← Book details Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 40

Sashe 22

Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Misalin karfe hudu bayan la'asar Bilki ta Rakata har gidan Mamie inda suka tadda ta a kitchen nan suka hau tayata aiki cikin sakewar fuska ta tarbe su harda rungumar Aisha sam Mamie ta watsar da komai inda ta rike Aisha da hannu biyu biyu ganin hidimar da Aisha take musu muddun zataso saita kawo musu girke girke masu mutukar dadi ta dauke su tamkar sune suka haife ta hakan yasa suke matukar kaunar ta, wurin shida saura suka gama taya Mamie aiki inda nan bilki taja Aisha bedroom din Mamie a cewarsu bayi zasu shiga, kwalliya taima Aishar mai kyau sai zuba kamshi takeyi nan suka fito bilki tanama Mamie dake zaune a parlor sallama ya shigo cikin shigar kananan kaya hannun shi rikeda katuwar Leda da Alama siyya yaima iyayan nashi, mintsinin Aisha bilki tayi tana mata nunu da ido Wanda Aishar ta fahimce abunda take nufi darasin da sukayi yau takeso yafara aiki tun yanzu, 'mai sona, Aisha ta furta hadeda kashe masa ido daya Wanda chak ya tsaya kamar Wanda akaima umarni kodai kunnan shi ke jiyo mishi gaibu? inda takarasa wurinshi cikin natsuwa tareda amsar ledar hannun shi, 'sannu da zuwa Ur Excellency, ta furta cikin yalwatatciyar murmushi harda dan riko hannun shi inda ya bita zagwai zagwai kamar rakumi tagama kashe shida mamaki, Anya Aisha Nada hankali kuwa? Meye haka kuma? Mamie kuwa sun gama burgeta kana ganinsu kaga masoyan da suka jike a soyya hakan yasa taita zuba murmushi tareda Kara godema Allah daya Kara hade kansu, oooh namiji munafuki ji yanda ya bita saikace bashi bane yayi gudun hijira ranar da aka daura musu Aure,oooh yaran yanzu saisu, Mamie take zancen zuci inda takosa daddy yadawo taimasa Albishir, Bilki kuwa Dan dukawa tayi ta gaishe da AK, ina wuni yaya, kallon ta yayi ganin ko kallon Arziki bata masa tun daga Randa ta same shi yana dukan Aisha ko sallama batayi idan tazo gidan, bata jira amsar shiba nanta waiga ta kalli Aisha, oooh sister saboda yaya AK yazo shiyasa aka Fasa rakani bakomai Mamie kinga tun yanzu anfara min hannunka mai sanda koh idan naji haushi nima inyi Aure, 'da gskiar su takwara ta kema kiyi Aure ki kyale mun yara na banasan Sa ido, yauwa Mamie gaya mata, inji Aisha tafadi tana tunkarar dinning dinda suka gama jera abinci akai, 'bari ma kigani mijina zan sama abinci nasan baici komai ba tunda yau ban wuni a gida ba shikuma ba abincin waje yake ciba, 'aiko dai ya gado daddyn kune daughter shima haka yakeyi baicin abincin kowa inba nawa ba, Wucewa bilki tayi renta yayi fari fes ganin tunda AK ya shigo da sallama yana zaune kamar Wanda aka dasa shiko gogan sai bin kowa dai'dai yakeyi da ido yana ganin Dan karamin dramar da ake tsarawa a parlon nasu, shirya abincin tayi a gabansa inda shima ya kalleta, wato dashi zata buga game kenan ohk let's c who will succeed, yafadi murmushi a fuskarsa, 'Amma kinsan bani kadai nake cin abinci bako? Mamie kinga saboda gulmar ganinki yau takicin abinci dani ya fadi da iyakar gaskiyar Sa yayinda ya Mike harda rikoma Aisha Hannu zaunarda ita yayi a kasan carpet din shima ya sauka, bari in dauko extra spoon tafadi tana shirin mikewa, 'nooo honey bunch ban yarda ba yanda mukeyi a gida zamuyi da spoon daya zamuci, yafadi yana mata kallon let's keep playing the game, 'ooooh ni Bilkisu naga abunda yafara fin karfina haka soyyar ta maidaku? Babu ko kunya AK kuyi abunku lokacin kune nima bari in lalubo tsohon mijina inji inda yake tafadi tareda dosar dakinta dauko waya ta kira daddy a cewarta itama tanada mijin kuma ta iya soyyar, tana wucewa ya dauko full spoon dinda ya cika tafda shinkafa da miya bakin Aisha ya dosa murmushin mugunta kwance a fuskarsa saida yazo saitin bakinta ya Saki spoon din nan abincin ya zube a jikinta harda chokalin, Oooops am sooo sorry darling wiffy yafadi yanasa hannu da niyyar kakkabe mata da gayyah yake dukanta inda cikin ikon Allah gaba daya ta naimi tsoran AK a Ranta ta rasa, Worry not hubby karka damu Anything for you my luv, tafadi tareda shafa gefen bakinsa, 'Anya Aisha ba gamo tayi ba😫wasa wasa fa yaga kamar ba Aishar saba har cikin idonshi take kallo yanzu batako kyaftawa a'a kodai a Asibiti tayi gamo da Aljanar rashin kunya ne? Idan zai tuna da safe har kuka saida taimasa tana durkushe a gabansa, Mamie ceta katse su inda take shaida musu daddy nakan hanya, 'yauwa dama magana nakeso inyi daxu dukanku, tattara kwanukan dake wurin Aisha tayi Wanda itace ta cinye kusan abincin dake ciki, saida ta gyara gun sannan tadawo ta zauna tareda fuskantar Mamie, banaso ku fassara maganata nasan komai nufi ne daga Allah babu mai badawa kuma mai hanawa sai shi, tafadi ko kadan Aisha banaso ki fassara magana ta dawata fuka sanin kanki ne bakida banbanci da diyarda na Haifa a cikina harga Allah ina jinki sosai a Raina, abun na damuna Aisha nakosa inga jikokina nida daddyn ku a karo da dama munso muyi muku Maganar amma bamusan ta inda zamu fara ba idan wani Abu ne na daban sai a nema taimako idan likita zaku gani gara asan abunyi amma Abu shekara Uku shiru kodai kun tsaya sisi ne? Tafadi tareda kafe Aishar da ido, yauwa Mamie AK ya furta Ranshi fal farincikin yanda zai gumama Aisha, Wlh Mamie maganarki haka take, ya furta tareda mikewa ya koma kujeran Mamie, kwalla ne suka fara ambaliya a fuskar Aisha dake Duke a kasa ganin yanda AK ya Mike tasan wani bomb din zai Dana mata, "have confidence wani sashi na zuciyarta kece mata, dnt let him see ur weaknesses again u r far more beyond that Aisha.
, subhanallah Daughter maiya faru kuka kuma? Idan maganata yamiki zafi kiyi hakuri daughter......ko kadan Mamie kin Sosa mun abunda ke damuna wlh babu yanda zanyi ne Allah ne shaida ta shike bani maganin Hana daukar ciki a cewarsa bayaso jikina ya baci ina haihuwa zan Zama mama kuma bai shirya Zama baba ba Wanda shine da naki amincewa munsamu sabani akan hakan yafita harkata haka nan na Amince amma wlh raina baiso ba amincewata shine sanadiyyan shiryawan da mukayi yanzu tareda Soyyah da farinciki a gidanmu.....Ashe kai mutumin banza ne Abdulkareem? Innalillahi mai nake shirin ji ni bilki? Whatttttttt sukaji an furta da karfi yayinda kallon su yakoma kan Daddy da shigowar shi yayi daidai da bayanin da Aishar keyi, mikewa AK yayi jikinshi na digarda zufa kallon Aishar yayi charaf suka hada ido nanta kashe mishi ido daya harda gwalo fuskarta taf da ruwan hawaye.

*Mrs Saddiq Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*

26
Chapter 22 · 0% Book details