← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 26

Sashe 3

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Nihal ta boye fuskar ta a kirjin Rayan ta na kara sautin kukan ta
Ci gaba da takowa ya yi ya zo gaban ta ya tsuguna ya riko hannayanta ya ce " mummy please stop crying , ba na son ganin ki cikin wannan halin , so ki ke ki karaya mana zuciya , Daddy ya tafi ya bar mu , kema ki tafi ki bar mu ? Ya ki ke so mu yi ? Please mummy ki daina kar ki janyo wa kan ki wata illa "

Slowly Nihal ta fara rage sautin kukan ta , ta shiga sauke ajiyar zuciya
Ya na jin hakan ya mike da ga tsugunin da ya yi ya koma saman bedside drawer ya zauna ya na kallon mummyn ta shi
Bai fi two minutes da zama ba Ummi ta shigo dakin kai a sunkuye ta na tafiya kamar wadda a ka daure kafafun ta

Gaban Nihal ta karaso ta Zube saman guyiwowin ta , ba tare da ta dago kai ba ta ce " i'm sorry mummy , na san na dauki tsawan shekaru ina bata miki rai , please forgive me , na san inda Daddy ya na nan ba zai taba yin alfahari da ni ba , duk tarbiyar da ya ba ni kafin ya tafi na yi watsi da ita na dauko wadda ba tawa ba , mummy ina kewar Daddy na sosai , har yanzu ban gama grief din shi ba , ko wace safya idan na tashi na shigo bedroom din ki na ga ke daya ce duk sai na fara danasanin zowa da yi , shi ya sa ki ka ga na daina zuwa gaishe ki da safe , mummy kar ki ce za ki tafi ki bar ni wlh ba zan iya jure rashin ku ba cikin rayuwa ta , duk irin rashin kunyar da na ke yi miki ba dan ba na son ki ba ne wlh mummy ina son ki fiye komai a rayuwar nan idan ke ma ki ka tafi ki ka bar ni wlh ni ma sai na bi ki , ke kadai ce na ke iya kallo na rage radadin rashin Daddy kusa da ni " kassa ci gaba da maganar ta ta yi sakamakon kukan da ya ci karfin ta

A hankali Nihal ta dago kan ta , ta talabo fuskar Ummi ta ce " Ummi na ya isa haka ki daina kukan nan kin ji ko ? " ta fada mata cikin sanyi

Mikewa tsaye Ummi ta yi ta dawo geffen Nihal ta zauna sannan ta rungume ta ta na fadin " i love you my mummy "
Dan karamin murmushi Nihal ta yi ta na fadin " ni ma ina son ki Ummi na "

Murmushi mai dan sauti Rayan ya yi kafin ya kali Little ya ce mishi " Little ! Je ka kawo mana abinci a nan za mu yi dinner "

Tsuke fuska ya yi ya na kallon Rayan ba tare da ya ce komai
Yar karamar dariya Rayan ya yi kafin ya ce " sorry General Ash , je ka kawo mana abinci "

Bai gama rufe bakin shi ba wani saurayi ya shigo dakin ya na rike da wani tray ya ce " ba sai ya je ba mun kawo "
Saurayin ya na kama sak da Nihal kamar an tsaga kara har colour din idanun brown a shekaru zai kai 24 years haka

Cikin dakin ya karaso ya tsaya gaban Nihal ya ajiye tray din kassa saman dan carpet da ke bakin gadon sannan shi ma ya zauna sama
" to malam sai ka je ka kira Vedad " Ash ya fada ya na kallon shi
( kar ku ce ba ku gane ba Ash ba kowa ba ne face Alyasat 😴😴 da haka su ke kiran shi yanzu , ni ma ban san dalili ba )

Noke kafada ya yi ya na shirin magana dayan saurayin ya shigo ya na rike da tray din fruits
Shi kuma wannan ya so ya dan yi kama da Aylan , sai dai shi ya na da kananan idanu farare kal amma kwayar cikin su Sky blue da ita har wani kyali ta ke gwanin burgewa a shekaru ba zai wuce 20 years ba

Geffen saurayin nan shi ma ya zauna ya ajiye tray din gaban shi
Shagwabe fuska ya yi ya na kallon Nihal ya ce " mummy , sauko ki ci , ko na cinye abu na dan ni fa gaskia yunwa na ke ji "

Saurayin da ke geffen shi ya dunkule hannun ya kai mishi bugu a damtse ya na fadin " Wai kai Vedad yaushe za ka daina wannan shirmen , ba fa yaro ne kai ba "

Vedad na shirin magana Nihal ta riga shi cewa " Iqbal , wlh ka daina buga min auta na " ta fada cikin tsare gida

Ummi da ke zaune geffen ta ta ce " mummy wlh duk ke ki ka goyawa Vedad baya ya na yi mana abun da ya ga dama , da an taba shi ki ce uban wa "

Yar karamar dariya Nihal ta yi kafin ta sauko kassa ita saman carpet din
Ta na zama Vedad ya yi sauri ya koma gefen ta ya zauna ya na murmushi
Ita ma Ummi saukowa ta yi ta koma dayan geffen Nihal ta dauki plate ta ajiye ma kowa gaban shi ta fara serving din su

Ta na farawa Rayan ya mike tsaye a hankali ya nufi kofar fita dakin ya ficewar shi ya bar ta tare da yaran ta ya na fita Ash ya mike shi ma ya bi bayan shi

Da sauri Nihal ta ce mishi " Ash ! Ba za ka ci tare da mu ba ne "
Ba tare da ya tsaya da ga tafiyar shi ba ya ce " ina zuwa mummy " ya kai karshen ya na ficewar shi

Rayan na shirin barin part din Ash ya ce mishi " His excellency ina son mu yi wata magana "

Cak Rayan ya tsaya ya juyo ya na kallon Ash da ya ke tunkaro shi fuska dauke da murmushi

Shi kuma Ash ya na karasowa gaban Rayan ya dai'dai ta tsayuwar shi ya rike hannayan shi a baya ya ce " His excellency..... "

Da sauri Rayan ya katse shi da cewa " Ash wai ba za ka daina kira na da his excellency ba , yanzu fa a gida mu ke "
Sakin hannayan shi Ash ya yi ya ce " okay uncle, ina so zan je Nigeria wajen wani aiki, so ina son ka kira Mr president ka fada mishi ya shirya mana gidan da za mu sauka "

" no ba sai an yi haka ba , mu na da gida je a Nigeria kawai in ka tashi tafiya ka fada min , kai da wa za ka tafi ne ? "

Sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce " all " a takaice
Cike da rudu Rayan ya ce " ban gane ba "

" uncle , aiki ne zan tafi yi a cen so ina da bukatar Junior tare da ni , na fadawa mummy ta ce ita ma za ta je domin yin wani aiki , shi ya sa na ce su shirya mu tafi baki daya "

Shiru Rayan ya yi ya na kallon shi na dan lokaci kafin ya ce " dan ka San ba zan iya biyar ku ba ne za ka min haka , yanzu ya zan yi cikin gidan nan ni kadai ? "

" zan so ka koma White house kafin mu dawo "
" okay yanzu yaushe za ku tafi "
" next week "
" okay , Allah ya ba da sa'a " ya na gama fadar haka ya juya ya ficewar shi

Da amine Ash ya amsa mishi cikin zuciyar shi kafin shi ma ya juya ya koma cikin bedroom din Nihal ya na sallama kassa kassa

Yanayin da ya tardo su abun ba karamin sanyaya mishi zuciya ya yi ba , kawai sai ya koma saman bedside drawer ya zauna ya na ci gaba da kallon su , su na cin abincin su su na dariya , Vedad kuma Nihal na ba shi a baki kamar karamin yaro

Bangaran Rayan kuma kai tsaye dining room ya koma
Nan ya tardo junior zaune shi kadai ya na faman latsa wayar shi

TAღRIN ZღCIYA 💖🌺💍

( RETღRN )

(ROMANTIC LUV STORY )💋🔥

❤👑 ꪑꪖꪶꪶꪖƙỉ᭢ ꪖꪑꫀꫀꪹꪖꫝ ꪖꪉᦔꪮꪗꪶꪖꪗꫀ 👑❤
𝗔.𝗞.𝗔 𝐀𝐍𝐈𝐒𝐇❥ 🕊💞

Wattpad : @bennybite

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )

FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks 👍💕

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ️

DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMETS SECTION

👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i

𝗧𝗔𝗣 𝗧𝗛𝗜𝗦 𝗟𝗜𝗞𝗘 𝗧𝗢 𝗝𝗢𝗜𝗡 𝗠𝗬 𝗣𝗢𝗦𝗧𝗜𝗡𝗚 𝗥𝗢𝗢𝗠

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054

_________________✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦__________________

[ 🅿🅰🅶🅴̥ 2 ❤🔥 ]

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

Saman chair din shi ya koma ya zauna ya na shirin magana junior ya riga shi cewa " ashe ba ka manta da ni ba "

" why zan manta da kai ? " Rayan ya fada ya na serving din kan shi
Ajiye wayar shi gefe junior ya yi sannan ya fara serving din kan shi, shi ma sannan ya ce " ka saba yi min hakan ai "

Dakatar da abun da ya ke yi Rayan ya yi ya kali junior ya ce " Aylan junior ........ "

Da sauri junior ya katse shi da cewa " please Dad why ba za ka iya kira na da Aylan kai tsaye ba kullum sai ka kara da junior , ko sunan ne bai dace da ni ba "
Chapter 3 · 0% Book details