← Book details Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 40

Sashe 13

Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ankai ya'u gidanshi na gaskiya saidai muce Allah ya gafarta mashi idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani, yayinda Garbati yace baza'ai zaman makoki ba sanin babu abunda za'ai a wurin sai gulman mamacin hakan yasa kowa ya watse badan rai yaso ba, 'Mamie ceke tsaye a parlor sai zufa takeyi dankwali rike a hannun ta tunda abun yafaru yan'gulma suka gaya mata komai tareda cikama wandon su iska gudun kada Alhaji muktar yadawo ya samesu a gidan, bakaramin tashin hankali ta shiga ba inda har kukan bakin ciki saida tayi ta kudiri aniyar saidai tarasa Auranta akan Auran Aisha amma Sam danta bazai taba Auran Yar'duniya ba, shigowar Alhaji muktar neya Kara tunzura ta da hanzari ta tarbe shi bakin kofan falo inda taita ruwan Masifa tana zagin Ramata akan asiri sukayi banda aikin Asiri ina AK ina Auran Aisha? Ance kwarya tabi kwarya ko cikin kwaryar bakowace kwarya bace tadace da dangatan danta ba, Aikin banza aikin hofi wlh saiya Saki karuwan nan bazan Zama abun nunawa a gari ba yarinyar da ubanta ke neman ta, 'kallon ta Daddy yayi tunda tafara haukan ta baice mata komai ba kanshi na Sara mishi babu abunda yake bukata sai bcci a lokacin dukda ana neman karfe biyar na yamma, wucewa zaiyi ta tare mishi hanya akan saitaji dalilin tozarcin daya jamusu, 'cikeda takaici ya kalle ta sama da kasa, 'wai bilki baki San mahaifin yarinyar nan ya rasu bane yau? Karona farko tun Auran su dataga yamata irin kallon nan, 'toh sai me? Nice na kashe shi? Ina ruwana dawata Rasuwar shi? Allah na tuba ai gara daya rasu koba komai an rage mugun iri a doran kasa, bai dameni ba wlh yau yau sai an sakar musu da diyarsu, 'hankade ta yayi saida tafadi akan kujera bayasan biye mata bare yadauki mummunan hukunci cikin fushi, yanufa dakin sa yayinda yarage kayan jikin Sa, wai maiyasa mata wani zubin sukeda Karamar kwakwalwa ne? Idan tanada magana dashi aiba haka ya kamata ta tunkare shiba yaushe bilkin ta chanza Halinta ne? Shi za'a kawoma iskanci a cikin gidanshi aiko zaiyi maganin ta daga ita har yaron nata Aure kuma zaiga ubanda ya isa ya raba shi muddin yana raye.

Gogan kuwa yana chan yana harkokin Sa a cikin gari gaba daya gidan nasu baya mishi dadi yanzu ya gwammace yabata lokacin Sa wurin business dinshi hakanan yau ya tsince kanshi da Muguwar faduwar gaba harsaida ya gayama wani Abokin shi inda yabashi shawarar yaita Addu'a kila Alkairi ne zai Same shi, hankalin shi gaba daya ya karkata kan gida hakan yasa shida saura ya doshi unguwan nasu tunda matasa suka hango motar shi nan akaita ihu ana daga masa hannu, Ango Angooo Angoooo kawai kakeji suna fada suna shewa, mamaki yayi toh dawa sukeyi? ango? Kodai sunyi tsammanin wanine bashi ba? Dariya yayi harda Jan tsaki yakara murza zaman hularshi a kanshi, 'oooh mutane da rigima sukeyi kaji wai Ango nida ko budurwa bantaba yiba naiman rigima kawai yawancin suma ban sansu ba, 'yafadi shi kadai, yana isa kofar gida tunda yayi horn kafun mai'gadi ya bude mai tuni wasu sun biyo motarshi a baya inda akan dole ya bude musu glass din motar cikeda mamaki, 'Ango kasha kamshi Dan Alaji yaushe za'a hada mana walimar maza tunda Auran yaxo bawai an shirya bane, 'walimar maza? Ya tambaya cikin mamaki, 'au eh mana wacce akeyi bayan an daura Aure mana, koda yake jeka huta muna nan munanan muna Sa ido Dan Allah kada a manta damu Dan Alaji, wooooo sai Ustaziya yasin Allah barku tare, 'dayaga abun yazama hauka Jan motarshi ciki yayi cikeda Al'ajabin samarin unguwar tasu, haka yafito ya rufe motar jikin shi dukyayi sanyi, mai'gadi kuwa sai kirari yake masa tareda Addu'ar Allah ya sanya Alkairi, 'wucewa yayi baiko bi takanshi ba inda yana shiga parlor ya tadda Mamie ta buga tagumi da hannu biyu biyu cikin yini guda harta Dan fada saboda tashin hankali, 'subhanallah Mamie lfy? Ya tambaya yayinda ya zauna kusada ita, kallon shi takeyi idonta ya rine yayi jajir, 'AK kasan abunda babanku yaimana? Kaji labarin tozarcin dayayi mana? Toh an daura maka Aure yau bayan sallar juma'a kasani idan baka Sani ba kabude kunne kajida kyau kazama mai mata mai iyali, tafadi tareda gyara zamanta harda buga cinyarta, 'dariya yayi har saida fararan hakoran shi suka bayyana, haba Mamie wlh kema kin iya tsokana Auran lfy saikace yaro, 'riko hannun shi tayi tareda kafa mishi ido babu Alamar wasa take kallon shi nan jikin shi yayi sanyi ganin yanayin nata, 'Abdulkareem nataba maka irin wasan nan? Wlh yau aka daura Auran kada Aisha diyar mai shayi, Mikewa yayi zumbur hadeda goge kunnansa harda Dan bugawa a tunanin shi baiji dakyau bane, 'eye? Yafadi yayinda yayi jifa da hular kanshi Mai kikace? Mikewa Mamie tayi hadeda maimaita mai abunda tace, 'chab haba wasa yakeyi duk matan duniya?jada baya baya yakeyi, Idan hukuntani yakeyi saboda naki Auran diyar Aminin Sa toh yanzu na yarda, Mamie Yammata nawa nema a gidan? Sun kai hudu? Wlh idan dukansu yakeso in aura na yarda akan abunda kike danganta nida shi, wlh ina sansu, ko Auran kauye ne aimun na Amince, kowacece na yarda Mamie ina Dadyn? Yafadi yana waige waige waiko zaiga Dadyn a wurinda suke, *Ina Dadyn?* yafadi cikin razanannan ihu har saida jijiyoyi suka furfuto akansa idonshi kamar zasu fado kasa sai zaro su yakeyi sunyi jazur, 'shi maiyasa bai aurota ata biyu ba? Maiyasa baiyi sadakatul jari'ar da itaba bayan yataba Aure? Tunda yataba Aure maiyasa dasai yakara da bazawara why me??
Why?
Why?
Auran fari infara da bazawaran titi?
Haba!
Haba!!.
Bazawara duk mazan gari sun Santa fa, Ustaziyaar banza? Kirarinta fa kenan, wai Ustaziya saboda yanda takeda fuska biyu, Ustaziya koko yar'duniya? yafadi yana yarfa hannunsa duka biyun saikace zai Mari mamin, saidai shi Dadyn ya aureta wlh sakinta zanyi Dan bata auru ba sai zaro mata ido yakeyi itako baki da hanci tasaki tana kallon ikon Allah yayinda take girgiza kanta cikin bacin randa bata taba tsintar kanta a cikin saba, ji takeyi kamar ta rufe shida duka, Dan ubanka AK ni zakaima bakin ciki? da tsufa na kake mun fatan kishiya? Yaron nan bakada mutunci kishiya kakemun fata da tsufana diyar cikina yarinyar Dana raina da hannuna? Lallai ko kishin mamarka bakayi kakemun fatan babanku yakara Aure? Tafadi da Alamar maganar ba karamin zafi taimata ba.

*Mrs Sadik Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie*

*Ina kuke yan hannun dama na🤝🏻godiya Mara iyaka sister futu marubuciyar Ramlat, tareda Asiyar Bachaka marubuciyar Danasani keya, leemat muna jiran sabon novel.Nagode sosai da kaunar ku a gareni.*

*Dedicated to sister Husnah*

18
Chapter 13 · 0% Book details