← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 26

Sashe 8

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

Vedad ne ya amsa mishi da cewa " Marshal ba Iqbal ba ne , video game ne mu ke yi , kawai sai ya daura bet wai duk wanda ya yi winnig , loser zai ba shi 1000$ kuma ni fa ban da kudi , shi ne da ya yi winnig ya ce sai na ba shi kudin shi ko ya dake ni , shi ne na gudo " ya kai karshen cikin shagwaba

Kamar da ga sama su ka jiyo Muryar Ash ya na fadin " ba na hana ku yin bet ba "
Dum Vedad da Iqbal su ka ji zuciyoyin su sun yi muguwar faduwa , har wasu fitsari Iqbal ya ji sun taho mishi

Ash kuma tsaye ya ke bayan su ya rike hannayan shi a baya , ya na sanye da Trouser Black colour da T-shirt white colour , ya daure wannan darck black curly hair din na shi a baya sai tashin kamshi ya ke yi kamar wanda ya yi wankan turare

Wasu yawu Iqbal ya hadiye har hawaye su ka zubo mishi ya san yau tashi ta karre laifi biyu rana guda ya san yau sai ya yi jinya word room

Wata razananiyar tsawa ce Ash ya daka musu , ba su Vedad ba har shi junior sai da ya sha jinin jikin shi ya na zaro idanu
" Marshal kai min su dakin horo ina zuwa " ya fada ya na juyawa ya nufi part din Nihal
Da kallo su ka raka shi sai da ya shiga sannan Iqbal ya saki wani marayen kuka kamar karamin yaro ya na fadin " wayooo na shiga uku ni Iqbal , Vedad Allah ya isa tsakani na da kai , yanzu za ka janyo min "

Bai gama rufe bakin shi ba junior ya mike tsaye ya fara takawa ya nufi door din fita parlourn ya na fadin " zauna nan ka na kuka ya tardo ku , wlh sai na lahira ya fi ku jin dadi "
Ai bai gama rufe bakin shi ba su ka tashi da gudu su ka bi bayan shi su ka fice parlourn

Bangaran Ash kuma , a hankali ya shiga part din Nihal ya na sallama cen kassa kassa
Kai tsaye bedroom din ta ya wuce , ya na shiga ya isko ta zauna kassa ta jingina a jikin gadon ta kamar wata yarinya ta na kuka ga pics din Aylan duk zube a gaban ta

Bai ce mata komai ba ya karaso gaban ta , ya duka duk ya kwashe pics din nan ya bude box din bedside drawer ya saka su a ciki sannan ya koma geffen Nihal ya zauna a kassa shi ma ya na kallon gaban shi bai ce mata komai ba

A hankali ta fara rage sautin kukan ta , ta na sa hannu ta goge hawayen ta , ta gyara zaman ta , ta yi irin zaman cin tuwo
Sannu sannu har ta daina kukan baki daya Ash bai ce mata komai ba , ko kifta idanu bai yi ba

Sai da su ka share wajen 30 minutes a haka ba wanda ya ce ma wani ufan
A hankali Ash ya bude baki ba tare da ya juyo ba ya ce " mummy , na gaji da ganin ki cikin wannan halin , duk fa abun da ki ke yi ina sane da shi , impossible ne a ce rana guda ta wuce ba ki yi kuka ba ko da cikin dare ne , wani lokaci cikin barcin ki , ki ke yin kukan , Why mummy ? A ganin ki in ya san halin da ki ke ciki zai ji dadi ? Mummy you know , you are my power , you are my weakness and you are my happiness , duk lokacin da na gan ki cikin farin ciki ko ban nuna ba , cikin zuciya ta ina farin ciki , please mummy ki daina cutar da kan ki haka , ke kadai ki ka rage min a duniya don Allah kar ki jawa kan illar da za ta raba ni da ke "

Wani cool murmushi Nihal ta saki ta na daura hannun ta saman kan shi , a hankali ta dan sunkuyo da kan shi ta mana mishi kiss a goshi ta na fadin " shikenan my little , duk yadda ka so haka za a yi amma ina da sharadi "

Slowly ya juyo da kan shi ya daga mata gera allamun miye sharadin ?
Kara fadada murmushin ta ta yi kafin ta ce " ina son ka yi aure ka ga in ina ganin jikoki na zan rage wannan yawwan damuwar "
" ba banza ba Daddy ke cewa ki na yi mishi wayo " Ash ya fada ya kokarin mikewa

Da sauri ta riko hannun shi ta medo shi ya zauna ta na yar dariya ta kai hannu ta ja hancin shi ta ce " shi dai ya ke min wayo , yanzu maganar auren ka ? "
" soon " ya fada a takaice
Hararrar wassa ta yi mishi kafin ta ce " wlh ka fitar da matar aure idan mu ka je Nigeria ko kuma na yi maka irin yadda papi din ku ya yi mana , kawai sai jin na yi ya aura min Daddyn ku " ta kai karshen ta na sakin hannun shi

Mikewa tsaye ya yi ya yi taku biyu gaba sannan ya tsaya ya dan juyo da kan shi ya ce " mummy duk duniyar nan babu matar da ta kai na bude baki na ce ina son ta bayan ke , zancen aure kuma gwara ki bar shi dan ba zan taba yi ba " ya na gama fadar hakan ya sa kai ya fice

Da kallo ta raka shi har sai da ya fita sannan ta yi yar karamar dariya ta ce " yaro man kaza, ba ka san wuta ba sai ka taka , ni na ke da iko da kai ba kai je da iko da ni ba , Allah ya kai mu Nigeria wlh da matar ka za ka dawo ko ka ki , ko ka so zamu gani " ta na gama fadar haka ta sake bushewa da wata shegiyar dariya irin ta mugun ta

▪ASH 🔥

Bayan ya baro part din Nihal kai tsaye part din shi ya koma , allamun ya manta da Su Vedad
Bayan ya shiga bedroom din shi a parlourn ya zauna saman sofa three seaters ya fido wayar shi da ga cikin aljihu ya fara latsawa
Bai fi five minutes ba da zama ya , Felix ya shigo parlourn ya na dauke da wasu bucket biyu na ruwa wanda a kila za su kai 30 liter na ruwa

Gaban shi Felix ya ajiye bucket din nan sannan ya sara mishi ya fice dakin , dai'dai lokacin da Junior ka shigo dakin Vedad da Iqbal na biye da bayan shi
Cikin dakin Junior ya karaso ya zauna saman sofa geffen Ash ya ce ma su Vedad su karaso ciki
Wasu yawu su ka hadiye kafin su ka karaso gaban shi su yi kneel down

Ba tare da ya dago kan shi ba Ash ya ce musu su shanye ruwan da ke cikin bucket din nan
Ba karamin zaro idanu Vedad da Iqbal su ka yi ba su na kallon bucket din gaban Ash , ai ko cikin kwana guda ba su iya shanye ruwan nan
" idan har ku ka bari na sake maimaita abun da na ce " Ash ya fada ba tare da ya dago kan shi ba

Nan take kuka ya kubce wa Vedad kamar baby har da shagwaba ya na fadin " Big bro don Allah ka yi hakuri wlh ba zan sake ba , duk Iqbal ne shi ya ce mu yi bet din ai , ni ban da kudi wlh " ya kai karshen ya na kara sautin kukan shi

Ya na gama rufe baki shi ma Iqbal ya shiga yin kuka ya na fadin " I'm sorry big bro ba zan sake ba "

Slowly Ash ya dago kai ya zuba musu wadanan sexy blue eyes din na shi , sai kuka su ke yi , Vedad har da majina ya na hadiyar zuciya
Shi kuma junior sai kumshe dariya ya ke , ya samu mugun ta
( munafiki ko shi ne a ka ce ya shanye fiye da liter goma ta ruwa lokaci guda ba zai iya ba , har da yi musu dariya 😑😑😑😑 )

Ajiye wayar shi gefe ya yi kafin ya mika wa Vedad hannu a kan ya zo
Da sauri Vedad ya matso gaban shi , ya na ci gaba da kukan shi
Hannu Ash ya kai ya kamo kunnen shi ya murde ya na fadin " nan gaba ko game za ku yi kar ku daura bet , na san ba yau ba ku ka fara , to yau shi ne na karshe in na sake kama ku da irin wannan laifin " ya na gama fadar haka ya saki kunnen Vedad , sannan ya kali Junior

Gyada mishi kai Junior ya yi kafin ya mike ya nufi table din da ke kassan makekiyar Tv plasma din parlourn ya dauko kwallin handkerchief ya dawo ya zauna saman sofar ya mikawa Ash

Hannu ya sa ya zaro handkerchief biyu sannan ya shiga gogewa Vedad hawayen shi , sai da ya goge mishi sannan ya ce ya tashi ya je ya sha fruits din shi ,
Ai ko da sauri Vedad ya tashi ya fice parlourn
Ya na fita Ash ya mike ya nufi bedroom din shi ya na ce ma Iqbal ya biyo shi
Ba musu Iqbal ya tashi ya bi bayan shi a hankali kamar wanda a ka yi wa dole
( ko da ya ke dolen ce a ka yi mishi 🤣🤣🤣 )
Chapter 8 · 0% Book details