← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 26

Sashe 6

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

( RETღRN )

(ROMANTIC LUV STORY )💋🔥

❤👑 ꪑꪖꪶꪶꪖƙỉ᭢ ꪖꪑꫀꫀꪹꪖꫝ ꪖꪉᦔꪮꪗꪶꪖꪗꫀ 👑❤
𝗔.𝗞.𝗔 𝐀𝐍𝐈𝐒𝐇❥ 🕊💞

Wattpad : @bennybite

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )

FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks 👍💕

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ️

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMETS SECTION

👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i

DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

𝗧𝗔𝗣 𝗧𝗛𝗜𝗦 𝗟𝗜𝗞𝗘 𝗧𝗢 𝗝𝗢𝗜𝗡 𝗠𝗬 𝗣𝗢𝗦𝗧𝗜𝗡𝗚 𝗥𝗢𝗢𝗠

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054

_________________✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦__________________

[ 🅿🅰🅶🅴̥ 3 ❤🔥 ]

▪ US ( WASHINGTON DC )

Misalin karfe 10 na safe Nihal ta na zaune cikin parlourn gidan ta na kallon Tv
Ta na haka kawai sai ganin wata yar karamar yarinya ta shigo parlourn da gudu ta na fadin " Mamie , Mamie , Mamie " ta kai karshen ta na fadawa jikin Nihal

Yarinyar fara ce tas kamar baturiya amma kallo daya za ka yi mata ka san jinin haoussawa ce , a shekaru ba za ta wuce 4 years ba , ta na sanye cikin wata gown pink colour mai mugun kyau

Wani kyakyawan murmushi Nihal ta yi kafin ta dauki yarinyar ta daura ta saman cinyar ta ta na fadin " Haleen di na , shi ne ba ki fada min za ki zo ba "

Yar siririyar dariya ta yi da Muryar nan ta ta irin ta yara
Ta na shirin magana Ayna ta shigo parlourn ta na sallama dan kallo daya na yi mata na gane ta , Anas ne rai da rai babu ta inda ta baro shi sai wajen wadanan ash eyes na Zarah

Cike da fara'a Nihal ta amsa mata sallamar ta kafin ta daura da cewa " ya mijin nawa ya ke ina ki ka baro shi "

Yar karamar dariya Ayna ta yi ta na dan sunkuyar da kai ta ce " ya na nan mummy ya ce ma a gaishe ki "

" Ina amsawa ki ce mishi na yi fushi tun dawowar ku da ga Turkey har yanzu bai zo gani na ba " Nihal ta fada ta na sauke Haleen da ga saman cinyar ta ta zaunar da ita geffen ta

Dai'dai lokacin da Ummi ta fara sauko stair ta na sanye cikin doguwar riga mara nauyi fara kal , ta saki wannan curly hair din ta sak irin na Aylan ya zubo mata har saman shoulder ta na tafe kai a sunkuye ta na latsa wayar hannun ta

Sai da ta karaso cikin parlourn sannan ta jiyo Muryar Ayna ta na fadin " Sannu Diyar Daddy "

Da sauri Ummi ta dago kai ta kali Ayna , nan take ta saki wani cool murmushi ta bude hannayan ta ta nufi Ayna

Mikewa Ayna ta yi ita ma ta nufe ta su ka rungume juna Ummi na fadin " Saukar yaushe , shi ne ba za ki kire ni ba "

Raba jikin su Ayna ta yi su na rike da hannun juna su ka koma su ka zauna saman sofar da Ayna ta taso ta na fadin " na yi wajen three weeks fa da na dawo , ko ranar da na dawo sai da na zo gidan nan amma mummy kawai na tardo "

Murmushi mai dan sauti Ummi ta yi kafin ta kali Haleen ta ce " Hi my baby girl , ba za ki gaishe da Aunty ba yau "

Noke mata kafada Haleen ta yi ta na komawa jikin Nihal ta boye fuskar ta
Yar karamar dariya Ayna ta yi kafin ta ce " ina ga ba yanzu ba za ku shirya ke da ita ba "

Ummi na shirin magana Vedad ya sauko stair da gudu Iqbal na biye da shi ya na fadin " Vedad ka dawo ka ba ni waya ta "

Karasowa cikin parlourn Vedad ya yi da gudu ya na dariya ya nufi Nihal ya zauna geffen ta ya na fadin " Mummy wlh shi da wata yarinya ya ke waya har da ce mata baby "

Da sauri Iqbal ya nufe shi ya dunkule hannu ya kai mishi bugu a ciki
Wata yar siririyar kara Vedad ya saki ya saki wayar ta fadi kassa ya ida shigewa jikin Nihal kamar baby

Kamar da ga sama su ka jiyo Muryar Ash ya na fadin " Tun da kun yi breakfast , sai mu Hau training ko ? "

A tare Vedad da Iqbal su ka juya su na kallon kofar shigowa parlourn
Ya na tsaye ya rike hannayan shi a baya , ya na sanye da Trouser na Army da t-shirt Fara

A hankali ya ke takowa ya karaso cikin parlourn kallon Nihal ya yi ya ce " Mummy , ku shirya gobe za mu Tafi Nigeria "

" ban gane ba , ba cewa ka yi ba sai next week " Nihal ta fada
Stair ya nufa ba tare da ya juyo ba ya ce " Vedad , Iqbal let's go " ya kai karshen ya na fara hayewa stair

Kallon juna Iqbal da Vedad su ka yi kowa ne sai zaro idanu ya ke yi , sun san abun da Ash ya ke nufi da hakan

" To sai ku tashi ku je tun bai dawo neman ku ba , laifin ya karu " Ummi ta fada ta na yi musu dariyar keta

Mikewa tsaye Vedad ya yi ya na dan karamin tsaki ya fara takawa ya nufi stair ya na fadin " wlh in ya dake ni a kan ka zan rama "
Bin bayan shi Iqbal ya yi zuciya na duka uku uku ya na tsoron a ce Ash ya ji abun da Vedad ya fada da ta shi ta kare yau

Kai tsaye part din Ash su ka nufa
A tare su ka yi sallama su ka shigo parlourn
Ya na zaune saman sofa ya na rike da laptop din shi ya na latsa wa , cikin zuciyar shi ya amsa musu sallamar su dan ko lips din shi ba su motsa ba

A hankali su ka karaso cikin parlourn tun kafin su ce wani abu ya ce musu " kneel down "

Wasu yawu su ka hadiye kafin su karaso geffen shi su ka yi kneel down su ka daga hannayan su sama kai a sunkuye

Sai da ya dauki wajen good 30 minutes a haka ba tare da ya dago ya kale su bare ya ce musu wani abu

A hankali Vedad ya fara yi mishi kukan shagwaba ya na fadin " Big bro ni fa ko breakfast ban yi ba "

Slowly Ash ya dago kai ya kale shi , cikin nitsuwa ya ce mishi " je ka kawo mana fruits "
Bai gama rufe bakin shi ba Vedad ya tashi da gudu ya fice parlourn
Hararrar kassan ido Iqbal ya yi mishi cikin zuciyar shi ya na fadin " Zan kama ka "

Ash kuma ya na jin Vedad ya fita ya ce ma Iqbal " kai da waye ka ke waya "
Dum ya ji gaban shi ya fadi har da zaro idanu
Murya na kerma ya ce " ba..... ba kowa "

Ajiye laptop din shi gefe Ash ya yi ya dago kai ya kali Iqbal ya matse gera ya ce " kariya za ka yi min "

Da sauri Iqbal ya girgiza mishi kai
" okay fada min da wa ka ke waya ko kuma mu tafi dakin horo " ya kai karshen ya na juyawa ya dauki laptop din shi ya ci gaba da abun da ya ke yi

Wasu yawu Iqbal ya hadiye ya dan ja baya kadan lips din shi har kerma su ke yi ya ce " My girlfriend " ya kai karshen ya na lumshe idanun shi da karfi ya na jiran saukar naushi

Gyada kan shi Ash ya yi kafin ya ce " She is muslim ? "
A hankali Iqbal ya bude idanun shi ya kali Ash na dan second kafin ya ce " yes she is muslim , university din mu guda "
" what is her name , da ga ina ta ke kuma "
" Maya ! Yar kassar NEW YORK ce karatu ne ya kawo ta nan amma duk familyn ta su na NEW YORK "

Shiru Ash ya yi bai ce mishi komai ba
Sai da ya dauki wajen good five minutes kafin ya ce " okay ! "
Ya na gama rufe bakin shi Vedad ya shigo dakin ya na sallama hannun shi rike da tray din breakfast din su , Fruits sai Pancakes da juice dan ya San Ash ba ya yin wani breakfast mai yauni Pancakes din ma kan shi ya dauko ma

Kassa saman carpet ya ajiye tray din sannan ya zauna shi ma , ko jiran wanda ya aike shi bai yi ba ya dauki fork da knife ya fara cin Pancakes din shi

" let's go eat " ya fada wa Iqbal ba tare da ya kale shi ba
Jinjina mishi kai ya yi kafin ya sauke hannayan shi ya matso kusa da Vedad ya fara shan fruits shi kuma cikin zuciyar shi ya godewa Allah da Ash bai mishi komai ba

Sai da ya Kamala aikin da ya ke yi sannan ya ajiye laptop din shi gefe sannan ya sauko kassa shi ma ya fara shan fruits
Ya na zama Vedad ya yanko pancake ya hada da strawberry ya kai fork din saitin bakin Ash ya na murmushi

Ba musu Ash ya bude baki ya karba dai'dai lokacin da junior ya turo kofar dakin ya na sallama
A tare Vedad da Iqbal su ka dago kai su na amsa sallamar shi , shi kuma Ash cikin zuciya ya amsa

Dan karamin murmushi ya saki ya na karasowa cikin dakin ya na fadin " Meeting a ke yi ba a gayato ni ba " ya kai karshen ya zama geffen Ash
Chapter 6 · 0% Book details