← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 26

Sashe 4

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan karamin murmushi Rayan ya yi kafin ya ce " Junior , ba za ka gane ba ne , ina jin yaunin kiran sunan nan kai tsaye , me ya sa ba ka iya fahimta ta ne ? "

Daukar spoon junior ya yi ya fara cin abincin shi kafin ya dauki wayar shi ya ci gaba da latsawa
" junior ! " Rayan ya fada a sanyaye

Ko kallon shi junior bai yi ba , sai ma ci gaba da cin abincin shi da ya yi
Shiru Rayan ya yi ya na ci gaba da junior
Sai da ya dauki wajen good three minutes a haka kafin Rayan ya ce " junior , na san abun da ke damun ka , ni ma......... "

Da sauri junior ya katse shi da cewa " stop Dad please , ka daina cewa ka san abun da ke damu , ba abun da ka sani a kai na , idan na tambaye ka what is my favorite colour , na san ba za ka iya ba ni amsa ba , tun bayan Rasuwar Momy duk ka daina kula ni "

" junior ! Ka fi kowa sanin irin son da na ke yi maka you are my only son "

" where is this love Dad ? Kullum sai ka ce ka na so na amma duk son nan da ka ke cewa , cousins din na ka ke nuna wa , duk soyayyar da ya kamata a ce ni na same ta da ga gare ka su ka ke nuna wa " junior ya fada da dan karfi

Riko hannun shi Rayan ya yi ya na fadin " please my junior calm down....... "

Kwace hannun shi junior ya yi ya na fadin " Stop that , it's late now , tun baya ya kamata a ce ka gyara amma sai ka yi watsi da abun "

" Junior , don't forget i'm your Dad , duk duniyar nan babu wanda zai cewa ya fi ni son ka , na san har yanzu ka na radadin mutuwar momynka , ni ma ina radadin mutuwar matata , kai kadai ne ka rage min da ga ita , don't say you hate me please wlh ba zan iya jurewa ba " Rayan ya fada idanun shi na kawo ruwa

Kallon wutsiyar ido junior ya yi mishi kafin ya mike tsaye ya dauki wayar shi ya fice dining room din
" Junior, where are you going ? " Rayan ya fada shi ma ya na mikewa tsaye

Bai amsa mishi tambayar shi ba , ya nufi stair ya Haye da sauri ya bar Rayan shi kadai a dining room

Komawa Rayan ya yi ya zauna
Kamar da ga sama ya jiyo Muryar Ash ya na fadin " yaran yanzu sai a hankali ko his excellency ? "

Da sauri Rayan ya dago kan shi , ya na tsaye gaban shi ya saka hannayan shi a aljihu
Murmushin karfin hali Rayan ya yi kafin ya ce " Ash , junior fa ya girme ka , shi ne za ka ce mishi yaro "

A hankali Ash ya fara takowa ya karaso cikin dining room din ya ja chair din da ke geffen Rayan ya zauna , ya jingina bayan shi a jikin chair din ba tare da ya ciro hannayan shi da ga cikin Aljihun shi ba ya ce " uncle ni da Junior sati biyu ne kawai ke tsakanin mu , duka 29 years gare mu , so ka daina cewa ya girme ni , na ga shi ma cewa ya ke ya girme ni "

Hararrar shi Rayan ya yi kafin ya ce " to kariya ya yi ne ? Ko ba komai ya riga ka shigowa duniya "
Kauda kan shi gefe Ash ya yi ba tare da ya ce komai ba
Yar karamar dariya Rayan ya yi kafin ya ce " to Shikenan , General ya Batun auren ku kuma , kun ga Mimi da Ayna sun yi auren su har da babys din su me kuke jira kai da junior da Ummi ko so ku ke sai kun tsufa sannan "

Slowly Ash ya dawo da kallon shi kan Rayan " aure sai dai Ummi da junior su yi , amma ni dai babu gurbin mace a cikin rayuwa ta "

Dariya sosai Rayan ya yi har sai da wasu hawaye su ka zubo mishi
Sai da ya Kamala dariyar shi sannan ya ce mishi " kar ka damu , haka shi ma Dad din ka ya ke fada , amma dubi yadda soyayya ta kama shi , har mutuwa zai iya yi a kan sister , saboda ita ya daina zuwa headquater sai dai ya bar min aiki shi ya dawo ya zauna tare da ita , ko Daddy da ya haifeshi bai taba ganin murmushin daddyn ku ba sai sister , saboda irin son da ya ke mata har zubewa ya yi saman guyiwowin shi ya na ba ta hakuri kamar yadda a ke rarrashin baby , yanzu a tunanin ka inda wani a baya ne wani ya fada mishi zai yi duk wannan abun ka na ganin zai yarda "

" Uncle , Daddy ka ce ba ni ba , babu macen da ta isa na zube saman guyiwowi na gaban ta , wai da sunnan hakuri , uncle har yanzu ba a yi ta ba " ya kai karshen ya mike wa tsaye ya fara takawa ya fice dining room din

Da kallo Rayan ya raka shi har sai da ya fice dining room din sannan ya bushe da dariya ya na fadin " za ka shigo hannu kai ma " da ga haka ya ci gaba da cin abincin shi har ya ma manta da maganar da su ka yi shi da junior

Bangaran Ash kuma kai tsaye stair ya Haye , wajen kamar dan balcony ne , an saka mishi wasu sofas farare kal kamar parlourn
Part bakwai ne a saman , na farko shi ne na Rayan , na biyu kuma na Ummi , sannan na Iqbal , sai na Vedad , da na Junior shi kuma Ash na shi ya na karshe kuma duk cikin part din na shi ya fi girma

Kai tsaye part din shi ya nufa , har ya wuce part din junior ya tsaya cak
Slowly ya juyo ya nufi door din , ya daura yatsar shi saman finger print , saboda duk kofofin da finger print su ke buduwa
Ya na daura wa kofar ta yi wata yar karamar kara sannan ta bude kan ta

A hankali ya shiga part din , parlourn ya na da dan girman , komai na cikin shi navy blue ne wajen ya tsaru gaskia
Ya na shigowa parlourn ya ga junior zaune saman doguwar sofa ya na rike da maltina a hannu daya hannun kuma ya na rike da taba

Karasowa cikin dakin Ash ya yi sannan ya zauna saman sofa geffen Junior ya zuba mishi wadanan sexy blue eyes din shi ba tare da ya ce komai ba

Juyowa Junior ya yi ya kali Ash ya ce " what are you doing here ?"

Shiru Ash ya yi bai ce mishi komai ba sai da ya dauki wajen good ten minutes kafin ya ce " what are you doing ?"

Dan murmushi Junior ya yi ya kai tabar shi a baki ya busa kafin ya ce " smoking " ya kai karshen ya na kai maltinar shi a baki ya sha kadan

Slowly Ash ya kai hannu ya karbi Tabar hannun junior ya daura saman table
Cike da nitsuwa ya ce " junior you are a soldier , na zata ka daina bushe bushen ga "

Dan karamin tsaki junior ya yi ya na kai maltinar shi a baki ya sha ya na kauda kai gefe
" please Ash let me , wlh ba na jin dadin zuciya ta ne , shi kadai ya ke rage min radadin da na ke ji "

Mikewa tsaye Ash ya yi ya na fadin " Junior , na san tun da mu ka taso ba wani sake maka fuska na ke yi ba , but don't forget ni dan uwan ka ne , duk wani abu da ke damun ka za ka iya fadamin , ba ka tsaya ka na cutar da kan ka ba " ya na gama fadar haka ya juya ya fara takawa cike da nitsuwa ya fice part din

Da kallo Junior ya raka shi har sai da ya fice sannan ya sa hannu ya ciro wata yar remote da ga cikin aljihun shi ya danna wani button , nan take door din ta koma ta rufe kan ta

Bangaran Ash kuma ya na fita ya koma kai tsaye part din shi , kai tsaye bedroom din shi ya wuce
Bedroom din ya na da girma sosai , ga shi ta hadu kamar ba a duniya ta ke ba , komai na cikin ta white colour ne har curtain din
Wata yar door ta glass ya nufa , ya na isa wajen ta bude kan ta ya shiga wani katafaren dressing room
Cikin dressing room din a geffen dama akwai wata door ita ma ta glass
Kai tsaye wajen door din ya nufa yanzu ma ya na tsayuwa gaban ta ta bude kan ta ya daga kafa slowly ya shiga

* WASHE GARI 🌤🌤🌤🌤🌤

* NIGER ( ZINDER STATE )

* KAUYEN NAWACH KALÉ
Chapter 4 · 0% Book details