Sashe 11
Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kan Ya'u akayi ina rai yayi halinsa tuni nan aka dauki kabbara Allah sarki ya'u ashe yanada rabon ganin Auran diyarsa Allah ya dauki Ransa a wurin daurin Auran yar'sa, jama'a nata jimamin lamarin tun bare jarumtar da Alhaji muktar yayi, liman yabada sanarwa da la'asar za'ai mai salla akai shi makwancin shi nan danan wani yaro ya ruga gida batareda bata lokaci ba Amarya taci kwalliyar ta babu laifi tayi kyau tasha lallan gargajiya inda babu wasu yan biki masu yawa sai makwaftar da gulma ce yakawo su harda masu kawo mata gudunmawar maganin mata na Ni'emah maganin matsi kuwa ankawo mata shi babu iyaka wasu saboda cin fuska kawai zasuzo suna mata bayanin yanda zatayi matsi bilki ceke tanka musu yayinda Ramata ta kwabar musu kada kowa ya tanka sunaso ayi rigima ne kuma yau ranar farinciki ne, shinkafa jaluf akayi mai kyau sai faten tsaki, Amarya kuwa kawayan ta basu wuce mutum biyu ba suma Abokanan karatunta ne suka samu labari dukda bata gayyaci kowa ba suko sunzo, 'Aisha ta Auri AK Dan gidan Alhaji muntari Naira, abunda yaron keta shela kenan harya isa gidan, Kai zonan mai naji kana cewa bafa masan iskanci, inji Wata makwafciyar suda ta damki hannun yaron tana shirin ingiza keyarsa waje, Wlh wlh yanzu aka daura Auran Aisha da AK wannan baturan daya dawo kwanaki, yasin idan nayi karya Allah tsinan, 'mikewa Aisha tayi bako kunyar Amare tareda jawo hannun yaron cikin daki, 'ummah kinji fa abunda yake cewa, tafadi tana washe baki nan kallo yakoma kanta, koda karya yakeyi yagama faranta mata ayau tunda ya danganta AK a matsayin mijin Auren ta, nan mata akaita surutu ana karyata zancen, 'yo duk matan garinga hauka yayi dazai Auri diyar unguwan nan, haba Malam banda ma haka GA yara masu komai a unguwa kai dalla wuce kada in zabga maka Mari, inji wasu matan da abun yafara kaisu bango, 'yauwaaa sannan babanku Ya'u mai shayi yafadi ana tunanin kamar Maya rasu, 'salati aka dauka gaba daya nan kowa yagama yarda ya'u ya rasu, Ramata kuwa tunda aka fara maganar kallon kowa dai'dai takeyi tarasa abun cewa koda aka fadi Rasuwar ya'u ko motsi takasa yi nan aka dinga bata baki, ana haka Garbati ya shigo tareda rokon jama'a akan subar musu dakin yanasan ganawa da Mahaifiyar Sa, 'zaure suka koma wasu kuma na zaune kofar gida a cewarsu sai sunga abunda zai ture nadin buzu, 'kallon Aisha yayi yayinda ya kalla bilki, 'ki harhada duk wani abunda Musa yakawo na Aure harda kayan fitan bikin dayayi ta cire wannan na jikinta a hada da sauran a kawomun, sannan mama........babanku ya rasu koh Garba? Ta katse shi tana kallon cikin idonsa, Allah ya gafarta masa mukuma Allah yabamu juriya da tawakkalin rashin nasa, 'jikin shi yayi sanyi yayinda tunda abun yafaru sai lokacin Yaji hawaye nabin kumatun Sa na tausayin mamar tasu da kannan shi, Wata irin mace ce ita mai dakewar zuci? Bata taba bayyana sirrin Ranta, hannunta yakamo zaiyi magana, 'tashe kuje a suturta shi akai shi gidan shina gaskiya, kukuma ku share hawayen ku Addu'a zamu cigaba dayi, 'mikewa yayi zai fita saiya waigo tareda kallon Aisha wacce ta hade kanta da guiwa tana kuka kasa kasa, 'An Daura Auranki da Abdulkareem Dan gidan Alhaji muktar akan sadaki dubu hamsin, dukda tana cikin tashin hankali saida ta dago ta kalli yayan nata idonta taf hawaye, murmushin ke neman subce mata nanta maida kanta akan cinyar ta samun kanta tayi da mika tawassali tareda godiya ga Allah Ashe AK Santa yakeyi?
Ashe ba ita kadai take dakon soyyar shiba?
ashe zata Kara tsintar farinciki a Rayuwar ta lokacin data cire ran samun murmushi a duniyarta sai gashe bayan lokaci mai tsawo ta manta daduk kuncin ta dukda Rasuwar mahaifin ta nanan daram a gefen zuciyarta amma murnar Mallakar AK ya shafe duk wani kunci a tattare da ita, mikewa tayi kamar mahaukaciya tareda girgiza bilki datake gabzan kuka, 'Auta Auta kinji mai yaya yake cewa? Auta Dan Allah ki mareni Auta ki jijjiga ni dukda nasan ba mafarki nakeyi ba inaso in tabbata bani kadai naji Abunda yake cewa ba, cewa fa yayi nazama matan Aure kuma AK na Aura, yaya AK na,
Auta Ashe AK zan Aura? Ashe sona yakeyi? Ashe shine ya Hana Musa Aurena yayinda kaddara taso ta shiga tsakanina dashi, Ummah, tafadi tareda rarrafawa tana rike kafan Ramata dake binta da kallo itada bilki gani sukeyi tadan samu matsala akanta ubanta fa akace ya rasu yanzu amma tana murnan Mallakar namiji ko kunyar idonsu bataji, 'ummah kice wani Abu mana, kinji, kinji umman mu, Kuka tafara yi mai sauti inda kadan yarage Ramata tayi kanta da bugu ganin ta zube a wurin tana kuka mai taba zuciya taji tausayin diyar nata yagama mamaye ta datasan matsayin ta a wurin AK din datafi haka yin kukan babu Wanda ya lallashi wani cikin su Ramata kuwa babu koda digon hawaye a idonta.
Ankai ya'u gidanshi na gaskiya saidai muce Allah ya gafarta mashi idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani, yayinda Garbati yace baza'ai zaman makoki ba sanin babu abunda za'ai a wurin sai gulman mamacin hakan yasa kowa ya watse badan rai yaso ba, 'Mamie ceke tsaye a parlor sai zufa takeyi dankwali rike a hannun ta tunda abun yafaru yan'gulma suka gaya mata komai tareda cikama wandon su iska gudun kada Alhaji muktar yadawo ya samesu a gidan, bakaramin tashin hankali ta shiga ba inda har kukan bakin ciki saida tayi ta kudiri aniyar saidai tarasa Auranta akan Auran Aisha amma Sam danta bazai taba Auran Yar'duniya ba, shigowar Alhaji muktar neya Kara tunzura ta da hanzari ta tarbe shi bakin kofan falo inda taita ruwan Masifa tana zagin Ramata akan asiri sukayi banda aikin Asiri ina AK ina Auran Aisha? Ance kwarya tabi kwarya ko cikin kwaryar bakowace kwarya bace tadace da dangatan danta ba, Aikin banza aikin hofi wlh saiya Saki karuwan nan bazan Zama abun nunawa a gari ba yarinyar da ubanta ke neman ta, 'kallon ta Daddy yayi tunda tafara haukan ta baice mata komai ba kanshi na Sara mishi babu abunda yake bukata sai bcci a lokacin dukda ana neman karfe biyar na yamma, wucewa zaiyi ta tare mishi hanya akan saitaji dalilin tozarcin daya jamusu, 'cikeda takaici ya kalle ta sama da kasa, 'wai bilki baki San mahaifin yarinyar nan ya rasu bane yau? Karona farko tun Auran su dataga yamata irin kallon nan, 'toh sai me? Nice na kashe shi? Ina ruwana dawata Rasuwar shi? Allah na tuba ai gara daya rasu koba komai an rage mugun iri a doran kasa, bai dameni ba wlh yau yau sai an sakar musu da diyarsu, 'hankade ta yayi saida tafadi akan kujera bayasan biye mata bare yadauki mummunan hukunci cikin fushi, yanufa dakin sa yayinda yarage kayan jikin Sa, wai maiyasa mata wani zubin sukeda Karamar kwakwalwa ne? Idan tanada magana dashi aiba haka ya kamata ta tunkare shiba yaushe bilkin ta chanza Halinta ne? Shi za'a kawoma iskanci a cikin gidanshi aiko zaiyi maganin ta daga ita har yaron nata Aure kuma zaiga ubanda ya isa ya raba shi muddin yana raye.