← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 26

Sashe 26

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 3 min read

Misalin karfe 8 cib ta farka da ga barcin ta , ko da ta farka ta shiga ta yi wanka , ta meda gown din ta , da hijab din ta fari sannan ta fito dakin ko lotion ba ta shafa ba

ta na shigowa parlourn ta ji gaban ta ya yi wata mumunar faduwa
amma haka ta ci gaba da takowa ta karaso ta na sallama

a tare Hajiyah da wannan mutun su ka amsa mata sallamar ta
sai washe baki ya ki cikin zuciyar shi ya na fadin " an ya zan iya kai musu yarinyar nan haka kawai , ya kamata na dan taba gaskiya "

ya yi nisa cikin tunanin shi ya jiyo Muryar Hajiyah ta na fadin " Ta na gaishe ka ba ka ji ba ? "

a razane ya dawo cikin hayacin shi ya na fadin " eh eh , yawwa sannun ki yarinya "
dan sunkuyar da kai Hayat ta yi cikin zuciyar kuma ta na tsara shirin da ta yi musu

a haka Hajiyah ta ce mata " Hayat wannan abokin aiki na ne , yau din nan ya dawo da ga Dubaï "

a hankali Hayat ta dago kai ta mishi kallon kassan ido murya cen kassa kassa ta ce mishi " sannu da zuwa , "

wani cool murmushi ya saki ya na gyada kan shi kafin ya kali Hajiyah ya ce " Ina kuma ki ka samu kyakyawar yarinya haka , a sani na dai yaron ki guda "

yar karamar dariya Hajiyah ta yi kafin ta ce " ɗiyar din wata abokiya ta ce wlh "

a dubu dari Hayat ta dago kai ta na kallon Hajiyah ta na zaro idanu cikin zuciyar ta ta na fadin " ku ji shegiyar mata yaushe na zama ɗiyar abokiyar ki kuma "

ta na a haka ta jiyo Muryar mutumin nan ya na fadin " oh ki ce hutu a ka zo miki , ya yi kyau gaskia , sannu fa daughter "

a hankali Hayat ta meda kan ta ta sunkuyar cikin zuciyar ta kuma ta na fadin " munafiki kai ka san minene Dauda din da ka ke cewa "

ganin ba ta ce komai ba ya sa mutuman nan cewa " Hajiyah yarinyar ta ki fa akwai ta da kunya , shikenan , yau dai ina da aiki sosai wlh da ga nan ma Abuja na yi , amma in sha Allah jibi zan dawo mu tafi shan ice cream "

kamar Hajiyah ba ta san da maganar ba kawai sai ta ce " kar ka wahalar da kan ka , na san aikin ka ba ka samun isashen lokacin ka , dan haka mun yahe maka "

" no kar ki damu ai ba wata matsala ba ce , jibi ina dawowa da ga Abuja sai mu tafi har shopping ma sai mu wuce ko ba haka ba daughter na " ya kai karshen ya na kallon face din Hayat
Chapter 26 · 0% Book details