← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yar karamar dariya ta yi kafin ta kai dan bakin ta ta daura lips din ta saman na shi ta yi mishi kiss
Ta na shirin janye bakin ta ya cabko lips din ta na kassa ya ci gaba da kissing cikin kwarewa , nan take duk wata sigar jikin shi ta mike , ya zagayo da dayan hannun na shi a baya ta ya na shafawa a hankali
Mayar mishi da martani ta shiga yi ita ma , dama ta jima ta na sha'awar shi amma kullum ya ki ba ta dama , yau dai ta samu abun da ta ke so

A hankali ta kai hannu ta riko zip din jacket din shi ta fara yi kassa da shi har ta fida shi , sannan ya sa hannu ta cikin t-shirt din shi , maimakon ta yi sama kawai sai ta yi kassa ta na neman sa hannun ta cikin trouser din shi

Ai ko cak ya damko hannun ta ya na ware idanun shi da su ka yi jazir , sai cikin na ta
Slowly ya zame bakin shi da ga cikin na ta , cikin wata zazzakar murya ya ce mata " me ki ke shirin yi ? "
A hankali ta girgiza mishi kai ta bude ta ce " I'm sorry , ni ma ban san na yi ba "
Bai ce mata komai ya janye hannun ta , ya daura shi saman cinyar sa , sannan ya sa hannu ya Meda zip din jacket din shi , ya tada motar shi su ka bar wajen

Marairaice fuska ta yi kamar za ta kuka ta ce " Baby , i'm sorry "
Slowly ya juyo ya kale ta kafin ya saki wani cool murmushi ya riko hannun ta , ya kai shi saitin bakin shi ya yi mata kiss sannan ya ce " It's okay , za ki je Funfair ? "
Da sauri ta gyada mishi kai ta na murmushi , shi ma murmushi ya yi mata da ga haka ba wanda ya sake cewa komai har sai da su ka isa wani makeken park , ba sai na fada muku na wanene ba

A haka su ka shiga cikin park din nan , su na rike da hannun juna gwanin burgewa , park din ya na da mugun girma , sai misalin karfe 6 su ka baro shi , a hakan ma ba su hau duk carousel din park din

Kai tsaye apartments din ta ya meda ta , a wannan karan sai da ya sauko ya raka ta har apartments din ta , su ka yi sallama ta masoya sannan ya baro building din ya koma gida kai tsaye

Ya na komawa a ka fara kiran Sallar magriba , kai tsaye part din shi ya wuce dan babu kowa a parlourn , ya na shiga ya wuce toilet ya yi wanka ya fito ya shirya sannan ya yi sallat

▪AFTER SOME HOURS

▪ASH 🔥

Zaune ya ke saman bed din shi da ga shi sai short da singlet , ya rike da laptop din shi ya na faman aiki , allamun tun bayan fitar Iqbal bai je ko ina ba

Ya na a haka Vedad ya shigo Dakin ya na sallama , ya na sanye da kayan barcin shi white color sai tashin kamshi ya ke yi , ya na rungume da wani pillow a kirjin shi , kai tsaye bed din Ash ya nufa ya Haye ya yi rub da ciki

Sarai Ash ya lura da shi amma bai ce mishi komai ba
Sai da ya Kamala aikin shi sannan ya ajiye laptop din saman bedside drawer , ya kali Vedad ya daura hannun shi saman kan shi ya shiga shafa lalawsan gashin kan shi ya na fadin " My angel , what's wrong ? "

" Let me , ni ba na son yi maka magana yau " ya fada ba tare da ya dago kan shi ba
Ci gaba da shafa kan shi Ash ya yi ya na fadin " Why ? Laifin me kuma na yi ? "
Bai gama rufe bakin shi ba rufe bakin shi ba Iqbal ya shigo bedroom din ya na sallama ya nufi Sofar da ke fuskantar bed din ya zauna ya na kallon su Vedad

Ya na zama ya saki wata yar karamar dariya ya ce " Cutie pie , yau yan shagwabar ne ke sama ? " ya fada cike da tsokana

Da sauri Vedad ya dago ya mike zaune ya tila wa Iqbal pillown hannun shi ya na fadin " Stop calling me Cutie pie "
Da sauri Iqbal ya cabko pillown ya na dariya

" ya isa in wassan ku , ku ke son yi , ku tashi ku fice min daki " Ash ya fada cikin tsare gida
Turo dan bakin nan na shi Vedad ya yi cike da shagwaba ya ce " ni babu inda zan je a nan zan kwana ma " ya kai karshen ya na komawa geffen Ash ya zauna ya kontar da kan shi saman shoulder din Ash

Shi dai Iqbal dan karamin murmushi ya yi kafin ya jingina bayan shi a jikin sofar ya daga kai sama ya lumshe idanun shi ya tafi duniyar tunanin shi

Ash na ganin hakan ya kai hannu ya dauki laptop din shi zai ci gaba da aikin shi
Vedad na ganin wallpaper din shi ya kai hannu ya kwace mishi laptop din ya na ci gaba da kallon wallpaper din ya saki wani kyawatencen murmushi
" My angel are you okay ? " Ash ya fada dan ya ji kamar Vedad ya yi sanyi

Girgiza mishi kai Vedad ya yi allamun ba komai ya na kashe laptop din ya mikawa Ash kayan shi
Karba ya yi ya meda ta saman bedside drawer sannan ya kai hannayan shi ya talabo face din Vedad nan ya ga hawayen da ke konce cikin idanun shi

Cikin konciyar hankali Ash ya ce mishi " My angel , why did you cry ? You know i don't like see you crying "
A hankali Vedad ya sunkuyar da kan shi ya fada jikin Ash ya rungume shi da kyau murya kassa kassa kamar me kuka ya ce " Big bro , wlh ina kewar Daddy over , kullum da dadare sai na jira shi , ya zo ya yi min adu'ar barci , amma kullum ba ya zowa har barci ya dauke ni "

" it's enough now , kar ka yi min kuka , ai ina nan , kuma Mummy ta na nan , ga Ummi and your best friend Iqbal , we are all here with you "

" i know but ....... "
Cikin nitsuwa Ash ya katse shi da cewa " But what , ko duk ba mu ishe ka ba ? "
Nan take kuka ya kubce wa Vedad , cikin kukan ya ke fadin " but i want to see my Daddy , I missed him "

Murya cike da rauni Ash ya ce mishi " please My angel stop crying , ni ma ina kewar Daddy over , kullum cikin yi mishi adu'a na ke , kai ma adu'a ya kamata ka dinga yi mishi duk lokacin da ka tuno da shi , ba kuka ba "

Slowly Vedad ya dago da ga jikin Ash ya na fadin " Da gaske ka na kewar Daddy ? " ya fada ya kallon Ash cikin ido

Gyada mishi kai Ash ya yi kafin ya kai hannayan shi ya fara goge wa Vedad hawayen shi ya na fadin " ina kewar shi mana , kawai dai na san adu'a ta ita ya fi bukata a yanzu , shi ya sa na shanye abun da ke cikin zuciya ta , ina yi mishi adu'a duk lokacin da na yi sallat "

Dan karamin murmushi Vedad ya yi ya na fadin " Ni ma kullum in na yi sallat sai na yi mishi Adu'a "

" Haka ya kamata ka dinga yi duk lokacin da ka tuno da shi my Angel " ya fada ya na kai hannu ya shafi geffen fuskar Vedad
Daga kan shi sama Vedad ya yi ya na fadin " Daddy ! You know i really missed you everyday ,Allah ya jikan kan , ya yi maka rahama , Allah ya sa ka huta , kai da dukanin al'umar musulmi da su ka riga mu gidan gaskia , ina rokon Allah ya sa wannan adu'ar ta tarda ka duk inda ka ke , I love you my Superman " ya kai karshen ya na sakin wani kyawatencen murmushi

A hankali Ash ya sa hannu ya janyo shi jikin shi ya rungume ya na fadin " na gwada maka wani abu ? "

Da sauri Vedad ya dago da ga jikin Ash ya na fadin eh
A hankali Ash ya koma ya jingina a jikin forehead din bed din shi sannan ya sa hannu ya dauki laptop din shi ya nuna wa Vedad geffen shi sannan ya shiga latsa laptop din
Da sauri Vedad ya dawo geffen shi ya zauna ya na murmushi

Ya na zama Ash ya mika mishi laptop din dai'dai wata video ta kama
Wani kyawatencen murmushi Vedad ya saki lokacin da idanun shi su ka sauka kan abun da ke cikin videon

Ba komai ba ne face Aylan shi da Vedad tun ya na karami ba zai wuce 3 years ba haka
Su na zaune saman Lillo cikin Garden din nan na Gidan Aylan na farko
Vedad sai tura fruits ya ke yi a baki Aylan na kallon shi ya na murmushi
Su na a haka Kawai su ka jiyo Muryar Nihal ta na kwallawa Vedad kira
Da sauri Aylan ya dauki Vedad ya bude jacket din shi ya saka shi a ciki sannan ya meda zip din kassa kassa ya ce " My angel yi shiru kar mummy ta jiyo ka , ta tafi da kai "
Yar karamar dariya Vedad ya yi ya na cikin jacket din Aylan
Chapter 10 · 0% Book details