← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

dan karamin murmushi Hayat ta yi ta na sunkuyar da kai wai ita ta ji kunya
dariya sosai Hajiyah ta yi , sai da ta tsagaita dariyar ta sannan ta ce " wai kunya ta ki ka ji , Shikenan ga perfume ki Feshe jikin ki da shi , sannan ki fito ki ci abinci na san ki na jin yunwa " ta na gama fadar haka ta ajiye perfume din saman bedside drawer sannan ta juya ta fice

ta na fita Hayat ta dauki karamin hijab din nan ta saka sannan ta dauki perfume ta feshe jikin ta da shi
maimakon ta fita sai ta nufi dressing mirror a hankali , ta tsaya ta na kallon kan ta
ba ta san lokacin da ta saki wani cool murmushi , ita da kan ta sai da ta ji ta burge kan ta ba karamin kyau ta yi ba , kamar ba yar Ƙauyen nan ba

a hankali ta juyo ta nufi kofar dakin ta fice , ta fito parlourn nan ta isko Hajiyah zaune saman sofa ita da wani kyakyawan saurayi , kamanin su daya da Hajiyah sai dai ta fi shi haske saboda bliching

karaso wa cikin parlourn Hayat ta yi ta na sallama cen kassan makoshi
slowly saurayin nan ya dago kai ya na amsa mata sallamar ta a ra'rabe
ita Hayat ba ta ma san ya na yi ba ta karaso cikin parlourn ta zauna saman carpet ta na sunkuyar da kai

sai bin ta da kallo saurayin nan ya ke yi har sai da ta zauna sannan ya janye idanun shi ya kali Hajiyah ya ce " Hajiyah wacece wanan kuma ? "

wani dan karamin murmushi Hajiyah ta yi ta na fadin " she's my guest yarinyar wata friend's di ta ce "

gyada kan shi kadan sauran yin nan ya yi kafin ya kali Hayat ya ce " what's your name " ya fada da turanci
shiru Hayat ta yi ba ta dago kan ta ba allamun ba ta ji abun da ya ce ba

" ohhhh Ba ta jin turanci kai ma " ta fada dan ta san da wuya ne a ce ta na jin turanci dan ba ta yi kama da yaran da ke zuwa school ba

kallon Hayat ta yi sannan ta ce " Hayat ! "
a hankali Hayat ta dago kai ta na amsa mata da " na'am "
nuna mata saurayin nan Hajiyah ta yi ta na fadin " Hayat wannan shi ne yaro na Razak , ki gaishe da yayan ki mana "

gyada mata kai Hayat ta yi kafin ta juya ta kali Razak murya kassa kassa ta ce mishi " ina wuni ? "

murmushi ya yi ya na fadin " lafiya lau , ya ki ke ? "
" Lafiya " ta fada a takaice ta na sunkuyar da kan ta
kallon Hajiyah ya yi cikin harshen turanci ya ce " Hajiyah ba za ki neman min auren ta ba gaskiya ta konta min a rai "

hararrar wassa Hajiyah ta yi mishi ta na fadin " ba na son shirme da ga ganin yarinya sai ka ce ta kon ta ma ka a rai ? to tun wuri ka cire ta , nan gani nan bari "

marairaice fuska ya yi ya na fadin " please Mum , why za ki yi min haka , ni gaskiya ina son ta "
wani mugun kallo ta wurga mishi cikin zuciyar ta ta na fadin " ka ga dan iskan yaro ka na neman ka bata min shiri "
cen kuma sai ta saki wani kyawatencen murmushi ta ce " shikenan zan yi magana da mamar ta , in ba a fitar mata da miji ba "

wani kyawatencen murmushi Razak ya saki kafin ya ce " yawwa mummy na shi ya sa na ke mugun son ki "
murmushi kadai Hajiyah ta yi ba tare da ce komai ba
ita dai Hayat kamar babu ita a wajen , ga shi da turanci su ka yi maganar su ita kuma ba jin turanci ta ke yi ba

su na a haka wata yarinya ta fito da ga cikin Kitchen ta na rike da wani tray dauke da wani plate rufe da wani plate din
bakin ta da sallama ta shigo parlourn
sai da Hajiyah ta amsa mata sallamar ta sannan ta ce " ajiye mata " ta kai karshen ta na nuna Hayat
ba musu yarinyar nan ta ajiye tray din gaban Hayat sannan ta mike ta komawar ta kitchen

ta na barin wajen Hajiyah ta ce ma Hayat " bude ki ci mana , na san ki na jin yunwa "
gyada mata kai kawai Hayat ta yi kafin ta kai hannu ta bude plate din , ta sa hannu har za ta fara ci Hajiyah ta tsaida ta da cewa " a'a dauki spoon mana "

a hankali Hayat ta gyada mata kai sannan ta kai hannu ta dauki spoon din da ke geffen plate din , a haka dai ta ka'kama duk da ba ta taba cin abincin da spoon ba amma sai da ta cinye jollof rice din nan tasss , sannan ta kora da ruwa , dama yunwa ta ke ji

su dai Hajiyah da razak kallon ta kawai su ke yi su na murmushi har sai da ta gama sannan ta dauki tray din ta mike tsaye

da sauri Hajiyah ta taro ta ta na fadin " zauna war ki , za ta dawo ta dauke shi "
girgiza mata kai Hayat ta yi ta na fadin " zan kai mata "
da to kawai Hajiyah ta amsa mata , da ga haka ta juya ta na rike da tray din ta nufi dining room

bakin ta dauke da sallama ta shigo kitchen din
nan ta isko yarinyar nan tsaye gaban gas cooker , slowly ta juyo ta na amsa mata sallamar ta
" ina zan ajiye " Hayat ta fada cen kassa kassa
wani desk yarinyar nan ta nuna mata ba tare da ta ce komai ba
desk din Hayat ta nufa ta ajiye tray din sannan ta karaso geffen yarinyar nan ta tsaya ta na fadin " minene sunan ki ? "

dan karamin murmushi yarinyar nan ta saki kafin ta ce " duk cikin yaran da Hajiyah ke kawowa gidan nan ke ce ta farko da ki ka yi min wannan tambayar , suna na Fatima "

" kennan bayan ni akwai yaran da su ka sha zuwa gidan nan " Hayat ta fada cike da mamaki dan Hajiyah ta fada mata ita kadai ce a gidan bayan yaron ta ba me zuwa

gyada mata kai Fatima ta yi ta na fadin " eh mana , ki na nufin ba aiki za ta samo miki ba "
girgiza mata kai Hayat ta yi kafin ta ce " a'a kawai mun hadu da ita saman hanya shi ne ta kawo ni gidan ta "

wani murmushi mai dan sauti Fatima ta yi kafin ta ce " ban cika shiga cikin harkar da ba tawa ba , amma da zan ba ki shawara tun wuri ki bar gidan nan , kafin ki yi nadamar shigowa cikin shi "

cike da rudu Hayat ta tambaye ta " me ki ke nufi ? "
dan karamin murmushin geffen fuska Fatima ta yi ba tare da ta ce komai ba ta ci gaba da aikin ta
ita dai Hayat ta rasa me ta ke nufi da maganar ta , jin yadda ta yi shiru ba ta amsa mata ba kawai sai ta juya ta bar wajen ta fice kitchen din

bayan ta fito kitchen din kai tsaye ta dawo parlour , har za ta wuce bedroom din ta , ta jiyo Muryar Razak ya na fadin " Sister ba za ki zo mu yi sallama ba , tafiya zan yi "

cak ta tsaya ta juyo a hankali ta dawo cikin parlourn ta zuba mishi ido ta kassa cewa komai
daga mata gera guda ya yi allamun minene
girgiza mishi kai ta yi murya kassa kassa ta ce " Allah kiyaye hanya "
ta na gama fadar haka ta juya da sauri sauri ta koma bedroom din da ta fito

da ido ya raka ta har sai da ta shiga dakin ya na kallon bayan ta ,ya na lashe lips
sai da ta shiga dakin sannan ya mike tsaye ya na fadin " Mum ni zan tafi may be nan da two days na dawo "

mikewa tsaye ita ma Hajiyah ta yi ta na fadin " Okay , Allah ya kiyaye hanya Baby na , sai ka dawo "
sai da ya kai bakin kofar sannan ya juyo a hankali ya ce " please mum kar ki manta magana ta " ya fada kamar zai yi kuka

gyada mishi kai ta yi ta na fadin " shikenan Baby na , zan fada mata , sai ka dawo "
ta na gama fadar haka ya sa kai ya fice gidan
da kallo ta raka shi har sai da ya fita sannan ta ce " Gaskiya sai dai ka yi hakuri , amma ba zan aura maka yarinyar nan ba , akwai shiri na musaman da na yi a kan ta , wannan kyawon na ta ba kananan kudade zai kawo min ba "

ta na gama fadar haka wayar ta da ke saman table , ta fara ringing
hannu ta kai ta dauki wayar ta na kallon screen din
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta dauki kiran ta kai wayar a kunne ta na fadin " Alhajin Allah , yanzu ko na ke shirin kiran ka ! "

shiru ta yi ta na sauraron abun da mutuman ke fada dan ni ba na iya jiyo abun da ya ke cewa

shiru ta yi na dan lokaci kafin ta saki wata shegiyar dariya ta na fadin " Alhaji Alhaji , ban jima da dawowa ba , yanzu haka ina gida kai kadai ne ke jira , ka zo Aljihu cike dan na yi sabon kamu yau "
Chapter 21 · 0% Book details