← Book details Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 40

Sashe 15

Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Mr's Saddiq Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Alhmdlh nadawo nagode da Addu'ar ku masoya, Gskia banyi niyyan posting yauba but Alkawarin danayi shiyasa kuka jini masu kirana suji lfy ina godiya sosai😍, Zaku cigaba dajina insha Allah daga yanzu*

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*

19

Ak kwance yake akan gadon dakin hotel dinda yakama a yanzu gadon baida banbanci Dana asibi saboda tun daga ranar daya sauka a dakin ciwo yaita yi kamar bazai kai labari ba family doctor dinsu yakira nan aka Dora mai ruwa babu yanda likitan baiyi akan zaifi samun kulawa a Asibiti Sam yaki yarda yayinda yaima doctor din kashedi mai tsauri akan bayasan iyayanshi Susan inda yake harsai sun neme shi, kimanin kwana Tara kenan yana kwance a dakin dukya fige ya rame sai uban farin daya Kara likitan ne atare dashi yayinda yagama zarkada masa Allurar karshe daya gama Amsa a ranan kashedi yaimasa akan yarage tunani domin yana gafda kamuwa da ciwon zuciya banda hawan jinin dayake dashi a halin yanzu, godiya yaima doctor din nan yafara hada yanasa yanasa a cewarsa ko mutuwa zaiyi gara ya mutu a gaban iyayan shi ba'a dakin hotel ba dukda bawai ya yafe musu cutarshi da sukayi bane😡aa zaidai koma ne kila a yanzu sunyi nadama sun kuma San zafin rashin Sa a kusa dasu, misalin karfe Tara na Dare ya shigo falon nasu yayinda yake tafiya kamar Wanda kwai ya fashe ma aciki hannun shi rikeda jakar gudun hijirar Sa, Daddy da Mamie na zaune a parlor suna kallo cikin nishadi kallo daya zakai musu ka tabbata basuda damuwa, sallamar sane yadawo dasu nan Mamie ta Mike da sauri ta tarbe shi tana salatin ganin yanda ya rame shiko gogan Kara murtuke fuska yayi adole fa anmai laifi, wani irin ciwo kayi haka ka ganka kuwa? daddy kuwa kallo daya yaimasa ya kauda idonshi ya cigaba da kallon shi, 'Ciwo kayi ne AK ka ganka kuwa? Kanaso ka halaka kanka akan abunda bai taka Kara ya karye bako? Tafadi rikeda hannun shi har bakin kujerun parlorn kememe yaki Zama a kujerar, 'yanaga kadawo dawuri? Koko sauran kayan ka kazo kwasa? Aida bakaxo ba saika yi waya idan yaso maba bireba yakawo maka sauran kayan inji Alhaji muktar yayinda ko kallon AK baiyi ba, shiko wani takaici yakara turnuke shi ganin iyayan shi sun daina sanshi da tausayin shi duk akan wata shegiyar Aisha, 'dukda haka bata baci ba zan yarda kayi kwanan karshe a cikin gidana, naba mamarka makullin daya daga cikin gidajena kaje chan ka zauna insha Allah nakusan kawo maka iyalin ka, 'nifa banda kudin dazan iya zuba kaya a cikin gidan, inji AK
Cikeda mamaki Mamie ta kalle shi wai AK ne baida kudi, 'Karka damu ai ninaga zan iya nasa muku duk wani abunda zaku bukata a matsayina na Uban Amarya uban Ango kuda akaima Auran gata? Lefenka ma ake hadawa bana bukatar ko kwandalar ka, ahtoh daddy yafadi yayinda AK ya wuce daki kai tsaye cikin takaici.

AK ya tare a dankareran gidan su Wanda ya hadu ya hadu ya hadu harya gaji da haduwa, gidan ba gidan sama bane four bedroom ne manya manya sai katotan parlor Guda daya a tsakiyar dakunan yayinda kowane daki yanada bayi harda parlor kowani daki saida a zuba furniture's hadaddu parlor kuwa Royal kujeru ne har set biyu sky blue da Orange, sai barayin dinnin dinda aka kewaye shida transparent glass komai na wurin white ne gskia dady ba karamin kudi ya zuba a gidan ba, hmmmm sai Wanda yagani bari inyi shiru kada ace zan zuba karya🤭.

Mamie ce ta aika gidansu Aisha aka amso measurements din kayan ta da size din takalmi da undis nan aka hada mata lefen ta mai rai da lafiya akwati set daya yayinda aka dinka kayan ciki sosai bayan an kwana biyu Mamie da kanta tazo da direba inda ta dauki Aishar basu zame ko'ina ba sai babban boutique English wears taita jidan ma Aishar a cewarta so takeyi ta rikita AK tanaso taga yazo ya durkusa yana musu godiya akan aura mishi Aishar da akayi kunya ta cika Aishar inda take ji kamar ta nutse a kasa, kaya ne naban mamaki masu daukar hankali ko kunya Mamie bataji ba nanta dinga gayama Aishar kissar mallake miji cikin dabara saikace ba sirikarka ba, itako Aishar jinta takeyi a sama duniyar ta fes, tun daga ranar Kullum da safe zatazo ta dauke ta takaita wurin gyaran jiki na amare, hmmmm Allah sarki Naira, cikin kwanaki Uku kachal Aisha tayi masifar kyau naban mamaki tayi fresh color dinta yakara fitowa gashin nan ba'a magana yayinda akaita dura mata maganin mata a zuciyar Mamie kuwa sotake AK yayi har kukan Agwagwa Ranan 1st 9yt😉oooh su Mamie iyayan Zamani, ranar karshe Kunshi akakai Aisha akai mata baki daja, hmmmmmm Kara gyara mata kanta akayi inda Mamie ta hadata da turaruka masu matukar kyau da motsa Sha'awa, sai wurin la'asar suka dawo nan take shaida ma Ramata akan daddy zaizo karfe Tara na Dare shi da kanshi zaikai Amarya dakin ta ba'a bukatar yan rakiya idan yaso bayan an kwana biyu sai aje aga daki, Hmmmm zo kuga bakin Aisha har saida yakusa yagewa saboda murnar zata kwana da masoyin ta ayau, tunda yamma Ramata ta hada mata ruwan wanka na turare kala kala, nanfa Aisha abun naima yasamu taita durzan fatan jikin ta a cewarta ayau zata fara hada jiki da Rabin Ranta muradin ta AK, shiru kakeji kamar an aiki bawa garinsu yayinda Ramata take shirin binta bayin sugani ko wani wabu yafaru ne ko nakuda takeyi ai ya isa ace ta haihu Yanzu inji Ramata, haba har ana shirin shin sallar Isha'e, Aisha kuwa badan taso ba ta fito kassncewar ruwan yakare kuma fatar jikinta yafara zafi durza yasha bana kadan ba, 'harara Ramata tabita dashi, aina zaci bcci kikayi a bayin, Kota kansu batabi ba tafara kwalliya mai daukar hankali tana rera wakar soyya cikin nishadi.

"So bai karewaaaa
"So bai chanzawa aaa
"Wanda nake kauna "da'eman fa bazai "chanza baa gani gaka, harda rufe fuska a dole tanaba kanta kunya, bilki kuwa daga uhmm sai uhm uhm, suna ganin ikon Allah, turare taita sawa kala kala saida bilki ta kwace kwalbar a hannun ta, nan tasaka wani dankareran red lase dinda yagaji da haduwa cikin kayan lefenta Mamie ta bata dazu tace shi zatasa idan za'a kaita, lefenta tuni ankai mata gidanta ko ganin shi basuyi ba a cewar Mamie Sa gani achan gidan, wow bilki ke cewa ita kanta yayar Tata tamata ba kadan ba ko makiyin ki wlh Anty Aisha idan yaganki saiyace shegiya amma fa tayi kyau, mayafin kayan tasa Wanda keda digo digon baki tareda flat shoes tasha dankunne ta sarka da zobe harda agogo da warwaro sak Amaryar masu kudi sunan da bilki tasa mata kenan a lokacin, 'Ramata da garbati sai santin ta sukeyi saikace ba ita ba lallai kudi sunyi, nan sukaita mata nasiha da fada mai shiga zuciyar mai sauraro inda Ramata keta kukan rabuwa da murnar Aurarda Aisha, itako Aishar batama San sunayi ba dukta kosa daddy yazo inda Rabin fadan dasuke mata ke shiga kunnan ta ya fita ta dayan kunnan jefi jefi tana Satan kallon agogo wurin karfe Tara saura, maiya tsaida Daddy? Itafa takosa akaita taga mijinta, 'toh Kidai rike maraicin ki kinsan wacece ke basai na tuna miki ba mu talakawa ne lis bamuda gata saina Allah, ke ai ko ba,ai miki fada ba ya isa kima kanki ganin irin Rayuwar da mukeyi har a unguwan nan, hakuri Aisha, Hakuri bazan daina maimaita miki ba, kiyi hakuri, girgiza kai kawai takeyi cikin mayafi sai a lokacin ne ta matso jaririn kwallar rabuwa da yan'uwanta bilki kuwa kuka takeyi kamar zata suma saika rantse itace Amaryar dukta kankame Aisha, aikowa akayi daddy yazo daukar ta, inda dakyar garbati ya sashi shigowa suka gaisa sama sama da Ramata daketa zuba godiya da kuka, rike hannun ta bilki tayi inda ta bude mata bayan motan ta zauna yayinda daddy ke zaune gaban mota shida driver dinshi, Inda akace bilki zata kawo mata kayan da akai mata anan zuwa jibi insha Allah,motar na tashi ta tsinci kanta da muguwar faduwar gaba tareda fargaban yanda daren nasu nayau zai kasance itafa tsoro takeji Allah yasa AK ya bita a hankali saboda tataba ji Wata yar'islamiyyar su tana bada labarin 1st 9yt dinta idan tace har saida ta suma, hmmmm nan takara rikicewa tana Addu'ar Allah yasa mijinta yabita a hankali.
Chapter 15 · 0% Book details