← Book details Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 40

Sashe 31

Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahuta na layi kanshi kamar zai fashe mommy sane da daddy suna karyawa a dinning section ihu momnyn Sa tasaki ganin shalele na shirin faduwa fuska jini da majina da gudu suka tashi har'rige rigen rikeshi sukeyi itada daddyn Sa inda babanshi yaita kunduma manya manyan Ashar tareda rantsuwar daukan fansa akan duk Wanda keda hannu akan abunda akaima dan'sa likitoci yashiga kira saikace Wanda yarasa kafafu inda yakira commissioner of police tareda lauyoyi manya guda biyu a cewarsa suzo akwai katon tashin hankali a gidansa yanaso yayi shari'a dawasu daga yau har'igiya tayi rara, 'batareda wani kunya ba mahuta ya gayama iyayanshi duk abunda yafaru cikin sha'gwaba nan mommy takara kulewa, 'matsiyata suba abun farinciki bane ace Dan lele kamarka yama diyarsu ciki ita mijin nata ai abun yayi murna ne jininka na Rayuwa a gidanshi akan dan'karamin abunnan ne zasu nakasaka harda cire hakori saikace Wanda yaima Yammata dubu ciki muba matsiyata bane idan bamasan cikin sai a burge idan munaso kuma dandai rai daya jal sai'a dauko masu aiki suyita kulada babyn mukayima wasu banza bare namu tsiyar rashin wayewa kenan ina ranar dakikanci? wlh wlh bazan yarda ba harta iyayan yarinyar sai munyi sha'ria dasu akanka aka farama mata ciki? Koko dole kayi mata har'tayi cikin?......'Mamie mijinta fa Babba ne daga gani shima Dan babban gida ne ina ganin kawai abar case dinnan abari ta haifo mun bby na kawai dukda ban shirya Zama tsoho ba but zanyi hakan a matsayin daukar fansa inbata sunan iyayanta diyar manyan malamai cefa.....'kaci gidanku, daddy yaimasa dakuwa, kana nufin sun bugi banza kenan?

Leemah kuwa kamar mahaukaciya tadawo duk inda ta gilma sai kallonta akeyi wasu najin kyamar ta wasu na tausaya mata chan gabada unguwar sosai ta tsaya a cewarta kada AK ya biyota dakyar tasamu napep dinda ya dauketa yayinda ya kaita gidanta na Isa kaita, fitowa tayi tashiga buga gate din mai'gadin gidan ya bude saida tabashi tsoro..........haaaajjiiya.....kece kuwa? Kodai bake bace? Subhanallah hatsari kikayi abun babu kyan gani wlh, 'banasan surutu karamin munafuki sallami mai a'daidaita kakuma kulle mun gidana......'isowar su meenah neya katse mata maganar ta yayinda suka fito suna salatin ganin ta a haka cikin munafunci ransu yayi fari kar' kamar audiga, "ubanwa yayi miki haka kinga fuskarki kuwa saikace zombie, meenah tafadi tana shirin shafa fuskar leemah, kul kada ki kuskura munafukin hannunki ya sauka a jikina Algunguma butulu maciya Amana wadanda basusan mutunci da Arziki ba matsiyata....'haba dakin hutu mai yayi zafi haka yanzu dai dan Allah bani kudi mu sallami mai abun hawannan, kudinda ubanku yabani ajiya? Tafadi tareda bude idonta dayayi suntum dakyar take iya ganinsu, Kallan mai'gadin sukayi, sallame su Dan Allah sai binmu sukeyi da ido, yana shirin basu kudi leemah ta buga masa tsawa, su kakema aiki koni? Wlh muddin kabiya kudinnan kamar ka yanki takardar barin aikinka a gidannan ne, oooh hajiya kuyima Allah kuyi hakuri har mutane sunfara kallan ku, 'kuma kada kabar kowace yar'iska shigan mun gida tunda gidan bana uban mutum bane, zuciya taja meenah jin Abunda leemah kecewa, ke gidan na uban naki ne mai dattin hula?
'Dukda bana ubana bane amma da sunana aka siyeshi sannan nikeda mallakin shi Baku ba, dama ance tsintacciyar mage bata mage.....aiko
nan suka damko leemah suka hau jibgarta dama a kule suke da ita kafun kace kwabo jama'a ancika akansu layi ya kaure da tikar dambe dakyar aka kwaci leemah a hannun su wacce da ana suma hamsin tabbas da tayishi a yau, yan unguwar ne suka raba dakyar masu napep kuwa cewa sukayi sunyafe kudin domin rabonda suga damben mata Wanda ya kayatar dasu irin wannan tun yarinta, nan yan'unguwa aka shiga zaginsu meenah kassncewar ansan gidan karuwai ne gidan amma ganin manyan masu kudi sun daure musu gindi kowa yakasa magana ganin yau dama tasamu hakan yasa akai musu chaa akai ana tsine musu harda masu dukansu tareda jama mai'gadi kunne duk wacce yabari tashiga gidan saisun gona gidan da mutanan gidan sungaji da zunubin da ake cika musu unguwa dashi, kuka su meenah sukeyi inda suke roko abarsu sushiga koda wayarsu ne su dauka gasuda uban kudi a gidan Ga motoci dankara dankara, kememe aka rakasu da duka sukabar layin kaya duk'ya yage kamar mahaukata takaicin su babu mai waya bare su kira Alhazawan samarin su, kuka sukeyi tareda tsine ma leemah a cewarsu ta shafama rayuwarsu bakin fenti ina suka dosa? Suba dangin iya barena Abba a garin kaduna dama barikice takawo Alkawarin zuwa gidansu leemah sukayi domin warwarema iyayanta halinda take ciki.
'Leemah kuwa tana kwance da alamar wani suman tayi wani makwafcin sune ya tausaya mata inda shida matasa guda biyu suka dauketa zuwa asibiti cikin gaggawa aka amshe ta babu kyan gani yayinda aka gyara mata cikinta da azaba yasashi komawa gefen mahaifa amma bai zube ba, azaba iya azaba tasha inda ta gwammace dama mutuwa tayi nan wadanda suka kawota sukayi wucewarsu.

Sai'chanda yamma AK ya farka inda yayi ramuwar sallolin da ake binshi ba laifi jikin nashi yayi kyau Sannan yaga gata wurin dangi kowa jidashi yakeyi tareda kwantar masa da hankali Aisha kuwa tana gefe daya tarasa sukuni babu ko kunya AK ke kallanta tareda tarin nadamar Abubuwan dayayi mata abaya cikeda Alkawarin neman gafararta ya yarda zaiyi Rayuwa da ita a'haka ya Amince yanzu baya bukatar swt 18 kokuma budurci matarshi yake bukata da soyyar ta duk runtse saiya lallaba abarsa, 'mikewa yayi gaban daddy dasu Ramata daki yacika yayi makil inda babu kunya kai tsaye ya dosa Aisha wacce ke zaune kusada Mamie cikin mamaki yasaki kuka tareda Dora kanshi akan cinyar Aisha nan kallo yakoma kanshi ganin katon Allah na rasgar kuka A'gaban matarshi, 'Mamie na cuceta na cuce kaina hakika Aisha bazata yafemun ba shiyasa nake naiman Alfarmar neman yafitarta a gabanku daddy Dan Allah kasa baki tanajin kunyar ka na cutarda matata wlh banida abunda nakeso samada Aisha wlh Mamie kinfi kowa sanin yanda nayi rainon soyyar Aisha tun kafun inbar kasarnan da soyyar ta natashi nakuma rayu Mamie duk abunda nayi soyyar ta ce sila, Santa ne sanadi da bakin kishin ta ku rokamun matata please Mamie har'dukan Aisha inayi......rufe masa baki tayi tana girgiza masa kai, bataso yayi bakinjini a idon yan'uwanta ga mahaifiyarta a wurin ga wanta garbati bawai hakan na nufin ta yafe masa bane a'a ko kadan saiyaji kwatankwacin azabar da tasha dukda ko'a haka tabarshi tasan ya gasu burinta taga wannan ranan, rananda AK zai tsuguna akan kafarsa yana kuka tareda neman gafararta, zata iya shiryawa dashi sukuma bazasu taba daina mishi kallon ba har'abada darajarshi bazata dawo a idonshi ba, kuka takeyi kamar Ranta zai fita, 'bawani uziri yaya AK bakada uziri baka sona kada kawani fake da soyya ta, Rungumeta yayi tsam a jikinsa tareda Kara fashewa da kuka.....'my Eesha bakisan sirrin dake zuciyata ba kinsan yanda nakeji duk Randa nasaki kuka kuwa........'gyaran murya Alhaji muktar yayi tareda kallansu, 'yanzu dai bare mufita mubar muku Asibitin tunda ka nuna matarka kakeso tayi jinyarka ana mana korada Hali babu ko kunya kuke rungume rungume a gabanmu harda kukan soyya, 'hajiya tashi mu wuce saiya gaya mata sirrin zuciyar tasa baza'ai rashin kunyar nan a gabana ba idan kuma zaki tsaya kallan dramar soyya toh Nina tafi saimun hadu a gida, fita Daddy yayi Ramata tabi bayanshi da garbati cikeda kunya Aisha tayi tayi AK ya saketa rantsewa yayi akan bazai saketa ba sai Mamie tabata hakuri harda rikema Mamie gefen zani inda Aisha keta kukan abun kunyar da AK kemata gaban surukai saikace yara. Mamie kuwa murmushi takeyi ganin sababbin Romeo and Juliet a gabanta.

Mrs Sadik Rumah 💅🏻
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*

*Written by Anty Mamie.*

*Dedicated to Sister husnah*

35

Mikewa takesan yi Amma ya'hanata wai saitace ta yafe mishi inda Mamie cikeda dariya take tayashi ba Aisha hakuri dukda batasan abunda ke tsakanin suba amma ya zatayi? Ya hanata koda motsi ne cewa tayi ta hakura ganin idon Mamie gakuma kunyar yanda ya kankameta koba komai Mamie bata chanchanci musu a wurinta ba hakan yasa Mamie mikewa tareda janye mayafinta yayinda taimusu fada sama sama wucewa tayi sanin daddy na jiranta a waje inda Aisha tafito Rakata nan Mamie ta dinga janta a jiki tareda nuna mata akan takula da Mijinta wannan wata sabuwar damace Allah yabata idan laifi yaimata duk mace mai aji basaita gayama mijinta yamata laifiba zai gane Laifin Sa cikin hikima da dabara ake komai a'haka sukayi sallama inda tabi daddy Wanda yaketa mamakin karfin Hali da rashin kunyar AK saikace ba shine yagama ihun bayasan Aisha oooh yaran yanzu basuda kunya yaro anama gata kakasa ganewa kadan ma kagani, inji dady yafadi yana murmushi. AK kuwa sabuwar sha'gwaba yake xubama Aisha kamar yaron goye ita abunma kunya yake bata gaba daya bata sakan masa fuska inda yakicin Abinci wai itace zata bashi a baki sai shege mata yakeyi ita kuwa cikin rashin sabo sai janyewa takeyi bataso tabashi fuska harga Allah tana matukar kaunar mijinta amma bata shirya Amsar'sa a yanzu ba saiya gane kuransa tukunna nan gaba yasan darajarda takeda shi.

Commissioner of police ne zaune gaban sanata inda Yaketa bashi hakuri tareda Alkawarin daukan mataki cikin gaggawa nan sanata ya Saki bakin Aljihu saboda komai yatafi daidai zai iya yafe komai banda cima iyalinsa fuska, mahuta kuwa azaba yakesha kanshi kamar ya fashe likita ya duba lafiyarsa tareda Dora shi akan magunguna bayi yashiga yadade yana gasa jikinsa bakaramin bugu yaci a hannun AK ba nan yashafa maganin zafi duka jikin nasa inda yaci abincin da mommy ta tasashi a gaba shayi kawai yasha saboda bakin nashi dake mishi azaba magani yasha nan yaita bccin wahala.
Chapter 31 · 0% Book details