Sashe 3
Wani Zaman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa yarinyar da sauri ta matsa bata tare da ƙunduma ashar, hakan ya jawo hankalin duka mutanen wajen, suka fara kallonsu, ta ce"Ni za ka taɓa? Saboda ka cika ɗan iska a gaban mutane za ka saka hannu a jikina?"
Usman ya ruɗe ya fara rawar murya ya ce"By...by mistake, wallahi ban sani ba, na zama zanin jikin yaron na danƙo".
A fusace ta ce"Wallahi ka taɓa Allah Ya isa, ɗan iska, asararre babban banza, ɗan wahala, kwaro, daƙiƙi!".
Kowa a wajen ya yi tsit, shi kuma ya juya ya fice ɗauke da ɗansa, Fatima ta ji ina ma ƙasa ta tsage ta shige, ko ta huta da wannan kunyar da ta mamaye ta, haka ta miƙe tsaye da ƙunshin ba ta cire ba, ta zuge jakarta ta biya kuɗin, ta fito daga wajen takalmi a hannu, tana tafiya kamar za ta faɗi saboda yadda santsin ledar ƙunshin yake kwasarta, ta shiga motar ta rufo, ta tarar da shi ya sunkuyar da kai, ta rasa me ma za ta ce masa, ya ce"Ki yi haƙuri don Allah Nana, mutane ne ba su da fahimta, ban da ta yi niyyar yi min sharri daga karɓar yaro?"
A fusace ta ce"Dalla rufe mini baki...!"
"Ni kike yi wa tsawa? Fatima?"
Ta ce"Na yi ɗin, ai ka cancanci fiye da hakan ma, ashe kai abun naka ya wuce zatona? Usman a titi a idon mutane, a gabana ka kai hannu ka taɓa mace?Ashe har ka shahara haka? Waye kai? Da wa nake zaune ne?" Ta sake fashewa da kuka.
Ta ce"To wallahi ban yafe maka ba, kuma na gama zama da kai, daga nan ka kai ni gidanmu!".
Ta yi maganar cikin fitar hayyaci, domin ta san ba ta da wani gidan da ya fi na mijinta, tun da mahaifiyarta ba ta raye, kuma ta fuskanci ƙalubalen rayuwa tsakanin rasuwarta da kafin aurenta da Usman ɗin, kusan ma a ce mahaifiyar Usman ɗin ita ce gatanta, duk da tana da sauran dangin uwa da na uba, amma karamcin matar a gare ta ya sa take ganin ta fi wasu danginta sau dubu.
"Kin ga ki yi haƙuri" Ya faɗa a daƙile, don ransa ya ɓaci da wannan tsawar da ta yi masa.
Ta cigaba da yi masa kalaman cin mutunci, shi kuma ya ja motar suka tafi, ya zama kamar kurma ya kasa ce mata komai, saboda ya san ba shi da gaskiya, a ransa kuwa rayawa yake yi anya ba zai dawo su sasanta da yarinyar nan ba?
Yana ajiye ta ya bar gidan, don ya gaji da wannan tijarar tata, Fatima ta ci kuka ta gode Allah, tun daga ranar kuma ta gama sanin da wa take zaman aure, tana son Usman, ba ta ma hasashen rabuwa da shi saboda wannan halin nasa, don haka ta shiga tunanin wace hanya za ta bi ta canza masa tunani, ya dawo gareta ya kafe a kanta ita kaÉ—ai? Ya daina ganin kowace mace sai ita? Tunaninta bai tsaya a ko'ina ba sai a kan maganin mata, gani take kawai ita ta gaza ne, ba ta da ni'imar da za ta gamsar da shi, shiyasa yake neman na waje, don haka ta yanke dole a yau ba sai gobe ba za ta samawa kanta mafita.
Da yamma ta saka hijjabi ta shiga gidan maƙociyarta wacce ta kasance ƙawarta, Salima irin matan nan ne waɗanda suka ɗauki maganin mata a matsayin makaminsu na zaman aure, suka gaisa ta ce mata so take ta samo mata maganin da zai saka mijinta ya kau da ido daga ganin kowace mace sai ita kaɗai, Salima ta ce mata ai kuwa akwai wani magani da ta gwada ta ga aikinsa sosai, don haka za ta yi mata hanya ta siya, nan take ta kira mai maganin a waya, ta ce mata gobe za ta kawo mata har gida, Fatima ta yi wa Salima sallama ta tafi gida tana jin sanyi a ranta, saboda rashin sanin matsalar da za ta shiga silar wannan maganin, inda ta sani da ba ta kai kanta ba.
08028966015
[28/05 13:02] Mai Zafafa: https://chat.whatsapp.com/KHaNhtgfrBoAKxQ6GGKFyq
*WANI ZAMAN*
BY
SADIYA ABDULRAZAK
Marubuciyar
Sandar dukan uwargida
Ranar kuka
Miji goma
Zuciyar mace
Matar shige
Iya ruwa
Wani auren da sauransu
FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS
Labarin ya ƙunshi
Kishi
Kissa
Makirci
Cin amana
PAGE 3
Fatima ta koma gida tana jin rabin damuwarta ya yaye, ko da Usman ya dawo ba ta tada masa zancen abin da ya yi ba, shi ma sai ya yi shiru, sai dai yana ta kaffa-kaffa da ita, ko da ya neme ta a daren ba ta hana shi ba, saboda ta san fushi ba zai zama maslaha ba.
Washegari kafin ya fita ta tambaye shi kuɗi, babu musu ya ba ta, wajen ƙarfe goma mai maganin ta zo ta kawo mata, wani abu ne ta ba ta ce saka shi a za ta yi a gabanta sai bayan kwana biyu za ta ciro shi, sannan ta ba ta wani mai kama da zuma ta ce a sati sau ɗaya za ta dinga shan cokali ɗaya, Fatima ta biya ta kuɗinta, nan take ta fara amfani da maganin, a ranar ta yi wankan dare ta ci kwalliya ta tafi ɗakinsa, ai kuwa ta ga kyaun maganin nan sosai, har tunani ta fara yi anya ba sa haɗawa da Malaimai kuwa? Washegari baban Mu'az wani kallo na musamman yake yi mata, cikin sati biyu ta bi ƙa'idar maganin nan, Usman ya ninka kyautatawarsa a gare ta, ya rage yin dare a waje, ana yin sallar isha'i zai dawo gida, ya rage bawa wayarsa muhimmanci, babu wani kiraye-kirayen ƴan'mata, sai nan-nan yake yi da ita, tare da kyautar bazata, hakan ya sa ta ƙara ƙaimi wajen shan maganin, a maimakon duk satin da aka ce ta sha cokali ɗaya, sai take shan cokali ɗaya kullum, saboda aikinsa ya linka fiye da yadda yake yi, maganin da ya kamata ya ƙare a wata uku sai ya ƙare a sati uku, ta shirya ta tafi gidan mai magani, bayan ta yaba mata kyaunsa ta faɗa mata ya ƙare za ta sayi wani.
Mai maganin ta dafe ƙirji ta ce"Ya ƙare!? Ta ta zai ƙare tun yanzu bayan na wata uku na ba ki? Anya kin bi ƙa'ida kuwa?"
Fatima ta ce"Ni fa daga baya kullum cokali É—aya nake sha".
Mai magani ta dinga salati ta ce"To Allah Ya tsare ki kuwa, amma wallahi ko miliyan za ki ba ni ba zan sake siyar miki da maganin nan ba, sai dai ku sayi wani kalar".
Fatima ta ce"A haba don Allah ki taimaka mini, ban taɓa amfani da magani mai kyaunsa ba wallahi".
Duk yadda ta kaɗa mai maganin nan ta ƙi siyar mata, ta haƙura ta koma gida tana mamaki, don ita ba ta ga wata illarsa ba.
Duk da maganin ya ƙare amma ba ta daina ganin aikinsa ba, a wannan lokacin sun samu zaman lafiya sosai da mijinta, ya rage abubuwan da yake yi. Wata rana da safe tana zaune tana chart hankali kwance, kawai ta fara ciwon mara, ciwo mai tsanani sak na naƙuda, kamar wacce za ta yi ɓari.
Tun tana daurewa har ta kasa, ta kwanta tana ta juyi, ga shi ranar Usman ba ya garin, ta aika aka siyo mata maganin ciwon mara, ta sha a banza, ciwo sai gaba yake yi, ta gama saddaƙarwa ciki ta samu zai zube, don haka ba ta kawo tunanin wannan maganin ne ya yi mata illa ba, haka ta wuni cikin mawuyacin hali, dab da magriba ta kira shi a waya ta faɗa masa, ya ce ta tafi asibiti shi ma yana hanya.
Ta shiga maƙota ta ba da ajiyar ɗanta, don kar ta jefar da shi a hanya saboda azabar ciwo, ta je wani asibitin kuɗi da yake kusa da su, ta yi wa likita bayanin abin da yake damunta, ya yi mata scanning, ya tsaya da mamaki a fuskarsa ya ce mata"Amma dai kina yawan amfani da magungunan mata ko?"
Gabanta ya faÉ—i, ta san faÉ—an likitoci don haka ta girgiza kai ta ce"A'a, ban yi amfani da komai ba".
Ya ce"To amma dai da mamaki, wani datti ne ya taru a mararki, kuma yawanci silar shaye-shayen magunguna barkatai ne yake haifarwa, dole sai an yi miki tiyata an cire shi, idan ba haka ba rayuwarki tana cikin garari".
Fatima ta fara kuka, duk ta rikice da jin zancen tiyata, likitan ya ce"Yanzu ki je gida ki shirya, sai ki taho tare da mijinki ko iyayenki, a yi miki aiki a cire wannan dattin, idan ba haka ba komai zai iya faruwa".
Fatima ta ce"To na gode".
Ta fita daga asibitin tana share hawaye, ga azabar ciwo ga ta tashin hankali, sai ta kasa komawa gidan, ta zarce wani asibitin, don rana ganin kamar wannan likitan ƙarya ya faɗa mata.
Shi ma nan ɗin kamar yadda asibitin farko suka yi mata bayani, haka ya faɗa mata datti ne a mararta, sai dai shi ya ce zai iya rubuta mata magunguna ta sha, ƙila dattin ya fito, idan bai fita ba sai a yi aikin. Ya rubuta mata magungunan ta fita, ba ta zarce ko'ina ba sai babban kemis, ta sayi magungunan ta dawo gida, ko zama ba ta yi ba ta sha maganin, sannan ta karɓo ɗanta.
Ana kiran sallar isha'i ta ji ciwon ya ƙaru, ya taso gadan-gadan, nan fa ta fara nishi mai ƙarfi tamkar dai mai naƙuda, kamar ɗa zai fito ta gabanta, hakan ya sa ta tafi banɗaki ta tsukunna, sai kuwa wasu irin abubuwa suka fara fitowa, baƙi da shi kamar chocolate, idan ta yi nishi mai ƙarfi sai ya fito curi guda, idan ciwon ya lafa ta yi tsarki ta koma ɗaki, idan ya taso ta koma banɗakin, cikin ƙanƙanin lokaci ta jigata.
Wajen ƙarfe tara Usman ya dawo, ya tarar da ita a galabaice, ya ce su koma asibitin, ta ce ai ta ji sauƙi ma, saboda ba ta son ya gane maganin mata ne ya ja mata matsala, ya siyo mata abinci ta ci, a ranar a ɗakinta ta kwana, saboda kar ya ga tana yawan shiga banɗaki, kwana ta yi tana zubar da wannan abun, sannan ta samu sauƙin ciwon marar.