← Book details Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 40

Sashe 27

Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Congratulations Amaryar shagali, gskia kin iya zabe wato ko'a cikin mazan Auren saida kika zaba kika darje naga ango ba karya yayi ya cika namiji harna mishi Addu'ar zaman lfy yayinda muka gaisa a wurin daurin Auran naku, da Alama anjima zan kai mishi ziyara na musamman tareda labari mai dadi harda gudunmawar Auran naku zan hada in bashi, hmmmm kina nufin da cikina zakije gidan wani ya turmushe ki? A wannan Karon kinyi karya wlh wlh San cikina nakeyi idan har wani Abu yasamu cikina zaki tabbatar dani tantiri ne kallon ki kawai nakeyi inga karyan duniyancin ki nabaki nanda Minti Goma sha biyar idan baki sameni a dakina ba, hmmm ki saurari jin labari mai kayatarwa tareda girgiza jama'a A gidan TV anjima da daddare sannan kada ki manta ki ajiye Redio a kusa domin sauraran program din Inda ranka zakiji labarin Diyar malamai budurwa mai Aure da cikin shege, hahahaa.*

Hijab din jikinta ta shiga girgizawa rufa dukya rufeta, innalillahi na shiga Uku ni halima yayinda ta Mike tsaye, Kallo ne ya koma kan Amaryar da Akema wa'azi a cikin mutane, 'lfy? Maiya faru? Nan kallo ya koma kanta Ashe a fili tayi maganar, Antyn tace tajata gefe inda take tambayar ta dalili, cewa tayi babu komai Wata kawarta ce aka turo mata text akan ta rasu, toh'ai Addu'a ya kamata kiyi duk kin tada mana da hankali, wucewa Antyn tayi inda ta shaida ma masu tambayan dalilin salatin Amarya, Meena ne suka jata lungu inda tana kuka take shaida musu Abunda yafaru wani munafukin ya gayama mahuta tanada cikin shi kuma yaki fita, wani munafukin ne ya gaya mishi Auran ta?,Dan girman Allah ku nema mun haryar fita Kota Katanga ne wlh mahuta zai iyayin fiyeda haka wyyooo ni kaina taya zan fara? Ya zanyi? Kuka takeyi inda taita kiran mahuta yaki daukan wayar text taita mishi babu reply inda daga karshe ta Amsa wayar meena ta kirashi aiko ya dauka, "yanzu ni zaka tozarta cikin sha'shakar kuka take magana hannu daya akan kirjin ta, duk soyyar Dana gwada maka? Kada ka manta fa kaika fara Sani na,....eh kuma kika yaudareni kika Auri wanina ba munafuka Karamar yar'bariki, 'kasan har duniya ta tashi bazan taba ba wani namiji irin zumar Dana baka ba ya kamata inci koda darajar wannan ne a gunka, 'lashe bakin shi yashiga yi tuno irin Roman daya kwasa dukda Yanzu bayajin irinshi a tareda ita, murmushi yayi tuno gskia ta fadi, 'dakyar da sudin goshi suka bashi hakuri itada su meenah tareda Alkawarin nanda kwana biyu zatazo gareshi, 'idan ma bakizo ba wlh wlh zaki ganni a gidan naki, kina nufin zaki bashi kanki cikina fa? 'Nooo Babu abunda zai shiga tsakanin mu nama Alkawari saboda inada ciwon da bai gama warkewa ba, 'Shegiya leemah, shikenan saimun hadu sai nazo yafadi tareda kashe waya yana dariyar mugunta.

Misalin karfe Tara na Dare yan'daukan Amarya sukazo inda Abokan AK sukaita kwasar su Amarya tasha fada ba laifi sai kuka takeyi za'a rabu dasu Malam dakyar aka banbare ta daga jikin su malam inda aka kaita gidanta daya gaji da haduwa, nan su meenah suka Kara kulewa harda kwallar takaicin daular da leemah ta shigo babu Wanda baiyi santin gidan ba Addu'a kuwa sunsha shi, an damkar Amanar Amarya a hannun uwargida Aisha wacce bata gayyaci kowa ba sai kanwarta bilki datai ta kwantar mata da hankali inda da hannu biyu biyu ta Amsa bilki na tayata sai washe baki sukeyi nan akaita yabon Aisha ba karamin rudewa Leemah dasu meenah harda dangin amarya sukayi ba ganin surar Aisha Cikakkiyar buzuwa komai Yaji mai diri kyakyawa black beauty, sanye take dawani danyan leshi kalar ruwan kwai da mint green bilki tamata kwalliya na Musamman irinnan amare kannan yasha daurin gwggwaro anbude gashinta ta tsakiya ga kananan kitso an yarfa mata gashin nan masha Allah kunshi hannu da kafa Jan lalle a tafin kafa sai zuba kamshi takeyi nesa ba kusa ba tafi Amarya kyau nan aka fara kananan gulma wasu na cewa idan banda jarabar namiji Yanada mace irin wannan Auran mai zai Kara kuma? Leemah hankalin ta yagama tashi inda su meenah keta dariyar mugunta a zuciya a fili kuwa lallashin ta sukeyi a cewarsu da baya Santa da bazai aurota ba ai yasan da matar tashi, kowa ya watse Leemah ta tasa keyar su meenah akan babu mai kwana mata a gida dole taji dumin jikin mijinta yau, badan sunso ba suka tafi suna mata Allah ya isa ta hanasu Dana gadon da za'ai bidiri akai.

Sai karfe goma da Rabi Ango ya shigo indai kai tsaye dakin Amarya ya nufa hannun shi dauke da manyan ledoji kasancewar ya Hana kowa rako shi inda akaita mishi tsiya, kwance ya tadda ta tsakiyar gado kaiba dankwali baiji dadin ganinta haka ba shida yake tunanin zai ganta da lullube ya yaye da kanshi, sallah ya umarceta suyi kai tsaye ta shaida masa batada tsarki yadanji takaici yaso yasan zakin mace ayau nan sukayi Addu'a sosai ya ciyarda ita taci ba laifi, gassar kaza ce sai yogot inda kai tsaye ta shiga wanka jiki na rawa ganin irin kyau dinda AK yakara mata nan wani mugun kwadayi ya motsa mata amma ya zatayi? Nan gani nan hange, shigar kayan bcci tayi kallo daya yaimata ya kauda kai ganin ko kadan bata kaima rabin tunanin shiba yanda kasan Agwagwa haka surar jikinta yadawo ba shape ba komai ga cikinta yadan tura kadan kamar karamin tunbi, samun kanshi yayi dajin haushin ganinta a hakan ko kadan bata burge shiba tunowa da surar jikin Aisha hakan yasa shi mikewa tareda Jan karamin tsaki yabar dakin, Jiki a sanyaye takoma gefen gado hadeda buga uban tagumi,mai hakan ke nufi? Daga kallo daya a first 9yt saikuma tsaki? Tayi tunanin zai tashi ya rungume tane ya rikice kamar yanda sauran samarin ta keyi, dakin shi ya shiga inda yayi wankan tareda chanza kaya zuciyarsa na azalzala masa yanaso yayi tozali da Aisha yanaso yaga halinda take ciki kodai tana kukan kishi ne? Murmushi yasamu kanshi dayi sanye da kayan bcci ya doshi dakin ta inda a karo da dama yake tunanin shiga, bude kofa tayi da niyyar zuwa kitchen zata ajiye Kofunan da akai Amfani dasu sanye take cikin hadaddiyar rigar bcci tayi matukar kyau, Jada baya tayi wyyoo Allah, harga Allah taji tsoran ganin mutum tsaye a bakin kofa, gefensa ta ratsa zata wuce inda zuciyarta ke suya ganin shida kayan bcci, 'tare hanya yayi, nanma takara yunkurin wucewa yakara tarewa, 'Malam wai lfy? Tafadi cikin harara, 'nazo kisama Aurena Albarka ne yafadi murmushi a fuskarsa samun kanshi yayi da farincikin ganinta tun bare yau tamishi kyau fiyeda koyaushe, jikinta kawai yake kallo ji yakeyi kamar ya ganta kwance a kirjin shi ....'Allah sanya Alkairi, tafadi yayinda ta wuceshi, tsayawa yayi anan harta fito daga kitchen din takara wuceshi inda ta buga kofarta tareda Danna key, Dakin leemah ya shiga da gudu inda har'saida taji tsoro ganin yanda ya shigo kamar maibin wani Abu, ledar kajin daya shigo ya dauka dama kaji Uku ya siyoma leemah sauran biyun ya dauka hadeda juice dinda suka rage, 'lfy kuwa ango Na ina kuma zaka? Baibi ta kanta ba dakin Aisha yakoma inda yahau buga kofar da karfi, tsaki taja yayinda takara Jan bargon ta hawaye daya nabin daya azababben kishi ke damunta, ganin baida niyyar dainawa harya fara kiran sunanta hakan yasata mikewa a hatsile, Malam wai lfy? Tafadi yayinda ta bude kofar Konaci ban biya bane? Hannu daya rike a kugunta tana girgiza jiki cikin masifa ji take kamar ta kifa masa Mari, 'Aisha kuka kikeyi? Kukan kishi na? Ji idonki laaaa wlh na kamaki hawaye ne, goge idonta tayi bataso yaga kukanta ba harga Allah ta manta kuka takeyi da bata bude kofar ba, 'mtsww lfy nace bccin ma baza'a barni inyi ba? Ina kabar matar so tazo taja mijinta, AK harda buga dariya abun yamai suger yau Aisha na kukan kishi,yarinya da tuntuni Abunda kikayi kenan kila Dana Dan huce, Anyway kazarki na kawo miki, mika mata ledar hannun shi yakeyi, wace kazar? Wacce na Aikeka ka kawo mun? Toh na yafe ka hada duka kaba matarso, BAMMM ta buga kofar tareda maida key, Juyowa yayi harda shewa yana dariya ya wuce leemah da tunda yafara buga ma Aisha kofa tafito ganin ikon Allah, cikeda takaicin daukar kazar Amarcinta take inda ta daure bata mishi magana ba a Ranta ta kudiri niyyar saita nunama Aisha ita Karamar yar'bariki ce saita gasa mata aya a hannu, Daki ta koma inda ta taradda AK ya kwanta wannan karan dariya yakeyi, ikon Allah, tace cikin Al'ajabi mai kuma ya sameka? Ashe haka Akeji idan ana kishin mutum? Kamar ya? Ta tambayeshi, ban gane ba?
Mu kwanta kawai Amarya bazaki gane ba, rufe ido yayi yafara sarrafata inda Yaji kirjin ta bawani labari Ashe ciko ne gashi sun zube sunsha matsan hannun gardawa kala kala Ranshi sai mamaki yakeyi har wani Dan kyama Yaji itako ta dage bako kunya wai a dole itama tanaso tarage zafi, haka nan yafara kiyasta surar jikin Aisha harga Allah bayajin komai gameda Amaryar tasa, da taimakon tunanin uwargida yake neman amsar budurcin Amarya inda cikin murya kasa kasa take Kara tuna mai batada Tsarki tana fashin sallah, ba haka yaso ba yaso ya rage azabar dayakeji kila idan ya dandana ta zai daina haukar Sha'awar Aisha, kila leemah zata mantar dashi surar Aisha.

*Mrs Saddiq Rumah💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie.*

*Dan Allah masu mun mgn ta private kuyi hakuri kada kuga bana Amsa ku, kunmin yawan dazan Amsa lokaci daya zan Amsa kowa a hankali aimun uziri please.🙏🏼*

*Dedicated to sister Husnah.*

31
Chapter 27 · 0% Book details