← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 26

Sashe 12

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta ce mishi " eh eh , akwai baban yaya na , da mu ka yi waya da shi a cen zai zo dauka ta " ta fada mishi

Gyada kan shi ya yi a hankali kafin ya bude kofar shi ya sauko sannan ya ce mata ta hau
Cike da murna ta Haye bus din , ta zauna geffen driver sannan ya Haye ya rufe kofar
Ya kai hannu ya dauki gorar ruwa da ke gaban steering motar ya mika mata
Da sauri ta sa hannu ta karba ta na yi mishi godiya kafin ta bude ta , ta baki babu ko bismillah ta fara sha , sai da ta shanye ruwan duka sannan ta sauko gorar ruwan ta na nishi godiya dama kishi ta ke ji

Dan karamin murmushi ya yi kafin ya ce " me ye sunnan ki ? "
" Shahd , amma Hayat a ke kira na da shi "
" Masha Allah duka sunayan ma su dadi ne "
Dan karamin murmushi ta yi ta na sunkuyar da kai kassa
Shi ma dan karamin murmushi ya yi ya kauda kan shi gefe , da ga haka ba wanda ya sake cewa wani abu har lokacin tafiya ya yi , driver ya tada motar su ka kama hanyar Nigeria , su na barin gidan bus din ko kwana ya dauki Hayat

▪WASHE GARI

Misalin karfe 8 na safe inna ta tashi da ga barcin ta , ta shiga dakin Hayat kamar ba ta san abun da ya faru ba ta fito da gudu ta na kara ta na fadin " Wayooo Allah na shiga uku , Hayat , Hayat , Adda Hayat ba ta cikin gidan "

Da gudu mutuman da ta kira da Adda ya fito da ga cikin dakin shi babu ko riga a jikin shi ya na fadin " Barira me ki ke fada ne haka , duba da kyau ko ta shiga ban daki "

Kukan kariya Barira ta saki ta na fadin " Adda na duba ko ina cikin gidan nan har bakin kofa na duba , babu Hayat har kayan ta babu su , Adda wlh guduwa ta yi , na shiga uku na ni Barira "

" Barira na shiga uku , ina Shahd ta tafi , sati biyu saura auren ta da rabeh , ko na sayar da shanu na ba zan samu kudin biyan shi sadakin ta da ya bayar , ga shi kuma na kashe kudin , na shiga uku ni Issa "

" Issa , ka na nufin dama Rabeh ya biya sadakin Hayat " Barira ta fada cike da rudu dan ita a iya sannin dala daya ba ta ga ni ba da sunnan sadakin Hayat

" Eh ya biya , Jakka Dari ya ba ni kuma wlh na kashe su dan yanzu bai wuce , jakka ashirin su ka yi min saura ba " ya fada kamar zai yi kuka

Daura hannayan ta saman kai Barira ta yi ta na fadin " Issa , Issa , Issa wlh ba za ka ga annabi ba , ka fi kowa sanin halin Rabeh cikin kauyen nan kuma a haka ka ce za ka dauki yarinya ta tilo ka aura mishi , ko dan ba kai ka haife ta ba , Issa wlh duk abun da ya samu yarinya ta , Allah ya isa tsakani na da kai "

Rage sautin Muryar shi ya yi ya na matsowa kusa da ita ya na fadin " ke don Allah ki rage sautin Muryar ki , kar makauta su ji mu na shiga uku "

Da sauri ta katse shi da cewa " sun yi dare in ba su ji mu ba , wlh Issa tun dare bai yi maka ba gwara ka fita nemo min yarinya ta , idan ba haka ba wlh zan dau kafa har birni na kai karar ka wajen yan sanda , macuci kawai , wlh na yi nadamar auren ka , kuma da ga nan gidan mu zan tafi ka kai min takarda ta na gaji da wannan auren azabar na ka " ta na gama fadar haka ta juya ta shigewar ta daki ta na kukan munafirci kamar ba ta san lokacin da Hayat ta bar gidan ba

Nan ta bar shi sai faman muzurai ya ke yi , ya kali nan ya kali nan ya rasa abun da zai yi , ya na a haka Barira ta fito da ga cikin dakin ta , ta na yafe da wani gyale ta rike da wani buhu na kayan ta , ta tsuke fuska allamun ba wassa

Issa na ganin ta ya nufe ta da sauri ya na fadin " Barira , Barira ina za ki je haka "
Cak ta tsaya ta rike kugun ta , ta na fadin " ka sake ni , Issa , na gaji da auren ka , dama ko cen ba son shi na ke ba "
Da sauri ya riko buhun kayan ta ya fadin " don Allah Barira ki tsaya ki ji mana , mu shawo kan matsalar nan tun kafin a jiyo mu "

Bai gama rufe bakin shi ba , ta fido wata wuka da ga kugun ta , ta na fadin " Issa ka sake ni , ko na kashe ka "
( 🤣🤣🤣🤙🤙 wayoo Allah ciki na , Ku bawa Barira hannu don Allah )

Cike da tsoro Issa ya saki buhun ta , ya ja da baya , ya baya , Muryar shi har kerma ta ke ya na fadin " ke , ke Barira ba ki da hankali ne , ajiye wukar nan "

Sakin buhun hannun ta ta yi ta sa hannu ta yaye kyalen ta , ta na daga murya ta ce " Eh ba ni da hankali Issa , wlh ka sake ni ko na kashe ka cikin gidan nan , ka kashe min miji na , ka raba ni da yarinya ta , yanzu kuma ka na son ka kashe ni ko , wlh sai ka sake ni ko ni na fara kashe ka " ta kai karshen ta na nufar shi da wukar

Wata razananiyar kara ya saki kamar mace ya yi baya da gudu ya na fadin " ke lafiyar ki kuwa ko aljanai su ka shige ki "

Da gudu ta nufe shi ta na fadin " eh aljanai ne , Issa ka sake ni , Ka sake ni ko na kashe ka , Yau ko mu ko kai cikin gidan nan yihuuuu , sai mun kashe ka Issa , Issa , Issa sai mun kashe ka " ta fada kamar mai aljanun gaske har wani nishi ta ke yi kamar mai farfadiya ta na biye da shi da gudu da wuka a hannun ta

Shi kuma dan rashin hankali ya kassa shiga cikin daki kawai ya yi ta zagayen harabar gidan ya na kara ya na fadin " Jama'a taimako , Qul yaa ai-yuhaal kaafiruun , Quuluu aamannaa billahi wamaa unzila ilainaa wamaa unzila ila ibraahiima , bismillah rahim , A'uzubillahi mina sharrin Barira , Jama'a ku taimake ni za ta kashe ni " ya kai karshen kamar zai yi kuka
Ya na gama fadar haka ya fada cikin dakin shi ya turo kofar ya danne da karfin shi , har wasu fitsari ya saki , yau ya ga mutuwa

Duk da haka Barira ba ta kyale shi ba sai da ta bi shi ta na bugun kofar dakin da duk karfin ta ta na fadin " Issa ka sake ni , za mu kashe , za mu kashe ka "

" Barira ki je na sake ki , don Allah ki kyale ni "
" saki nawa " ta fada ta na barin bugun kofar
" saki daya ! " ya fada
Wani wawan bugu ta kai wa kofar da duk karfin ta , har sai da ya nemi faduwa ta na fadin " saki uku mu ke so "

Cike da tsoro ya ce " ki je na sake ki saki uku " ya fada kamar zai yi kuka
Ya na fadar haka Barira ta saki wani kyawatencen murmushi ta saki wukar hannun ta ta fado ta juya da sauri ta dauki buhun kayan ta , ta fice gidan

ALLAH YA KARA MANA SON MANZON SA ❤
WAYOOO AMMA YAU NA SHA DARIYA 🤣🤣🤣🤙🤙🤙

TAURIN ZUCIYA 💖🌺💍

( RETURN )

( ROMANTIC LOVE STORY )💋🔥

❤👑 MALLAKIN MEERAH 👑❤

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

PAGE 5 ❤🥂

TAღRIN ZღCIYA 💖🌺💍

( RETღRN )

(ROMANTIC LUV STORY )💋🔥

❤👑 ꪑꪖꪶꪶꪖƙỉ᭢ ꪖꪑꫀꫀꪹꪖꫝ ꪖꪉᦔꪮꪗꪶꪖꪗꫀ 👑❤

𝗔.𝗞.𝗔 𝐀𝐍𝐈𝐒𝐇❥ 🕊💞

Wattpad : @bennybite

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )

FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks 👍💕

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ️

DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMETS SECTION

👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i

𝗧𝗔𝗣 𝗧𝗛𝗜𝗦 𝗟𝗜𝗞𝗘 𝗧𝗢 𝗝𝗢𝗜𝗡 𝗠𝗬 𝗣𝗢𝗦𝗧𝗜𝗡𝗚 𝗥𝗢𝗢𝗠

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054

_________________✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦__________________

[ 🅿🅰🅶🅴̥ 5 ❤🔥 ]

Ya na fadar haka Barira ta saki wani kyawatencen murmushi ta saki wukar hannun ta ta fado ta juya da sauri ta dauki buhun kayan ta , ta fice gidan
Chapter 12 · 0% Book details