← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 26

Sashe 15

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawo da kallon ta ta yi kan Ash cike da rudu ta ke fadin " Ash , wannan pics din na miye ? Ko matar auren ce ka ke nema haka " ta fada cikin zolaya ta na yar dariya
Hannu ya sa ya karbi laptop din shi cikin ruwan sanyi ya ce mata " no , aikin da ya kawo ni ne nan "
" kamar ban gane ba ? "

Shiru ya yi na dan lokaci kafin ya mike ka mata laptop din shi , ba musu ta sa hannu ta karba ta na kallon screen din

Da sauri ta lumshe idanun ta na kauda kai gefe ta na fadin " Inallillahi ! Minene wannan abun Ash ? "
Karbar laptop din shi ya yi , kafin ya kashe ta , ya ajiye saman cinyar shi ba tare da ya ce komai ba

A hankali Ummi ta bude idanun ta , ta juyo ta kale shi ta ce " Ba dai yaran nan ne ba "
Cikin nitsuwa ya ce mata " su ne ? "
" Oh my God , yanzu wanene zai yi wa yaran nan irin wannan abun , babu ko tausayi "
" ni ma abun da na ke son sani kennan , shi ya sa na taho nan , a binciken da na yi , da ga Nigeria a ke kai yaran nan US da sunnan za a sama musu aiki "

Cikin nitsuwa ta katse shi da cewa " da ga nan a yi sacrifices din su "
A hankali ya girgiza mata kai kafin ya ce " no ba Sacrifice din su a ke yi ba "
Shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba dan ta ma rasa abun da za ce mishi
A hankali ta kontar da kan ta saman shoulder din shi ta lumshe idanun ta , ta daura hannun ta saman na shi cikin sanyin murya ta ce " Ash kar a je su ne su ka kashe...... "

Katse ta ya yi da cewa " no , ba su ba ne "
" I really missed Him " ta fada kamar za ta yi kuka
A hankali Ash ya lumshe idanun shi ya na bude su murya kassa kassa ya ce " Me too ! "
Dan karamin murmushi Ummi ta saki kafin ta daura dayan hannun ta saman kirjin shi saitin zuciyar shi cike da zolaya ta ce " kenan wannan zuciyar ba ta dutse ba ce , Allah ya kawo wadda za ta shiga ciki to "

Daura hannun shi ya yi saman na ta ya ce " bayan ke da mummy babu macen da za ta samu wuri a ciki " ya kai karshen ya na janye hannun ta

Dago kan ta ta yi ta na kallon shi ta ce " kenan ka na so na , shi ne kuma ba ka taba fada min ba " ta kai karshen ta na marairaice fuska

Slowly ya juyo ya kali face din ta " I love you more than my life "
Wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta rungume shi ta na fadin " I love you too my little "
A hankali ya zagayo da hannayan shi a bayan ta ya rungume ta shi ma , nan take ya ji wani sanyi cikin zuciyar shi , har ya manta last time da ya rungumi Twins din shi , amma ya san tun kafin ya fara horon soja ne , an jima gaskiya

Dan bubuga mata baya ya yi ya na fadin " okay , sake ni na ci gaba da aiki na "
Da to ta amsa mishi kafin ta sake shi , sai da ta manna mishi kiss a saman forehead din shi sannan ta tashi ta bar wajen , shi kuma ya dauki laptop din shi ya ci gaba da aikin shi

▪ZINDER

( KAUYEN NAWACH KALÉ )

▪BARIRA

Bakin ta dauke da sallama ta shigo cikin gidan na su
Harabar gidan ta na da girma sosai , cen na hango wata mata zaune saman tabarma , dattijuwa ce gaskia , da ga gani za ta wuce shekara 60

Barira na ganin ta ta saki kukan munafirci , ta nufe ta gudu
A rude matar nan ta ke fadin " Barira lafiya , me ya faru ki na kuka haka " ta fada dai'dai lokacin da Barira ta karaso ta zauna saman tabarma ta rungume matar nan ta na ci gaba da kukan ta ,

" kaka , Issa ya sake ni " ta fada cikin kukan na ta
Cike da tashin hankali matar nan ke fadin " na shiga uku ya sake ki ? "
Gyada mata kai Barira ta yi kafin ta daura da cewa " eh kaka , saki uku ma , kuma gashi ya sa Hayat ta bar gida kaka "
" ban gane ba , kamar ya ta bar gida "

A hankali Barira ta dago da ga jikin matar nan ta na fadin " eh kaka , kun fi kowa masaniya a kan auren da ya ke shirin yi mata da Rabeh , duka duka Hayat a nawa ta ke , ko al'ada ba ta fara ba , amma za ku sa ido ya dauke ta ya bawa mutumin da sai ya yi jika da ita , kaka Hayat ta tsere daren jiya , sai da ta ce min ita ba za ta aure shi ba amma na rufe ido , yanzu ga shi na rasa ta "

" inallillahi wa'ina illaihi raji'un , yanzu ina Hayat za ta tafi " Matar nan ta fada kamar za ta yi kuka ,
Mikewa tsaye Barira ta yi ta nufi dakin da ke fuskantar su ta na ci gaba da kukan ta , kayan ta ma a nan ta bar su

Ta na shiga matar nan ta mike ta nufi hanyar fita gidan ta fice sai sauri ta ke kamar za ta tashi sama , a haka har ta nufi fadar mai gari dan ta san wanda ta ke nema ya na cen

Ta na karasowa fadar mai gari ta ga wajen cike da mutane , a rude ta karaso wajen ta na tambayar lafiya , ba ta gama rufe bakin ta ba idanun ta su ka sauka kan gawar Issa , gaban Mai gari , kan shi sai zubar da jini ya ke

Ba ta san lokacin da ta saki wata razananiyar kara har da toshe bakin ta , nan take duk hankalin mutanan wajen ya dawo gare ta , da sauri wani dattijon da ke zaune kassa geffen mai gari ya taso ya nufe ta ya na tambayar me ya kawo ta nan

Cike da rudu ta ke fadin " Malam lafiya me ya same shi ? "
Bai ba ta amsar tambayar ta ba ya kamo hannun ta su ka juya ya na fadin " kontar da hankalin ki ba abun da ya faru , mu je gida zan fada miki "

Ba musu ta bi bayan shi su ka koma gidan da ta fito , su na shiga ta shiga jero mishi tambayoyi
Sakin hannun ta ya yi kafin ya juyo ya kale ta ya ce " komai ya wuce yanzu , Rabeh ne , ya tarda shi har gida ya yi mishi dukan tsiya wai ya cinye mishi kudin shi , yanzu haka maganar da na ke yi miki sun tafi su kai shi birni wajen yan sanda , shi kuma Issa a na jiran mai magani ya zo ya duba shi , abun da na ke so da ke , ki je gidan shi ki taho da Barira da Hayat tun kafin wani abu ya same su "

" to ai Barira ta na cikin gidan nan " Ta fada mishi
Cike da mamaki ya maimaita abun da ta fada
Gyada mata kai ta yi kafin ta ce " eh , dalilin da ya sa ma na je fada neman ka , Hayat ta tsere ta bar garin nan , ita kuma Barira Issa ya sake ta , malam don Allah ka sa samarin garin nan su tafi neman ta tun wani abu bai same ta ba " ta kai karshen kamar za ta yi kuka

Bayan inallillahi ba abun da malam ke fada , ya na dan zazaro idanu ya ma rasa abun da zai ce
Duk maganar nan da su ka yi a kunnen Barira ta na jin su amma ta ki fitowa sai ma Allah kara da ta ke yi wa Rabeh da Issa
Bari dai mu dan leko Hayat mu gani

TAღRIN ZღCIYA 💖🌺💍

( RETღRN )

(ROMANTIC LUV STORY )💋🔥

❤👑 ꪑꪖꪶꪶꪖƙỉ᭢ ꪖꪑꫀꫀꪹꪖꫝ ꪖꪉᦔꪮꪗꪶꪖꪗꫀ 👑❤

𝗔.𝗞.𝗔 𝐀𝐍𝐈𝐒𝐇❥ 🕊💞

Wattpad : @bennybite

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )

FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks 👍💕

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ️

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMETS SECTION

👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/BoRRwG9bqUFBt4djqzcNbb

DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

𝗧𝗔𝗣 𝗧𝗛𝗜𝗦 𝗟𝗜𝗞𝗘 𝗧𝗢 𝗝𝗢𝗜𝗡 𝗠𝗬 𝗣𝗢𝗦𝗧𝗜𝗡𝗚 𝗥𝗢𝗢𝗠

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i

_________________✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦__________________

[ 🅿🅰🅶🅴̥ 6 ❤🔥 ]

▪NIGERIA ( KANO STATE )

▪HAYAT 💦

Bayan ta baro gidan Bus tafiya ta fara yi saman titi sam ba ta san inda za ta je ba , amma ita ko a jikin ta , sai ma tafiya ta ke ta na cin bread din ta , ta na korawa da ruwa

Har sai da cinye kayan ta sannan ta fara lura da inda ta ke , Dum ta ji gaban ta ya fadi lokacin da idanun ta su ka yi mata arba da wata dankareriar mota da ta yo kan ta da mugun gudu
Chapter 15 · 0% Book details