? A ranar bacci rabi da rabi ta yi, washegari kuma Usman ya ce mata yau masu jere za su zo, sannan idan za ta yi biki ta yi masa list ɗin abubuwan da take buƙata, ta ce masa ba za ta yi ba, sannan ta tambaye shi za ta fita unguwa duba ƙawarta ba ta da lafiya, ya ce"Kamar ba yanzu na faɗa miki za a zo jere ba? Sai a zo ba kya nan?"

Ta ce"Ka ba su mukullin gidan mana, idan sun zo É—in ina nan me zan yi musu? Ni da ba a kaina za su yi jerensu ba?"

Ya ce"Ko ma dai mene ne ki zauna, kar ki fita ko'ina, Hasana ma ta ce za ta zo yau É—in". Daga haka ya fice daga gidan.

Ta gama shirinta tsaf ta zauna, wajen ƙarfe goma Hasanar ta zo, tana zuwa ta bar mata ajiyar gidan da yaran, ta saka hijjabinta ta fice, gidan Zulaiha ta shiga ta zayyana mata duk abin da yake faruwa. Zulaiha ta ce"To tun da kika ga haka ita ma amaryar ƙila ba a zaune take ba, don haka ina ga kawai ki haƙura, ko kuma a nakasa ta ɗin bayan auren".

Fatima ta ce"Na haƙura a yi mini kishiya? Wallahi ba zan yarda ba".

Zulaiha ta ce"To sai ki cigaba, akwai wata ƙawata da take zuwa wajen wani, amma fa shi boka ne, don da nisa sosai ma wajen nasa, tana ganin kyau aikinsa sosai".

Fatima ta ce"Yanzu ya za a yi? Za ta raka ni?"

Zulaiha ta ce"Bari na tambaye ta".

Ta ɗakko waya ta kira ta ba ta shiga ba, sai ta yi mata magana ta whatsApp, an kusa minti talatin har Fatima tana shirin tafiya, sai ta duba saƙon, Zulaiha ta yi mata bayani, ta ce ai kuwa ba ta ƙasar, sai nan da sati biyu idan ta dawo sai ta raka ta".

Fatima ta ce"Ai kafin nan kuma an yi an gama".

Ta ce ta yi mata kwatance, ta ce musu da nisa sosai, kuma ba lallai ta gane ba, amma akwai ƙawarta da take zuwa, za ta tambaye ta idan za ta je nan kusa sai su je tare, suka yi sa'a kuwa ta ce mata gobe za ta je, amma fa tana ta jadda mata ta shirya, don sassafe ake tafiya, kuma sai dare ake dawowa saboda nisan wajen, sannan ta saka kuɗi a jakarta, don ba a yi masa transfer, Fatima ta ce ta ji ta gani.

A ranar ta ciro dubu ɗari biyu ta saka a jakarta, ta koma gida, sam ba ta ɓoyewa Hasana komai, duk da ƙanwarsa ce uwa ɗaya uba ɗaya, amma haka ta ba ta labarin zaryar wajen malaman da ta yi, da kuma inda za ta je gobe, Hasana jikinta ya yi sanyi ta ce"Amma maman Mu'az kina ganin hakan daidai ne? Kin san fa shirka ce wannan, kuma kin san hukuncin, akan kishiya bai kamata ki kai kanki ga halaka ba, kina fa sane yanzu duk sallar da kike yo ba karɓa ake ba, to me za ki ce da Allah idan kika mutu a kan haka? Duk abin da Allah Ya tsara ba wanda ya isa ya rushe shi fa, ya kamata ki zubar da makamanki, ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara".

Fatima ta ce"Ai Allah mai yafiya ne, kuma komai na É—an lokaci ne, ba wai zan dawwama ina yi ba, a gaba zan tuba".

Hasana ta ce"Ke ce da gaban? Wa ya san gobe? Dukanmu gawa ne a tafe, yanzu idan kika kwanta kika mutu a yau fa?"

Fatima ta ɓata rai ta ce"Kin ga ya isa, a bar maganar haka".

Hasana ta ce"Dama ai gaskiya tana da É—aci".

Fatima ta tashi ta bar mata falon.

Ana gobe É—aurin aure ya kama za su je wajen bokan nan, duk da ta ce ba za ta yi biki ba, amma a gidan nata dai za a yi taron, haka Æ´an'uwa suka tsara, don haka tun yau za su zo a fara shirin hidimar goben, sannan kuma yau za a yi dinner.

Ƙarfe shida Fatima ta shirya tafiya, don a yadda suka yi da wacce za su tafin ma ce mata ta yi ana idar da sallar asuba ta fito, ba ta fito ba sai shidan, ko ƙaramin ɗanta ba za ta tafi da shi ba, ta yi wa Hasana sallama tare da roƙonta don Allah kar ta faɗawa kowa inda ta tafi, kawai ta ce ita ma tashi ta yi ba ta ganta ba, idan ta dawo ita za ta ji da kowa har Usman ɗin, Hasana ta ce a dawo lafiya.

A motar matar suka tafi, suka yi tafiya mai nisa, bayab azhar suka zo wata ƴar ƙaramar kasuwa, a nan suka tsaya suka ci abinci, don ita Fatima ko karyawa ba ta yi ba, bayan sun gama cin abinci suka yi sallah a nan, sannan ta bawa wani ajiyar motarta, da alama dai ta san shi sosai, suka hau babura suka fara tafiya, tun suna ganin garuruwa har suka shiga daji, ana ta zura tafiya, har abun ya bawa Fatima tsoro, tafiyar awa ɗaya suka yi a babur, ya ajiye su, matar ta roƙi masu baburan su jira su, za su ba su dubu ashirin, suka yarda, su Fatima aka fara tafiyar ƙafa, aka nausa cikin daji ana ta yi.

Fatima ta gode Allah da ba ta taho da ɗanta ba, ganin tafiya ta ƙi ƙarewa, ta gaji liss, ta kalli matar ta ce"Ni Hajiya me yasa muka sauka ba mu ƙarasa a babur ɗin ba?"

Ta ce"Ai wancen bishiyar da kika ga mun tsaya mun sauka madakata ce, babur ko mota a nan zai tsaya muddin wajen bokan nan mutum zai je, saboda yanzu mun riga mun shiga masarautarsa, yanzu haka a ciki muke tafiya, yana kallonmu yana jinmu, kuma kafin mu ƙarasa zai gama ganin buƙatunmu, ya gama tsayar mana da mafita, da mun je babu wani bayani sai dai ya zartar da hukunci kawai mu sallame shi mu juya".

Fatima ta jinjina kai, suka cigaba da tafiya suna sauri kamar za su tashi sama.

Suna ƙarasawa kallo ɗaya ta yi masa ta ji gabanta ya fara faɗuwa, don wannan hamshaƙin boka ne irin wanda take gani a TV, "Ke ɓatacciya! Ki cire takalminki!" Ya dakawa Fatima tsawar da duka dajin sai da ya amsa, saura kaɗan Fatima ta faɗi saboda yadda ta rikice, sai a lokacin ta lura ita Hajiyar ashe ta cire nata, ta cire da sauri ta tsugunna jikinta yana karkarwa, Hajiyar ta ce"Tuba take ranka ya daɗe mai girma Duhu, laifina ne ban faɗa mata ba, tuba muke".

Fatima da rawar baki ta ce"Tuba nake".
Chapter 13 · 0% Book details