← Book details Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 40

Sashe 2

Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tafiyar minti goma ne daga gidan nasu zuwa wurin haddar kodata karasa sainaga harta wuce makarantar tasu ta tsallake babban titin dake gaban makarantar duk a tunanina ko biro zata siya😕sainaga ta bude bayan Wata shegiyar farar rangerover 2016 ta kame a ciki saikace ta tsohon ta, batare da bata lokaci ba aka cilla motar akan titi cikin kwarewa koda na leka motukin motar macece mai tukin, Yammata biyu ne a gaban motar cikin Wata shegiyar shiga kamar wadanda suka zo daga America a cikin Daren saika rantse da Allah musulunci baije musu ba idan kayi la'akari da kayan dake jikin nasu, 'leemah kin bata mana time fa, inji Wanda ke tukin motar, 'sorry meena abun ne saida siyasa kinsan iyayen namu sai a hankali Ummi nake Dan lallabawa saboda hawan jinin ta danta dagus banda matsala yaci lokacin shi, tafadi tana zame hijab dinta tareda Jan tsaki, bari in cire wannan buhun dukya dumama mun jikina mtseww, vest ce Mara hannu iya Mara tareda guntun wando a jikinta, "yah club din zamu wuce direct koh? Wacce take gefen Direver ta tambaya, noo nooooo feenah r u kidding me? Take a luk at me please saina watsa ruwa sai zufa nakeyi and I need to change my clothe.

Unguwa ne na masu hannu da shuni motar ta dumfara horn naga tayi a wani katotan gida madaidaici, bude gate din gidan wani buzun mai'gadi yayi, wuri ta naima tareda ajiye motar suka furfuto cikin takun kasaita leema kuwa tuni ta nunke hijab dinta ta Danna cikin jakar islamiyar da babu komai ciki sai kayan maye da kayan kwalliya, a mota tabar jakar sanin tanada duk abunda take bukata cikin gidan, wow cikin gidan yafi wajen gidan haduwa nesa ba kusa ba saidai wani abun mamaki gidan babu kowa sai Yammata Uku da suka shigo yanzu, cikin gaggawa ta fada hadaddan bayi tareda sakar ma kanta ruwa tanayi tana waka fitowa tayi zigidir haihuwar uwarta dukda towel dinda ke bayi I'lla Dan karami data rike a hannun nata tana goge jikinta tana wakan "cilindion mai taken Am Alive" kawarta meena ceta buga mata duwawu nan suka hau wasan banza babu kunya a haka harta gama shiryawa nan take ta rikice daga diyar musulmai takoma leemah sak, Yar'malam taki halin Malam, kawayan nata suka furta cikin shewa suna jinjina mata ganin yanda take karairaya a gaban madubi, "da karatu gwanda rawan disko tabasu amsa tareda Juyowa tana girgiza kirjinta Wanda babu abunda ba'a gani ko bra batasa ba.

More comments more typing.

*Mr's sadik Rumah*💅🏻
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*

4

Koda suka isa club din suna shigowa aka fara bude musu hanya anga dakin hutu sun shigo Wanda hakan ne taken nasu, wani baki dogon saurayin dake zaune kallo daya zakai mai kasan babban yaro ne kusan minti talatin da shigowar shi wurin barasa yake sha batareda kula kowa a wurin ba da alamar jiran zuwansu yakeyi ganin ya Mike lokaci daya ya dumfare inda suke batareda bata lokaci ba cikin kwarewa ya ruko kugun leemah tsaf ta lafe a kirjin nashi tana shafawa da hannun hagu basu ko damuda yawan mutanan dake wurin ba, saitin kunnanta yakai bakinsa tareda furta mata *Ustaziya koh Yar'duniya*?
Lumshe ido tayi cike da duniyanci ta chapko lips dinshi na kasa ta shiga tsotsa harda Dan cizon shi Sannan takai bakinta saitin kunnan shi yanda zaiji abunda zatace *Duniya gidan kashe ahu tun kuruci bai wucemu ba* tureshi tayi tana juya kugu ta nufa wurin da aka killace saboda shan hayaki tahau busawa cikin kwarewa da wayewa ta hanci ta baki kamar yanda sauran frnds din nata keyi su a ganinsu kananan chicks neke rawa a club sudai kawai suji sun hau saman gajimare sujisu a duniyar sama yauwa shine magana Alhaji.

Hayaniya ke tashi a parlon Abokanan keta zuba fira AK kuwa sai kumbura yakeyi ganin har 8:30 babu miya ba Alamar Sa dukda komai da komai na wurin kowa nacin abunda yake Sha'awa sunata zuba santi,bakinta rike da sallama shigowa tayi da kular miyar cikin natsuwa kanta da katon mayafi ta yafa, Amsa sallamar dukansu sukayi banda oga gaishe su tayi cikin sakin fuska suka amsa yayinda take Allah Allah ta ajiye tabar wurin "madam sannu da kokari wannan girki haka shiyasa AK kewani kiba yayi fresh abunshi gskia Abokina kayi sa'ar mace zan turo madam dita a Kara hora mun ita gurin girki inji Abokin shi Musa Wanda dama yasaba zolayar ta, murmushin dabai wuce bakinta ba tayi ganin yanda gogan yakara hade Ranshi kamar hadari saika rantse baya wurin, hannun shi rikeda da kofin mug dinda yakeshan kunun gyada sai girgizawa yakeyi kamar baisan da halittar ta a wurin ba dayake kusa dashi take tsaye ta juya kenan zata bar wurin ya Saki kofin cikin rashin Sa'a tayi saurin matsar da kafarta aiko ya tarwatse a kasa yayinda takaici yakara cika shi domin a kafarta yaso ya tarwatse duk Wanda ke wurin sunga abunda yafaru kowa yayi shiru yana kallon shi ba halin magana yahau ruwan masifa, barin wurin tayi cikin hanzari ta dauko tsintsiya ta kwashe tareda goge wurin kamar yana jira tabar wurin yabita kitchen din ta zauna kenan tanacin abincin ta akan kujerar kitchen din, a kanta ya tsaya yana Kare mata kallo, " miyar Egusi dinda ke gabanta ya dauka yana jujjuyawa a hannun shi aikuwa yafara juye mata a jikinta a Hankali harya gama Tass, ferfesun kan Sa ya dauka Wanda tadan zuba zata sha, batareda bata lokaci ba ya daga shi harda murmushin mugunta jin yanada zafi sosai a kanta yafara zubawa da gudu ta tashi daga zaunen ta matsa gefe jin azabar da kanta ke mata rokon shi ta shigayi yayi hakuri karya Kara tozartata ta gwammace yaimata su kadai a gidan, "wannan ne kike kira miyar Egusi? Eye? Dan mugunta saikace kashin jariri? Babu abunda kika iya sai jawo hankalin yan iskan kwartayan ki nothing baki iya komai ba sai tarin iskanci da munafunci mai fuska biyu bakar munafuka, Please! please!! Am sorry I did my best, " oooh this is what u called ur best swt wiffy? Kureta yayi a jikin bangon miyar dake jikinta ya lakuto yayinda ya murza mata akan ciwon dayaji mata a baki kafun ya fita, well make sure kin cinye komai kin kuma gyara wurin nan cox niba kazami bane kamarki bazan dauki Albazaranci ba, yafadi yana cusa mata katon sakwaran daya yanzo a hannun shi, 'hannu ya wanke a fanfo sannan ya wuce parlor kamar Wanda akaima bushara da gidan Aljannah, saikace bashi ke cika yana batsewa ba nan ya zage sukaita fira da frnds dinshi daya cikasu da mamaki bakaramin Abu kesa AK dariya ba sai washe hakora yakeyi harda zuba sakwara da Egusi tunda yaga tanaci a kitchen kanshin ya dame shi sai hadiye miyau yakeyi nan ya zage ya kwasa girki yana buga santi da shewa, Aisha kuwa bakinta ta toshe hawaye nabin kumatun ta maiyasa take kuka? Abunda muguntar shi yagama bin jininta ta rigada tasaba Duk abunda yake mata bata taba jin tsanar shiba ko kadan takaicin ta kenan, "shegiya zuciyata maiyasa zakimun haka??
Laifin maina miki kike gasani tareda horo mai tsanani? Duk cikin azabar dazaki gana min maiyasa zaki samun soyyar maso wani? Soyyar abunda baida makiyi bayan ni?

*Mr's sadik Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?*🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀

*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*

5
Chapter 2 · 0% Book details