← Book details Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 40

Sashe 10

Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Alhaji muktar neke shirin zuwa Office dukda baicika zuwa ranan juma'a ba ko zaije baya zuwa dawuri amma tun safiyar ranar ya tashi ya shirya dawuri Mamie ceta shigo dakin cikeda mamaki, Daddyn su Abdul badai fita zakayi ba? 'Kaji mai idonki yagani idan ba fita zanyi ba mainene amfanin babbar rigar Dana Sa? Bafa nasan tambayar rainin wayau, 'Allah yabaka hakuri gani nayi yau juma'a ai sai bayan an sauko masallaci kake Fita gashi yaune daurin Auren diyar Ramata na dauka zakaje, 'auu kinga ko shaf na manta wlh Wasu baki mukeda su zasu zo daga Lagos zamuyi meeting dasu tuntuni Nike jiran kiransu saboda yau zasu toso da sassafe, karan kiran wayar shine ya tsaida shi yayinda ya dauki wayar dake kan kago cikin hanzari ya juya harshan turanci, yayi minti Uku a wayar ya katse cikin takaici sai masifa yake, 'ina amfanin rashin cika Alkawari kun tsaida mutane Dan iskanci kuce kun daga sai ranan Monday? Kaji fa, akin banza, 'ya akayi kuma mai gidana wake tabo munkai yaune inji Mamie datake shirin samai hula akan shi, 'maida ai nama Fasa fitan anyi canceling meeting din sai Monday insha Allah, yafadi tareda cire babban rigar shi, Anjima naje wurin daurin Auran ko lada na samu.

Misalin karfe daya babban masallacin unguwan ya cika makil babu masaka tsinke yayinda aka idar da sallar juma'a ana shirin daurin Aura saidai mai? Babu ango babu Alamar shi babu waliyan Ango nanfa akaita kananan surutu, a gefe daya ya'u ke zaune jikinshi manne Dana mai unguwa kassncewar tunda bikin ya matso yaita tura garbati wurin mai anguwa naiman Alfarman halartar daurin Auran diyarshi tareda Alkawarin ana daurawa baza'a Kara ganin shiba, dakyar da sudin goshi mai unguwa ya lallashi matasan unguwan akan subashi damar shigowa yau daya rak koba komai Auran diyarsa ake, yasha fararan kaya harda babban Riga sai washe baki yakeyi cikeda farinciki saikace shine angon, tunda akaga babu wani dangin ango bare angon aiko ya'u yaita hada zufa harda cire hular kanshi yana fifita dukya jike babban Riga, 'Musa ne ya shigo masallacin cikin hadin gambiza sanye da wandon farin shadda tasha guga sai Wata bakar kodaddiyar T-shirt baza ido yakeyi sai zage zage yakeyi aikuwa charaf idon shiya sauka kan ya'u daya kara makure jikin mai'anguwa, 'munafukin Allah ta'ala wato ni zaka Aurama diyarka daka gama kwakule ta saida ka tande ta tsaf zaka kawo mun tallar Auran ta? Macucu mazinaci tir duk iskancin ka ace sai kayi da diyar cikinka? Billahillazi ko balarabiya ce sai andawo da kudina tundaga kan taro zuwa sisi na bazaiyi ciwon kaiba yafadi yayinda yake nade kafar wandon shi kafun a Ankara harya shako wuyan babbar rigar ya'u ya hadashi da bango yakai masa naushi a baki, 'banda rainin hankali karuwar zaka aura mun duk mazan unguwan nan sungama saninta akace, mutane ke bashi hakuri yaki sakin ya'u a cewarsa sai an maido mai da komai saikace Wanda ya kashe kudin Arziki babu yanda baayi dashi ba kememe yaki sakin wuyan ya'u daya Kara makurewa, ya'u kuwa kunyar duniya tagama rufe shi ji yakeyi kamar kasa ta bude ya shiga kokuma Allah ya dauki Ranshi a lokacin wannan abun kunyar damai yayi kama? Dawani ido zai Kara kallan iyalin Sa a karo na biyu yakara tarwatse musu Rayuwa a dalilin gyaran dayake tunanin yayi, 'Alhaji muktar neya Mike yayinda ya tunkari wurin rike hannun Musa dake wuyan ya'u yayi, bawan Allah kaima Allah ka sake shi, wannan ai tozarci ne, fisabilillah saboda masifa ya fadar Ma yarinya ko'ince jarabawa saikuma taki auruwa? Haba jama'a ku tayani ganin lamarin nan idan ba'a Aurarda da ita ba karuwa barnar zatayi kadauki hakan akan zakayi sadakatul jari'a hakan ya kamata aima irinsu bawai Asa musu karan tsana ba da tsinuwar dake Kara dulmiyar da doran kasa bawai a dinga gudun suba Allah kadai yasan yawan ladan dazaka Sa.......''dakata dalla Malam gafara kafun in hadaku duka in tumurmusa rainin wayau kana nufin in Aure ta dukda ubanta ke cinta komai kake nufi? Toh billahillazi babu Dan iskan daya isa ya cuceni da dadin baki waikai zakai mun wa'azin bogi uban waya hanaka yin sadakatul jari'ar kai? Komu matsiyata akeso mu dinga yinta muna Auran yara karuwai idan kanaso ka burge ba haka zakayi ba saika Mike kawai a daura dakai ko mai gadin gidan ka ka Kara masa yakarasa ragowar ubanta dawata wa'azin ka Mara ma'ana sannu limamin madina kabar ganin ana kaunarka kanaso ka Kara siyan soyyar mutane da dadin baki, dalla kauce bani wuri ba maganan matsayi akeyi anan ba, 'Alhaji muktar Ranshi yayi mutukar baci ganin yanda Musa ya kwance mai zani a tsakiyar kasuwa duk girman shida daraja shida mutane keyi, abun takaici wasu burgesu Musa yayi yayinda dayawa ke dariya da ganin wautan Alhajin, cikin sanyin jiki yaje yaja hannun liman tareda makwabtan dake jikin gidan shi mutum biyu gefe suka koma cikin minti kadan liman yafara magana a lasifika,toh jama'a Alhmdlh ina cikeda farinciki tareda Kara ma Allah godiya akan lamarin daya faru yanzu wani baya taba Auran matar wani, duk a gyara Zama Dan Allah a kimtsa za'a daura Aure....'da uban wa? Inji musa, badai dani ba? Babu Wanda yabashi Amsa I'lla iyaka sadakin shida aka mika mishi dubu talatin chif, nan yaita washe baki yayinda ya zauna bako kunya harda lankwashe kafa cikin yan kallo shima yanaso ya kashe kwarkwatar idonsa, ya'u kuwa da garbati sakin baki da hanci sukayi, nanda nan jama'ar wurin suka shaida Auran *Abdulkareem muktar tareda Aisha Ya'u* akan sadaki Naira dubu hamsin nan take Alhaji muktar ya kirgo su tsaf makwabtan shi sune waliyan Ango sumai unguwa kuma waliyan Amarya duk Wanda ke cikin masallacin ba karamin mamaki yayi ba, ya'u kuwa hawaye kebin idon shi wani nabin wani yatashi jiki na rawa har inda Alhaji muktar yake zaune zubewa yayi hade da rike kafafun shi duka biyun sai bude baki yakeyi amma yakasa magana sai hawaye kawai, damke kafan Alhajin yayi sosai sai nishi da numfashi yakeyi idon shiya kafe a sama, dif ya zube a wurin zuciyar shi ta buga lokaci daya baiko motsa ba nan akayi kanshi ana salati, 'Vairus kuwa baiso haka ba domin kadan yake jira yace a daura Auran dashi dama Addu'ar shi daya Aisha tayi kwantai yaga samu yaga rashi.

*Mr's Sadik Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Yah Rabbi duk inda na zaga duk inda na leka kowa Ustaziya harna rasa bakin Magana, waya kona amsata babu iyaka messages kuwa na mutane har wayata na daukewa, shin ta ina zan fara muku? Gskia mutum Rahama ne, nagode da Addu'ar ku a gareni masoya, Ustaziya fans group kuna Sani nishadi Mara iyaka comments dinku na jiya naci dariya, godiya gaduk masoyan Ustaziya makwaftan Aisha ina gaisuwa da kawayan ta tace ace muku adaina kushe mata Angon ta hakanan take san abunta.🙏🏼😍*

*Dedicated to sister Husnah Amarya*

17
Chapter 10 · 0% Book details