← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 26

Sashe 7

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yar karamar dariya Vedad ya yi kafin ya ce " Marshal , ba wata Meeting breakfast ne kawai mu ke yi "

Hannu junior ya kai ya dauki Apple ya na fadin " breakfast a karfe 11 ba dan mintina , sai dai ka ce karawa ku ke yi "
Mikewa tsaye Ash ya yi ya dauki laptop din shi ya juya ya shiga bedroom din shi
Mikewa shi ma junior ya yi ya bi bayan Ash ya na fadin " ina zuwa "

Da to su ka amsa mishi a tare kafin Vedad ya ce ma Iqbal " mu je mu yi video game "
Hararrar wassa Iqbal ya yi mishi ya na fadin " kai ba ka da aiki sai game ba ka da exams ne "

Kashe mishi gera guda Vedad ya yi ya na fadin " injustice ? "
Da sauri Iqbal ya ce " ina son Superman "
Yar karamar dariya Vedad ya yi ya na tashi da
Da sauri shi ma Iqbal ya tashi ya bi bayan shi su ka bar part din da gudu , su ka bar kayan breakfast din a nan

Bangaran su Ash kuma , junior na shigowa bedroom din ya isko Ash zaune bakin gadon ya na ci gaba da aikin shi cikin laptop
Geffen shi Junior ya karaso ya zauna ya na kallon abun da Ash ke yi cikin laptop din shi

Yar karamar dariya junior ya yi ya na dafa shoulder din Ash ya ce " kar ka ce min General of American Army Staff Ash har ya fada tarkon soyayya "

Dan karamin tsaki Ash ya yi kafin ya kauda kan shi gefe sannan ya ce " har ka gama shirya wa tafiyar mu ne ? Gobe za mu tafi "
" kar ka damu General ni ko yanzu ne sai mu tafi , amma kai ka na da aiki gaban ka sai a je a rarrashi madam tun lokaci bai kure ba " ya kai karshen ya na bushe wa da dariya

Dan tsaki Ash ya yi ya kai hannu ya dauki pillow da ke geffen shi ya tila ma junior a fuska ya na fadin " girlfriend din Iqbal ce , ina son na samu karin bayani a kan ta idan mun dawo da ga Nigeria , zan sa his excellency ya je neman mishi auren ta "

" okay that's good , to kai fa yaushe za a auren na ka "
Wani dogon nunfashi Ash ya ja sannan ya ajiye laptop din shi saman bedside drawer ya juyo ya kali junior ya ce " duk ranar da ka yi aure , a ranar za a yi na wa " ya na gama fadar haka ya tashi ya nufi dressing room

Da kallo Junior ya raka shi har sai da ya shiga sannan ya sa hannu da sauri ya dauki laptop din Ash ya yi wasu dane dane kafin ya meda ta ya ajiye ya tashi ya fice bedroom din
Ya na fitowa parlourn ya ga tray din breakfast da su Vedad su ka bari
Dan karamin tsaki ya yi kafin ya karaso wajen tray din ya duka ya dauke shi sannan ya fice part din

Kai tsaye Stair ya sauko , tun da ya daura ido kan Ayna ya saki wani kyawatencen murmushi , haka zalika ita ma murmushi ta yi mishi cikin tsokana ta ce " Marshal Junior , ashe ka na nan " dai'dai ya ida sauko stair din

Dan karamin murmushi ya yi ba tare ya ce mata komai ba ya nufi dining room ya ajiye tray din hannun shi saman table din sannan ya juyo ya koma cikin parlourn ya nufi geffen Ayna ya zauna sannan ya rage sautin Muryar shi kassa kassa ya ce mata " ki na ji ko , ki daina kira na da Marshal junior , na san ba za ki iya kiran suna na kai tsaye ba , dan haka ki ce Marshal kawai , ai duk ni ne "

Yar karamar dariya Ayna ta yi , Ummi kuma ta kauda kai gefe dan yanayin face din ta ya sauya ta ji abun da ya ce hakan ya so ya dan sosa mata rai
Shi kuma ko a jikin shi ya na gama fadar haka ya sa hannu cikin aljihun shi ya ciro wayar shi ya fara latsawa
Ba su yi one minute ba wani jibgegen soji ya shigo parlourn , ya na sanye da trouser din shi na soja da T-shirt fara
Kai tsaye junior ya nufa ya sara mishi cikin girmamawa ya ce " good morning Sir "

Ba tare da ya dago kan shi ba ya ce ma sojan nan " okay Felix ! Je ka gyara part din General sannan ka shirya min kaya na , an sauya magana gobe za mu tafi Nigeria "
" Yes sir " wanda ya kira da Felix ya fada ya na sara mishi sannan ya juya ya nufi Stair ya Haye ya nufi part din Ash
Ya na barin wajen Ayna ta mike ta na fadin " Mummy , ni zan koma gida , Haleen tasso ko "

" ayya har za ki koma , Tom shikenan ki gaishe da mijin na wa in kin koma " Nihal ta fada cikin sanyi
Da sauri Haleen ta mike tsaye saman sofar ta kai dan bakin ta saitin kumatun Nihal ta mata kiss ta na fadin " See you Next time mamie " da ga haka ta diro da ga saman sofar ta nufi Ayna da gudu ta na yar dariya

Riko hannun ta Ayna ta yi sannan ta juya ta kali junior ta riko gashin shi da hannu daya har sai da ya saki yar kara ya na fadin " please let me , me kuma na yi miki "
" yi min shiru , wlh ka tabbatar kafin ka dawo da ga Nigeria , ka samo mana sirika "
" Ayna ni kadai ki ka raina wlh , in haka ne ki je ki yi wa Ash hakan , ai shi ma ya isa aure "
" ba ruwan General a nan , ni kai na sani , wlh in ka dawo a tuzuru to sai na yi maka auren dole , ga Ummi a gida , na san za ta bada hadin kai a fitar da brother din ta kunya " ta kai karshen ta na sakin gashin shi ta saki yar dariya

" a'a Ayna gaskia Junior di na ya fi karfin Ummi " Nihal ta fada ta na kallon Ummi ta kassan ido
Murguna ma ta baki Ummi ta yi ba tare da ta ce komai ba
" mummy sai an jiman ku " Ayna ta fada ta na fara takawa za ta bar parlourn
A tare Junior da Nihal su ka daga murya su na fadin " ki gaishe da gida "
Da to ta amsa musu ta na sa kai ta fice war ta
Ta na fita Nihal ta kali Ummi ta ce " yanzu Ummi ba za ki raka ta ba "
" zuwa ina ? " Ummi ta fada cikin ko in kula kafin ta mike ta fara takawa ta Haye stair abin ta
Da kallo Junior da Nihal su ka rakata , har sai da ta Haye sannan ya ida konta wa saman sofar ya na ci gaba da latsa wayar shi

Ya na a haka ya jiyo Muryar Nihal ta na fadin " Junior , wai yanzu kai ma Ash za ka bi ku mutu a tuzurai kenan , ba ka da aiki sai latsa waya "
A hankali ya juyo ya kali Nihal ya saki wani dan karamin murmushi ya ce " mummy , ni fa ina son na yi auren , matar ce wadda ba ke so , she is not muslim kin ga ba zan iya auren ta ba , shi kuma Ash ba matar ba ce bai samu ba , sam sha'awar mace ce ba ya yi , kar ki so ki ga yan matan da ke bin shi har headquater da sunnan su na son shi da ga musulman har krista , wlh akwai yarinyar da ta baro UK kawai dan ta gan shi , kuma yarinyar president din UK ce fa, ko last week sai da ya sa wata officer ta yi wa wata yarinyar dukan tsiya kawai dan ta rungume shi , kar ki so ki gani har yanzu yarinyar ta na Asibiti "

Dan karamin murmushi Nihal ta yi ta na dan sunkuyar da kai cikin zuciyar ta ta ce " dole mata su so shi , mahaifin shi ma haka ya ke farin jini wajen yan mata " ba ta kai karshen maganar ta ba idanun ta su ka ciko da hawaye , da sauri ta tashi ta koma part din ta

Shi dai Junior da kallo ya rakata har sai da ta shiga sannan ya mike zaune ya na shirin tashi , Vedad da Iqbal su ka sauko stair a guje
Dan karamin tsaki ya ja cikin ranshi ya ce " yaran nan wlh horon soja zai dace da ku " ya na gama fadar haka ya dago ya kali su Vedad dai'dai sun karaso cikin parlourn ya daka musu ya na fadin " Vedad, Iqbal mazza ku zo nan "

Cak su ka tsaya da gudun su , su na dan zaro idanu su na kallon shi , sun san halin junior ba karamin maketaci ba ne , musaman in ba ya gaban idon Ash
Wasu yawu su ka hadiye a tare kafin su daga kafa su ka nufe shi
Tun kafin su karaso ya nuna musu gaban shi da yatsa allamun su yi kneel down
Ba musu su ka karaso gaban shi su ka yi kneel down , Vedad sai turo dan bakin nan na shi ya ke ya na shagwabe fuska

Sai da junior ya dauki wajen good ten minutes ya na kare musu kallo ya na daure fuska sannan ya ce musu " wai ku ba ku iya zama waje guda ba , yanzu fada min , gudun me ku ke yi haka sai ka ce wasu babys "
Chapter 7 · 0% Book details