← Book details Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 40

Sashe 25

Ustaziya Ko Yar Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iya rikicewa leemah ta rude akan surar AK idan yagama tafiya da tunanin ta sauri sauri takeyi ta amso sakon da aka aiketa tanaso ta Kara gilmawa ta gabanshi tabbas ba'a taba namijin daya wuce da dukkan tunaninta lokaci daya kamar hot guy dinnan Everything about him, his looks, dressing, kamshin turaran shi tasha hurda da manya hadaddun guys but this very one he is very special, 'gaisawa sukayi da Malam inda yaita zubama AK Addu'a nan suka Dan fara fira sama sama inda AK ya nuna Alamar tafiya zaiyi sunanan tsaye aka gama shigarda komai inda yayi daidai da dawowar leemah cikin tafiyarta ta natsuwa wacce takeyi ta musamman tazo gilmawa inda har saida Malam ya lurada kallonta da AK yakeyi inda Malam ya kauda kai tareda gyaran murya, leemah kuwa bata kalle shiba saida tazo gafda su tadaga idanun ta Wanda tagama narkar dasu cikin salo taimasa wani kallo guda daya kwakwara mai wuyar fassara, dauke kanta tayi tareda shiga cikin gida inda AK ya Saki Ajiyar zuciya, 'gskia rabonda yaga mace mai tarin kamala kamar yarinyar nan ya manta, abun Sha'awa gata very Yong and cute, yasan Aisha tafita kyau nesa ba kusa ba, but wannan tafi Aisha Kuruciya, haske Da uwa uba natsuwa da kamun kai, gyaran murya Malam yayi a karona biyu ganin AK ya Lula duniyar tunani, 'cikin kame kame yayinda kunya tadan kama shi ganin kallon da Malam ke masa, yanaso yaima Malam maganan ta amma yanajin kunya matuka ganin tsananin kamarda takeyi da Malam din ya tabbata diyarsa ce, sallama yaima Malam inda kai tsaye ya doshi gida cikeda tunani harga Allah tunda ya taso a duniya baya Sha'awar Auran mata biyu, aso samu mace daya rak ta isheshi rayuwar duniya tohya zaiyi? Aisha tariga tagama dashi koba komai shiba dutse bane bayaso yafada halaka shekara talatin da biyar ba wasa ba dole ce zatasa yayi Aure saboda Martaban da Asalin gidan dakuma yarda dayayi da tarbiyyan Malam liman, wasa wasa cikin kwana biyu AK ya kammala dukkan binciken da zaiyi gameda halayyan halima wacce shaidar data samu da yabo a unguwan nasu saida yabashi mamaki inda yakara jin San abun sosai a Ranshi, kai tsaye ya tunkari Malam liman da maganar batareda bata lokaci ba yace ya yarje masa ya nemeta, hmmmm ina leemah zata shiga a sabuwar duniyar ta saboda farincikin burin rayuwarta zai tabbata Auran mijinda ta Dade tana mafarki saidai kashe ba a lokacin nan taso su hadu ba taso ya hadu da ita a matsayin bazawara wacce tayi Aure ta fito saboda gudun zargi harga Allah irin mijin nan taci burin Rayuwa dashi har abada tareda yaransu bataso tabada kofar dazai mata kallo na daban, but ya zatayi? Gskia bazata wuce damar taba zata iya hakura da komai banda zazzafan handsome Saurayin nan insha Allah zata nema mafita dole asan abun yi tasan tabbas tunda tanada Anty zakwai bazataji kunya ba "Wata shahararriyar mai maganin mata ce tun daga mai'duguri take mata hadi na musamman" Kudi zata baza mata a like ta tsaf akan AK babu abunda bazata iyayi ba kuwa itada shi kuma mutu ka raba insha Allah.

'Soyya sukeyi Mara hayaniya Sam AK bai saba da hakan ba kasancewar baitaba yin wani I love you I need u dawata ba hakan yasa yake ganin abun wani iri kamar shirme har kunya ma yakeji inda leemah takebin duk wani hanyar dazata jawo hankalin shi akanta kira 24/7 text kuwa ba'a magana har mamakin iya soyyar ta yakeyi, koda Ya tunkari su Mamie da Daddy da maganar saida akakai ruwa rana dakyar da sudin goshi daddy ya Amince amma da sharadin babu hannun su a ciki tunda ya dage sai yayi Auran suna ganin hakan kamar cima Aisha fuska zaiyi daga maganar haihuwa saiya zo musu da batun Karin Aure, saida akakai ruwa rana sannan suka amince inda ya tabbatar musu bazai taba tozarta Aisha ba, babu abunda zai Chanza a Auran
Dazai Kara nan hankalin Mamie yadan kwanta, Ankai kudin gaisuwa tareda kayan Sa rana inda ba'a ja bikin ba Wata Daya akasa a cewar AK yanaso ayi da wuri harga Allah Sha'awa na neman yimasa illah inda duk abunda akeyi Aisha batasan wainar da ake toyawa ba.

Kawayan leemah su meenah kuwa koda suka samu labari suka kuma kyalla ido sukaga AK nanfa hankali ya tashi ganin yanda Leemah tayi musu fintinkau a bariki dukda sun rigata shiga Amma tafisu cin riba uwa uba zata Auri babbar harka, tsananin barikin su saida iyayan su suka koresu a gida inda suke zaune darajarta sukeci kasancewar gidan na mahuta, gashi kuma akan idonsu zata Auri handsome young milonia sukuma fa? Sukare a duniya? Inaaaa nanfa hassada mai zafi ya darsu a zuciyar su inda ta rokesu bataso mahuta yasan da Auran da zatayi suka Amsa mata akan ana Tare bazasu gaya masa ba.

Amarya fa sai lakuce lakuce da banke banke da like like takeyi kullum cikin hayakin HQ take saikace yar'bori maganin mata kuwa sha take kamar hauka daga karshe saida yasata zawo saboda shan haukan da takeyi Anty zakwai kuwa ta kuke ta dage tun daga Maiduguri tazo hada leemah inda tai mata masauki a dakinta na isa kaita, kudi sosai tasamu wurin mahuta inda ya sakin mata Aljihu ganin ta chanza test da harta fara sire mishi ta bude dayawa amma yanzu dayaji sabon sinadari nan ya ware Aljihu, Wata kawarta ce Deejah bariki tabata shawara akan zata Rakata asibiti a dinke ta tsaf kamar kwarya yanda ko AK na aiki da Aljanu bazai taba gane ta bude ba, nan kuwa leemah tayi matukar farinciki San AK take kamar hauka nan takara sakinma mahuta jiki ya kwashi gara aikuwa tasamu yanda takeso kudi yabata sosai ba tareda bata lokaci ba suka nufi asibi inda saida aka kankare fatar wurin aka goge, subhanallah Karamar tiyata akai mata a wurin *"hattara mata wani sabon bala'e daya shigo kenan yanzu mace saitaje Asibiti Yammata harda matan Aure akan a dinki su tsaf ko kunya babu ku wage jiki da sunan gyara haka za'ai ta dinke ku saikace buhun masara kai jama'a waiduk kan da'namiji😕 hmm Wata kotayi a banza wlh kozai chanza miki na lokaci kadan ne zaki Kara budewa ke kenan kin dinga zuwa ana miki dinki kenan? Saikace wacce ta haihu? Shi namijin maiya dinke kokuma mai yakeyi domin samun gamsuwar ki? Wlh wani ko magani bazai taba Shaba domin burgeki amma duk kudinki yagama karewa akan maganin mata🤦🏻‍♀karshe su nakasa miki mahaifa GA cancer datai yawa a mata yanzu, subhanallah wata ma yanzu tana samun ciki yana shiga Wata tara zataje asibiti ta kwanta aimata operation tun bata fara nakuda ba wai ita tayi dabara bataso ta bude ita uwar sisi da gayu maisan gamsar da namijin da bazakiyi bajinta ba ko tsoran lafiyar ta batayi, Allah yasa mu dace🙏*

Rabonda Aisha tasa AK a ido an kwana biyu tun tana boyema ganin shi harta daina kwata kwata baya Zama a gida inda kayan abincin su yayi kasa sosai tanaso taimasa magana batasan ta yanda zata fara ba, dukda shike duba komai zaiba yaron aikin shi kudi ya siyo duk abunda ake bukata saidai taga an jera mata su a kitchen, tana zaune sanye da Pakistan Riga da wando, wandon pencil rigar ma batada wani tsawo pink mai kyau tasha ado sai zuba kamshi takeyi kanta daure da karamin rober band, shigowa parlon yayi yana waya da leemah cikin nishadi dukda daga wurinta yake amma ka'eda ne yana barin gunta zata kira shi suyita waya harya kai gida yauma hakan ne, burki yadan ja cikin mamakin ganin Aisha zaune a parlor tana kallo harga Allah rabonda yasata a ido ya manta dukda yaga tadan rame amma kuma takara kyau, 'matar so just a minute I will call you, kashe wayar yayi 'A'a su Ustazai ne Ashe kunyi wuyar gani, yafadi cekeda zolaya inda saida tayi mamakin shi wai yau itace yake zolaya, tunda Allah yasa mun hadu yau wlh Sam nama manta dake a gidan, cut the story short, yauwa next week insha Allah za'a kawo mun matar so, Amarya kuma uwargida ta swt 18 Asalin Ustaziya diyar mutunci diyar malamai da kamala kimtsatiya kamila, hafiza, malama bawai a suna ba nooo, uwa uba uwa ga yarana insha Allah, farincikin AK ina fatan zaki bita sau da kafa saboda gudun shiga matsala a wurina? Biyya dole ce gara ki kwantar da hankalinki zaki karu da ita yauda gobe na tabbata zata saki a hanya kema kidanyi hankali, yafadi yana dariyar keta, kallon shi tayi daga sama har kasa dariya ciki ciki, 'heeeyeeeeah Allah tafadi yayinda ta tafa hannu duka biyun, sannu namiji, Sannu Ango kasha kamshi lallai ka cika namiji Gwarzo ai abunda ya kamata kayi tuntuni kenan Allah yakawo matar so, Allah yakara kauna tsakanin kada matar so, Allah kuma yakara Soyyah, mikewa tayi yayinda takara kallon shi shekeke, daga kai har matarka bakwa gabana gara tun kafun ta karaso kaja mata kunne ka ajiye rikakkiyar Yar'duniya billahillazi ta shiga gonata nan zaku Kara tantance banbancin diyar malamai da diyar mai'shayi yar duniya ubanta zataci ni baka gabana daga kai har ita, akwai lokacin da nake jira yanayi zan cikama rigata iska inbar muku gidan Soyyah kukara soyewa, Allah ya sanya Alkairi ango mai jiran gado, daki ta nufa tana tafiya tana juya mazauni harda yar Karamar waka,

'Ga ango Na Amarya,
"Inaaa Ango Na Amarya,
" Kai sai ango Na Amarya.

yayinda yabita da kallo baki bude samun kanshi yayi dajin takaicin maganar datayi saiyaji Auran yadan sire mishi ko kadan ba haka yaso tayi ba aiya dauka shake shi zatayi tana rokon shi kada yaimata kishiya ta tuba inda zai shuka mata Rashin mutunci sosai Lallai kodan kishin da mata keyi Aisha bata masa kishiya fa yace zaimata muguwar yarinya maiya mata a Rayuwa Wanda takasa nuna jinjirin kishi akan Sa? Wace irin kiyayya ce haka? Ada idan zai tuna ai tana matukar sansa dama so na chanzawa? Ikon Allah, Kodan kukan da mata keyi baiga Alamar tanada niyyar yiba.

Tana shiga daki ta kulle da makulli toshe bakinta tayi nan bakin kofa ta zube tareda fashewa da kuka mai kona zuciya.

*Mrs Saddiq Rumah 💅🏻*
🧕🏼🧕🏼🧕🏼
*Ustaziya ko Yar'duniya?🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀*
Chapter 25 · 0% Book details