← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 26

Sashe 13

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya na jin ta yi shiru ya bude kofar ya dan soko kai ya leko ya ga ko ta nan
Sai ya ga gida fayam babu kowa , ajiyar zuciya ya sauke har da lumshe idanun shi ya na fadin " Allah na gode maka , Allah na gode maka , gwara na zo na bar kauyen nan , tun kafin Rabeh bai isko ni ba , na san ta shi haukar ta fi ta Barira musaman a kan kudi " ya fada shi kadai kamar dani mahaukaci ya shiga tattare kayan shi da sauri sauri ya hada cikin dan buhu ya fice gidan da sauri

Bangaran Barira kuma sai da ta yi nisa da gidan sannan ta tsaya ta bushe da wata shegiyar dariya , har da dafe ciki kamar mahaukaciya har da hawaye bibiyu
Sai da ta yi dariyar ta iya son ran ta sannan ta yi shiru ta fara takawa a hankali cike da nitsuwa ta nufi hanyar gidan su ta na fadin " Haiiii barka Barira , yau tsawon shekara goma sha biyu Allah ya raba ki da Jarabbabe , shege matsiyaci kawai " ta na kai karshen ta sake bushewa da dariya a haka har ta isa gidan su ta na dariya kamar mahaukaciya

Ita dama ta jima ta na son ta rabu da Issa amma ba hali , a daren jiya da ta ga Hayat na neman guduwa wani tunanin ya fado mata a rai , me zai hana ta yi anfani da wannan damar ta kirkiro wata masifar da zai sa Issa ya sake ta , shi ya sa ba ta yi kokarin tsayar da Hayat ba ta bar ta , ta yi tafiyar ta

BARI MU LEKO MUTANAN US NA SAN KAFIN NAN BARIRA TA ISA GIDAN SU 🤣🤣🤣🤣🤙

▪US ( WASHINGTON DC )

*MISALIN KARFE 2 NA DARE

▪ASH 🔥

A hankali ya ke tako stair din gidan ya sauko parlourn Kassa
Har ya nufi dining room ya ga haske da ga cikin part din Nihal

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya ya nufi part din Nihal , ya na isa ya tura kofar ya na sallama cen kassan makoshi

Nan ya ga Nihal da Rayan su na zaune saman sofa three seaters
A tare su ka kai kallon su wajen kofar su na amsa mishi sallamar shi sannan Rayan ya daura da cewa " General ba ka yi barci ba "

Karasowa ya yi cikin parlourn ya zauna saman sofar geffen ta su ya na fadin " His excellency ba ka yi barci ba "

Murmushi mai dan sauti Rayan ya yi kafin ya ce " ban yi ba , na zo yi wa sister di ta Allah kiyaye hanya , amma ban ji dadin rashin bin ku ba wlh , na so na je Nigeria ni ma ko dan na ga su Haidar "

" Yaya Rayan , ka bari idan mun dawo sai ka tafi , ka ga Ash sai ya kula da office din shugaban kassa " Nihal ta fada ta na murmushi

" mummy ni fa ba zan iya aiki shugaban kassa ba , ko shi his excellency da ya ya ke yi " Ash ya fada ya na kallon Rayan

Yar dariya Rayan ya yi kafin ya ce " General , wlh aikin shugaban kassa babu sauki , ni har na fara nadamar hawa na wannan kujerar "

" To sai a ci gaba da rikewa dan babu wanda zai hau ta cikin gidan nan " Ash ya fada ya na mikewa
Da sauri Nihal ta taro shi ta na fadin " Ash ina za ka je haka "
" zan koma na yi barci , dama My angel ne ya tada ni wai fruits zai sha " ya fada ya na sa kafa ya fice part din

Da kallo su ka raka shi har sai da ya fita sannan Rayan ya juyo ya kali Nihal ya ce " Sister ya kamata mu kawo karshen gwaurancin General & Marshal , dubi ki ga yadda ya sangar ta Vedad , ki na fa ji cewa ya yi My angel , gaskiya ya kamata a nemo mishi mata "

Yar dariya Nihal ta yi kafin ta ce " kar ka damu Yaya Rayan , kai dai ka roki Allah , ya hada ni da kyakyawar yarinya , mai tarbiya , da adini , wlh ko sun ki , ko sun so sai sun yi aure "
Hararrar wassa Rayan ya yi mata ya na fadin " ke dai , ke dai sister yaushe ki ka koyi mugun ta haka "

Dariya sosai Nihal ta yi kafin ta ce " yaya Rayan ba wata mugun ta , ai mu ma haka a ka yi mana kuma ga shi , yanzu har da yaran mu hudu , ka ga hakan shi ne hanya ma fi sauki da za mu aurar da su , in mu ka ce mu bi ta ra'ayin su wlh ba za su yi auren nan ba "

" Gaskiya ki ka fada , amma sai mun yi a hankali "
" kai dai yaya Rayan ka bar maganar nan a hannu na za ka sha mamaki " ta fada cikin gwarin guyiwa
Dan karamin murmushi Rayan ya yi kafin ya ce " shikenan , ki dai kula min da kan ki sister Allah ya kiyaye hanya ya dawo min da ku lafiya , ya dawo da ku lafiya sister di na "
Ita dai Nihal da amine ta ke amsa mishi da ga haka su ka yi sallama ya fice part din ya tafi na shi , ita kuma Nihal ta tashi ta shiga bedroom din ta ta wuce toilet ta yi wanka sannan ta shirya cikin kayan barcin ta , ta konta asuba ta gari

▪WASHE GARI

Misalin karfe 8 dai'dai na safe duk mutanan gidan su ka shirya har da Rayan su ka fice gidan su ka kama hanyar international airport of Washington-Dulles

Duk wasu shirye shirye da za a yi an riga da an yi su , Ash kadai a ke jira
Airport din cike ya ke jibga jibgan sojoji da dankara dankaran motoci ma su nunfashi , ban ma yi kokarin kilga su ba dan na san ba zan iya ba wlh

A haka su ka wuce kai tsaye cikin Jet din Ash , su na shiga ya daga ko , ya kama hanyar Nigeria , his excellency Rayan kuma ya kama hanyar white house kamar yadda su ka yi da Ash , sai dai mu ce Allah ya tsare ku , ya kai ku lafiya
Bari mu leko su Hayat na san kafin nan jirgin su ya sauka

▪NIGERIA ( KANO STATE )

▪HAYAT 💦

Misalin karfe 7 na safe bus din su ya shigo cikin garin Kano ,
Ta na tsaka da barcin ta mai mugun dadi driver ya tada ta , ya na ce mata ta tashi sun iso
A rude ta tashi ta na bin wajen da kallo , ta na tambayar in sun iso
" eh min iso , sai ki sauka ki tafi wajen dan uwan na ki , Allah ya kiyaye hanya " Driver ya fada mata

Wasu yawu ta hadiye kafin ta ce mishi " dan Allah , dan uwa zan iya samun wani abu na ci wlh yunwa na ke ji " ta fada ta na marairaice fuska

Dan karamin murmushi ya yi kafin ya kai ya dauki bread din da a ka sayo mishi da gorar ruwa guda ya mika mata
Da sauri ta kai hannu ta karba ta na washe baki ta shiga jero mishi aduo'in godiya har sai da ya ce mata ta tafi ya isa haka
Ba musu ta sauka da ga cikin motar , shi dai da kallo ya raka ta har sai da ta bacewa ganin shi sannan ya saki wani cool murmushi , har ga Allah yarinyar nan ta kon ta mishi a rai , ya ji tausayin ta sosai , sam yanayin idanun ta bai sa ya ji kyamar ta ba , sai ma burge shi da su ka yi , ya so ya raka ta har gidan su amma ba zai iya ba , dama saboda ita ya ba da kudi a ka amso mishi bread din nan , ko da ba ta tambaya ba , shi da kan shi zai ba , Sai dai na ce Allah ya biya ka , dan a wannan zamanin ba kowa ba zai yi irin wannan taimakon da ka yi

▪KADUNA

▪ KADUNA INTERNATIONAL AIRPORT

Misalin karfe daya na yamma jirgin su Nihal ya sauka a cikin international airport na kaduna , allamun a kaduna za su sauka

Airport din cike ya ke da manya manyan motoci ma su nufashi ma su bala'in kyau da tsada ni kassa kilga su ma na yi , ga ubanin sojoji cike da airport din kowane rike da gun , ba fa sojojin Nigeria , sojojin US ko shugaban kassar Nigeria da kan shi ba zai samu irin wannan tarbar ba , tun cikin daren jiya Rayan ya ba su umarni su taho , tare da wannan manyan motocin , musaman dan shirya zuwan familyn shi , har gidan da za su zauna sojojin nan sun riga da sun gyara komai

Kai tsaye wajen motocin nan su ka nufa , Ash da junior su ka shiga mota guda , Ummi da Nihal su ka shiga mota guda , sai Iqbal da Vedad su ka shiga mota guda , a jere motocin su ka bar airport din nan da mugun gudu su na jiniya kamar wanda za su tashi sama

Ba su dauki wani lokaci ba su ka iso cikin unguwar Nassarawa ,
Tun kafin su iso bakin kofar gidan , sojojin da ke cikin gidan su ka wangale musu kofar , su ka yi cikin gidan da mugun gudu
Kai tsaye parking space su ka nufa , su ka yi parking din motocin su , sannan sojojin nan su ka fara dirowa da ga cikin motocin su da sauri sauri kawai ji ka ke dib dib dib
Da gudu su ka nufi motocin mutanan gidan su ka bubude mu su kofa , su na sarawa Ash da junior
Chapter 13 · 0% Book details