← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 26

Sashe 11

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dai'dai lokacin da Nihal ta karaso wajen lillon ta yi sallama sannan ta ce " Abban Ummi ina Vedad ya yi , tun safe na ke neman shi yaron na tsere ya buya "

Cikin ko in kula Aylan ya ce " Duba wajen Khaled may be Ya na cen shi da Iqbal "
Tsuke fuska Nihal ta yi ta ce " Abban Ummi minene ke motsi cikin jacket din ka "
Yar karamar dariya Ummi da ke rike da wayar Aylan ta yi ta na toshe bakin ta

Hararrar wassa Aylan ya yi mata kafin ya ce " Baby na ne , you don't know i'm Pregnant "
Wata muguwar harara Nihal ta wurga ma Aylan , da sauri ya sa hannu ya zuge zip din jacket din shi

Wani cool murmushi ta saki kafin ta koma geffen shi ta zauna ta daura hannun ta saman face din Vedad , har ya yi barci a jikin Aylan " Duba duk ya bata maka kaya " ta fada cikin sanyi

Rungume Vedad tsam Aylan ya yi ya na fadin " ba komai" ya kai karshen ya na kai dan bakin shi ya sumbaci forehead din Vedad da ga haka videon ta kai end

Yar karamar dariya Vedad ya yi ya dago kai ya kali Ash ya na mika mishi laptop din shi ya ce " big bro ina ka samo wannan videon ? "

Ajiye laptop din saman bedside drawer Ash ya yi ya na fadin " a lokacin Ummi ta na rike da wayar Daddy ta na game , Ta cikin camera din na ga abun da ku ke yi , ai ni na fadawa mummy ku na garden "

" you , you are wicked big bro " Vedad ya fada ya na kontawa ya rungume kugun Ash dan barci ya ke ji ya lumshe idanun shi

Shi dai Ash bai ce mishi komai ba , sai a lokacin ya tuno da Iqbal da ke zaune saman sofa , duk abun nan da su ka yi bai ce uffan ba allamun ya yi barci ko akasin haka

A hankali Ash ya kai hannu ya dauki pillow ya tila wa Iqbal
A razane Iqbal ya dawo cikin hayacin shi
Da sauri Ash ya ce mishi " Shut up !!!!!!!! Tunanin mi ka ke yi haka ? "
Dan karamin tsaki Iqbal ya ja ya na kauda kai gefe ya na turo dan bakin shi ya ce " ni ba tunanin da na ke "
" oya come here "

Ba musu ya taso ya dawo dayan geffen shi ya zauna ya na ci gaba da turo dan bakin nan na shi
" Fada min gaskia , ba dai wani abu ku ka yi kai da yarinyar nan ba " Ash ya tambaye shi , dan ya lura yadda sigar jikin shi duk ta ke mike

Cikin ko in kula Iqbal ya ce mishi " ni fa ba abun da na yi mata , ai ita ta fara yi min kiss "
" Kai kuma me ka yi mata ? "
" Kiss kadai na yi mata , ni ban ma san ya a ka yi ba kawai sai jin hannun ta na yi , ta na kokarin saka shi cikin trouser di na "
" ka bari ta saka ? "
Da sauri ya girgiza mishi kai ya na fadin " no , ban bari ba "

Okay kawai Ash ya ce kafin ya gyara konciyar shi , ya na rungume da Vedad
Shi ma Iqbal konta wa ya yi su ka saka Ash a tsakiya
" ka san wani abu ? " Iqbal ya fada ya na kallon Ash da ya lumshe idanun shi
Girgiza mishi kai ya yi ba tare da ya bude idanun shi ba

A hankali Iqbal ya matso ya kai bakin shi saitin kunen Ash kassa kassa ya rada mishi " Amma fa big bro , na ji dadin kiss din nan over "

Cikin ko in kula Ash ya ce mishi " Okay bari in mu ka dawo da ga Nigeria , Sai ka yi abun da ya fi hakan ba wanda zai hana ka , but ka ce min Duk familyn ta a New York su ke zaune ko ? "

" eh a NEW York su ke "
" Tun yaushe ku ke tare da ita ? "
" this year , wannan shekarar ce ta shigo university din mu , So za mu kai six to seven months haka "
A hankali Ash ya gyada kan shi kafin ya ce " Kai ka ce ka na son ta "

Yar karamar dariya Iqbal ya yi kafin ya ce " kai da ka san halin brother din ka , ita ta ce ta na so na , amma na ki yarda , Sai da ta matsa har kokarin kashe kan ta ta yi , sannan na hakura na yarda da ga baya na ji na kamu da son ta ni ma "

Shiru Ash ya yi bai ce mishi komai ba " Tabass akwai wani abu a kassa " ya fada cikin zuciyar shi saboda Binciken da ya yi da safe bai samo komai ba a kan ta , ko university din su Iqbal da ya duba register din First year bai ga mai sunan Maya ba , hakan na nufin akwai wani abu a kassa may be aiko ta a ka yi dan cutar da familyn shi ? Ko ma minene ya dauki alwashin sai ya gano shi , dan ba zai bari wani abu ya sami brother din shi ba
Da wannan tunanin har barci ya dauke shi , dan shi ma Iqbal ya jima da yin barcin shi

* NIGER ( ZINDER STATE )

* KAUYEN NAWACH KALÉ

▪MISALIN KARFE 12 NA DARE

* HAYAT 💦

A hankali ta sa kafa ta fito da ga cikin Dakin ta , ta na sanye da wata Gown duk ta kaude ta tsufa , ta na sanye da wannan hijabin ta na safe dama su biyu ne ta mallaka
Hannu ta , ta na rike da wani kumshi na kaya cikin wani zane na atanfa

Garin duk duhu ne , babu ko irin wanan tochilar a tsakiyar gidan , ba ka jin motsin komai sai kukan awaki da Shanu
Amma a haka ta sa kafa ta fito dakin ta na tafiya cikin sanda kamar barawo , a haka ta nufi hanyar fita gidan , sai kale kale ta ke yi kar a je wani ya gan ta

Har ta kai bakin kofar gidan ta jiyo Muryar inna ta na fadin " Waye a nan ? " ta fada ta na haska Hayat da torch din hannun ta
Dum Hayat ta ji gaban ta ya fadi da sauri ta juyo ta kali inna , idanun ta na kawo ruwa ta shiga girgiza mata kai

Ita ma inna tsaya wa ta yi ta na kare wa Hayat kallo ta kassa cewa komai
Kamar da ga sama su ka jiyo Muryar wani mutun cikin dakin da inna ke tsaye bakin kofar shi ya na fadin " Barira wanene wai ? "

Da sauri inna ta ce mishi " ba kowa Auwalu ne ya fito shan ruwa " ta na gama fadar haka ta juya ta shiga cikin dakin ba tare da ta ce wa Hayat komai ba

Hayat na ganin ta shiga Dakin ta , ta sauke nanauyar ajiyar zuciya , ta juya da gudu ta fice gidan
Ta na fitowa gidan ta daga rigar ta sama ta fara Gudu da wadanan kananan kafafun na ta , gudu ta ke cikin fitar hayaci , ko gaban ta ba ta gani , ga kuma garin duk duhu ne

A haka kawai ta ji ta yi tuntunbe da wani dutse ta yi wata muguwar faduwa kassa dibb , amma ba ta tsaya duba in ta ji ciwo ko ba ta ji ciwo , ta tashi ta ci gaba da gudun ta , ita dai a yau ta kudurta sai ta bar kauyen nan , dan ba za ta iya auren rabeh ba , ta grimace ta mutu a kan ta aure shi

Ta dauki wajen good 30 minutes ta na wannan gudun na fitar hayaci kafin ta fita kauyen ba ki daya , ba abun da ta ke gani sai ita ce , da ciyayi
Duk da ta yi nisa sosai da kauyen , ba ta tsaya da gudun ta ba , babu alamun gajiya sam a tattare da ita

Sannu sannu har ta share wajen good 1 hour ta na wannan gudun babu tsayawa , haka har ta wuce wani kasurgumin daji sannan ta fara Hango wani Haske a cen nesa da ita , allamun ta fara shigowa gari

Ta na ganin hasken nan ta tsaya da gudun ta , ta na kallon gaban ta , ta saki wani kyawatencen murmushi ta na meda nunfashi

Sai da nunfashin ta ya dawo dai'dai sannan ta ci gaba da gudun ta , ta karaso cikin garin Zinder
Hanyar da ta biyo babu kowa sai lamps din da su ka haska wajen , ba ta dauki wani lokaci mai tsawo ba ta karaso Gidan Bus , dai'dai lokacin da motocin ke shirin tashi , a na ta saka kayan passengers a ciki

Da sauri ta karaso wajen daya da ga cikin bus din geffen driver ta tsaya ta na fadin " Don Allah motar nan ina ta yi "
Kare mata kallo da kyau driver din ya yi kafin ya ce " Nigeria ta yi , sai dai ta cika "

Nan take wani kuka ya kubce mata , ita ba ta ma san ina ne Nigeria ba amma haka ta shiga rokon shi da Allah ta na fadin " Don Allah dan uwa ka yi hakuri ka saman min waje , wlh yan uwa na duk su na cen , mahaifi na ne ya rasu ina son na koma gida , don Allah , don son annabi , ka taimaka min "

" shikenan shikenan ya isa haka , yanzu in ki isa Kano akwai wanda zai tarbe ki " ya fada dan har ga Allah ta ba shi tausayi
Chapter 11 · 0% Book details