← Book details Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 40

Sashe 5

Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

*Cigaban labari*

Shiryawa tayi cikin kayan makarantar nata doguwar Riga wacce tadan haura kugun ta da dogon wandon har kasa sky blue sai hijab dinta iya guiwa fari tas takalmin gida tasa flat a cewarta tunda karatun WAEC sukeyi ba'a takura musu daka ganta kaga student fuskarta babu kwalliya I'lla pawder da man baki Mara kala dukda haka tayi kyau ba laifi, wurin 7:30 tafito dauke da Karamar jaka Wanda katon littafi guda dayane a ciki shima dandai daukan nashi yazama dole ne, iyayan ta tasamu zaune a matsaikacin parlor dinsu Wanda babu komai a ciki sai ledar tsakar daki a gefe daya kuma katon dirowa ne shake da littattafai kala kala na Addini ko'ina tsaf gwanin ban Sha'awa suna zaune akan tabarma da Alama Karin safe sukeyi, dukawa tayi ta gaishe da iyayan nata cikin faraa suka Amsa mata, 'uwata ya karatu? Yakuma haddar taki? Duk inda kike da matsala wurin rashin fahimta ki gayamun sai inkara doraki akai, inji Malam liman, Toh Abba insha Allah bama Wata Matsala, "toh toh yayi haka akeso aita dagewa shi ilimi da kike gani kogi ne sai gaba zakiga amfanin shi maza zauna ki karya ki hanzarta kada ki makara ya fadi yayinda da kanshi ya tsiyaya mata koko cikin kofin dake hannun shi da Alama ko gama sha baiyi ba tura mata yayi gabanta harda ledan kosan daya siyo musu na Kari, mamanta ce ta turo mata wani kwanon Samira ta ajiye gabanta, dumamen tuwon dawa ne miyar kubewa danya sai tururi yakeyi, 'maza ki hada da wannan saboda kiji nauyi nauyi tunda keda dawowa sai shida na yamma, 'a'a mama kosan maya isheni tafadi tana shan koko cikin natsuwa, dari biyu babanta ya mika mata dari Na abun hawa dari kuma kozata siya wani Abu darana saboda yinwa gashi zata tsaya lesson din WAEC, 'baba kabarshi Wanda kabani jiya da daddare ma yananan tafadi , a'a uwata hada duka aikin chanchanci komai gurina babu abunda bazan iya miki ba dakyar ta Amsa Naira dari wacce tace kudin mota zatayi dashi, 'mikewa tayi cikin natsuwa tabar gidan a'daidaita ta nema drop ta dauka basu zame ko'ina ba sai gidansu na isa kaita Wanda yake a U/rimi GRA rabonta dawata shegiyar Boko harta manta a cewarta babu abunda kudi bazai siyan mata ba kuma tana dasu, hakan yasa harta biya ansamu Wanda zaimata komai da komai da sunanta batareda ciwon kai ba. tana isa mai'gadin su dayake zaune kofar gidan sanin cewa daidai lokacin take zuwa, gaishe ta yahau yi Kota kanshi batabi ba 'kada abar kowa ya shigo batareda ambaka izinin yin hakan Ba, tafadi yayinda tashiga cikin gidan, batajin zata iya tarban baki da safe saita huta domin bccine sosai a idon nata.

*Mrs Sadik Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?*
🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀

*Written by Anty Mamie*

*Gskia sai jiya na tabbatar da masoyan littafin nan Nada yawa fiyeda tsammani na wayata har daukewa takeyi saboda ruwan comments da Addu'a a gareni nayi matukar farinciki tareda mamakin yanda kuka karbe shida hannu biyu biyu, bazan daina fadi ba comments dinku nasani matukar nishadi tareda karfin typing, Godiya mai tarin yawa Ga makaranta😍😍*
Sorry nayi mistake a last page inda zansa Sunan Aisha nasa Zainab, Afuwan typing error ne.

*Dedicated to sister Husnah*

9

*Shin wacece Aisha? Wanene kuma AK?*

Ya'u shine Mahaifin Aisha tareda mahaifiyarta Ramata Asalin yan cirani ne daga Damagaram dake jahar Nijar, inda suka shigo Nigeria lokacin da yaransu biyu, namiji da yar'karamar yarinya mace wacce mahaifiyarta Ramata ke rike da ita a hannu, a lokacin bazata wuce shekara biyu a duniya ba, namijin suna kiransa da garbati, yayinda macen suke cemata shatu, Sanye suke da bakaken kayan buzaye yayinda sukasha nadi a kansu daka gansu kaga bakin haure, daga Ya'u har Ramata irin dogayen buzayen nanne sosai wankan tarwada kyawawa Tubarkallah, yayinda cikin ikon Allah suka sauka garin Kaduna a unguwan shanu kai tsaye gidan mai unguwa sukayi inda suka gayamai kudirin suna San fara sana'a yanda zasu tallafa rayuwar su, cikin ikon Allah mai unguwn yabasu daki daya Wanda ke zauran cikin gidajan shina unguwan aiko ba karamin murna suka dinga yiba tareda godiya da Addu'a a gareshi, dakin karami ne baida girma sai window kwaya daya rak, inda Allah ya taimake su zauran nada dan fadi hakan yasa Ramata keyin sanwa a lungun zauran, yayinda suka hada bayi da mutanan dake cikin gidan dukda gidan bawani Babba bane dakuna Uku ne a cikin gidan sai bayi guda daya da kitchen dinda kowa ke Amfani dashi, batareda bata lokaci ba Ya'u ya kafa Karamar teburin shayi a gaba da gidan nasu nan danan yafara Tara customer's bakaramin ciniki yakeyi ba darana kuma saiya kasa rake duk anan wurin yayinda Garbati ke tayashi Zama a lokacin yanada shekara goma a duniya akwai tazarar shekara takwas tsakanin shida Aisha, Ramata kuwa baa barta a baya ba, wankau tafara a cikin gida, itama babu laifi tana samu hakan yasa tace barita gwada shiga cikin gidajan masu kudin unguwan kila zata Dace su dauketa wani aikin, cikin ikon Allah nan saman layin su sosai inda gidaje masu kyau suke nanta tunkara duk gidan data shiga bata dacewa harta fara gajiya ga zafin rana Ga Aisha dake bayanta sai kuka take tsalawa, ganin sauran wani gida daya Wanda yafi duk Wanda take zuwa tsaruwa tana shirin komawa gida hakanan tace bari ta gwada sa'ar ta, tun daga kofar gidan mai gadin gidan ya dakatar da ita, 'hajiya lafiya? Yana Kare mata kallo sama da kasa, kafun takaiga bashi Amsa sukaji karan horn din mota Alamar masu gidan ne suka dawo, matsawa tayi gefe tareda rusunawa, koda suka shigo hajiyar gidan ce dayara guda biyu tareda ita, babban shekaransa goma sha biyar mai suna Abdulkareem yayinda dayan bazai wuce sha'daya ba, shikuma Abdulhakeem kallo daya zakai musu kaga kallar kamarsu da mamar tasu wacce take fara kar, 'a'a lafiya? Wacece wanchan? Hajiyar ta tambaya tareda nuna Ramata daketa zuba zufa cikin tsakiyar rana, Kafun mai gadin yabata Amsa ta karaso tareda Kara dukawa gaban hajiyar tana gaishe ta, 'amsawa tayi cikin sakin fuska, 'hajiya Dan girman Allah ki taimakeni kibani aikin yi, ta furta cikin rawar murya, achan kasan layinku gidanmu yake Mijina ne mai saida shayi da rake a kasan layi, 'shigo mu shiga ciki hajiyar ta furta ganin yanda Aisha keta tsala kuka kamar zata suma, samarin kuwa tuni sukayi cikin gida hannun su rikeda Leda da Alamar siyya sukayi da mamar tasu.

A babban parlon dake kasan gidan sukai masauki kassncewar gidan gidan sama ne, parlon ya tsaru sosai, a gefen kujera Ramata ta zauna yayinda hajiyar tayi tayi ta zauna kan kujera taki, Wata dattijuwa ceta shigo parlon rikeda farantin ruwan sanyi da lemu tanama hajiya sannu da zuwa, amsawa tayi tareda mika ma Ramata ruwan aikuwa ta Amsa ta sha sosai tareda kwanto Aisha tabata tasha nan tayi shiru tana Ajiyar zuciya da Alama zafi neya dameta dama.

Basu bar gidan ba saida hajiya taimata Albishir din bata aikin wanke wanke da gyaran kitchen da tsakar gida, tunda sunada mai musu girki sannan ba abincin kowa suke ciba, cikin Ikon Allah tafara zuwa tareda samun Alheri mai tarin yawa inda kusan anan take saman musu abincin da sukeci a gida, kassncewar idan abinci ya kwana basa ci, nan hajiya taba Ramata izinin dauka tunda dama Almajirai ake dunduma ma, dukda ranar juma'a ana girki na musamman da yamma Almajirai na layi amsar sadakan abinci mai rai da lafiya, nanfa duniya tadawo masu ya'u da Ramata harma da yaransu sabuwa sunyi fes sunyi kyau sosai sun murmure Aisha kuwa sai wayo takeyi tayi bulbul da ita gwanin ban Sha'awa takawa takeyi ko'ina.

*Mr's Sadik Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*

11
Chapter 5 · 0% Book details