← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 26

Sashe 16

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

A razane ta saki wata irin razananiyar kara ta na sakin kumshin kayan ta , ta na toshe kunnuwan da duka hanayan ta biyu ta lumshe idanun ta , ta na jiran motar nan ta buge ta , Amma sai ta ji shiru

Slowly ta bude idanun ta , ta na kallon kassa sai ganin tayoyin motar nan ta yi dab da kafafun ta ,
A hankali ta dago kan ta , idanun ta ba su sauka ko ina ba sai saman wata kyakyawar mace , sanye cikin wani tsadaden lace milk colour ya na da ratsin baki , an yi mata babban dinki , ta yi daurin dan kwalin ta irin wannan no respect , ko gyale babu a jikin ta , ta yi uban make up , abun har ya ba ka tsoro amma ya yi mata kyau over , a shekaru za ta kai 40 haka , amma da ga ganin fatar jikin ta , ta na samun hutu irin wadanan manyan hajiyoyin

A hankali ta dafa shoulder din Hayat ta na fadin " daughter ba ki ji ciwo ba dai ko ? "
Gyada mata kai Hayat ta yi allamun a'a
Kallon Hayat matar nan ta yi da ga sama har kassa , sannan idanun ta su ka sauka kan kumshin kayan ta , nan take ta saki wani kyawatencen murmushi , ta kai hannu ta dauko kumshin kayan ta , ta riko hannun ta ta na fadin " shikenan mu je na rage miki hanya "

Ita dai Hayat da ido kawai ta ke bin ta , ta kassa cewa komai
Haka matar nan ta bude kofar wajen mai zaman banza ta ce ma Hayat ta shiga , ba musu ta shiga sannan matar nan ta rufe kofar , ta bude gidan baya ta saka kayan ta , sannan ta ragayo ta shiga mazaunin driver ta tada motar su ka bar wajen

Sai da su ka dan yi nisa sannan matar nan ta kali Hayat ta ce " ya sunan ki daughter "
Wasu yawu Hayat ta hadiye kafin ta ce " Hayat "
Gyada kan ta matar nan ta yi ta na dan tabe baki sannan ta ce " shikenan Hayat , ina zan sauke ki ? " ta fada ta na kallon ta ta wutsiyar ido

Dan sunkuyar da kai Hayat ta yi ba tare da ta ce komai ba
" a'a daughter lafiya , ba ki fada min ba , kar na wuce gidan na ku " matar nan ta fada cike da damuwa

A hankali Hayat ta bude baki kamar za ta yi kuka ta ce " guduwa na yi da ga gidan mu , kuma ba zan koma ba "
" asha , ki yi hakuri ki fada min ina ne gidan ku , saboda ba garin nan na ke ba , kaduna zan wuce , ba zan iya tafiya da ke ba "
Nan take Hayat ta fashe da kuka ta na girgiza kai ta ce " don Allah ba zan koma gida ba , auren dole su ke son yi min , ni zan bi ki don Allah kar ki meda ni "

" yanzu in su ka shiga neman ki , a ka gan ki tare da ki za qu ce sato ki na yi don Allah ki yi hakuri ki fada min , kar ki janyo min matsala "
" babu wanda ya san na taho kuma , kuma ba da garin nan na ke ba , da ga Niger na ke , babu wanda ya san nan na taho "

Parking motar ta matar nan ta yi geffen titi sannan ta juyo ta kali Hayat ta ce " shikenan , zan tafi da ke kaduna da sharadin bayan sati guda zan meyar da ke gidan ku "

Da sauri Hayat ta gyada mata kai ta ce " eh eh na yarda "
Dan karamin murmushi matar nan ta yi kafin ta zaro handkerchief guda ta mikawa Hayat ta ce ta goge hawayen ta , ba musu Hayat ta kai hannu ta karba ta fara goge hawayen ta

Ta na karba matar nan ta juya ta tada motar ta su ka bar wajen

▪ KADUNA

▪ASH 🔥

Zaune ya ke cikin parlourn part din shi , da ga shi sai short da singlet , ya daure wanan lalawsan gashin kan shi a baya ya sako wasu dan sirarren a gaban goshi , sai baza kamshi ya ke yi , ya kurawa Tv gaban shi ido babu ko kiftawa

Ya na a haka Iqbal ya shigo parlourn ya na sallama kassa , ya karaso geffen Ash ya zauna

Ba tare da ya juyo ba Ash ya ce mishi " What's wrong with you , tun da safe na ga sai kai kawo ka ke yi "

Dan karamin tsaki Iqbal ya yi kafin ya ce " Big bro , Wai me ya kawo mu Garin nan , ba mu yi ten hours ba da zuwa amma har na yi wanka shidda , saboda zafi "

" and ? " ya fada a takaice
" kamar ya and ? Ina fada maka zafi na ke ji ka ce min and , so ka ke sai na mutu " Iqbal ya fada kamar zai yi kuka

" ni na san ba zafi ba ka ke ji , fada min gaskiya , ita ce ta fada maka ka dawo ko "
Dan zaro idanu Iqbal ya yi , baki sake ya ke fadin " how did you know ? "
" ka na kewar ta ne ? " Ash ya tambaye shi

Dan kontar da kan shi ya yi saman shoulder din Ash ya ce " sosai ma , i don't know why duk lokacin da na rufe ido ina tuna........ " shiru ya yi ya kassa kai karshen maganar shi

Slowly Ash ya juyo ya kale shi , da sauri Iqbal ya kauda kai gefe ya na musurai da idanu
" why ka yi shiru ida maganar ka " Ash ya fada dan ya gane abun da ya ke son cewa

Da sauri Iqbal ya tashi ya na shirin fita dakin , amma bai yi taku daya ba , Ash ya riko hannun shi cak ya janyo shi da karfi ya dawo ya zauna inda ya taso
Cikin tsare gida Ash ya ce mishi " za ka kai karshen maganar ka , ko sai na fido shi da karfi "

Kukan shagwaba Iqbal ya shiga yi mishi ya na fadin " uhmm uhmm , Ni fa ba abun da zan ce "
" Shut up , ba na haka yi min wannan shirmen ba "
kunbure fuska Iqbal ya yi ya na turo dan bakin nan na shi
ya na shirin magana Ash ya riga shi cewa " Oya stanp up ka fara Frog jump "

dan zaro idanu Iqbal ya yi ya na fadin " Frog jump ? no , Really big bro frog jump sai dai Vedad ni na girma " ya kai karshen ya na kauda kai gefe

gyada kan shi Ash ya yi kafin ya ce " gaskiya ne , dole ka ce ka girma ka fara jin kamshin mace ba dole ba , za ka tashi ka fara ko sai na "

dan karamin gunguni Iqbal ya yi kafin ya tashi , ya koma tsakiyar parlourn ya tsuguna ya fara frog jump , ya san duk lokacin da Ash bai kai karshen maganar shi ba to ba da wassa ya ke ba , yanzu in ya ce ba zai yi ba , wlh dukan tsiya zai yi mishi kuma ba me raba su gidan nan

sai da ya dauki wajen good ten minutes ya na frop jump ko sannu Ash bai ce mishi ba
su na a haka Vedad ya turo kofar Parlourn ya shigo ya na sallama
ya na ganin Iqbal na frop jump ya bushe da wata shegiyar dariya , ya nufi sofar da Ash ke zaune ya zauna geffen shi ya na ci gaba da dariyar shi har da dafe ciki

wata muguwar Hararra Iqbal ya wurga mishi cikin zuciyar shi ya na fadin " za mu hadu waje "
kamar ko Ash ya san abun da ya fada cikin zuciyar shi sai ya ce mishi " Babu inda za ku hadu , ka na taba shi sai na yi maka dukan kawo ruwa "

turo dan bakin shi Iqbal ya yi wai shi ya ji haushi
a hankali ya mike tsaye ya na kallon Ash ba tare da ya ce komai ba
daga mishi gera Ash ya yi allamun minene ?

murguna mishi baki Iqbal ya yi kafin ya nufi hanyar fita parlourn da gudu
a dubu dari Ash da Vedad su ka mike a tare su ka bi bayan shi

da gudu Iqbal ya shige part din shi ya wuce bedroom , ya turo kofar ya na shirin rufe ta Ash ya damko ta da hannun shi , Vedad ya shigo cikin dakin ya rungumo shi ta baya ya na fadin " Big bro , ga shi na riko shi "

sakin kofar Ash ya yi ya shigo bedroom din sannan ya tura kofar ta rufe kan ta sannan ya danna wani button a jikin ta , a hankali ya juyo ya bai ce ma Iqbal komai ba , ya nufi bed din shi ya dauko pillow guda biyu sannan ya dawo ya ce ma Vedad " sake shi " ya kai karshen ya na mika mishi pillow guda

cike da mugun ta Vedad ya riko pillow su ka fara bugun Iqbal da shi
bawan Allah sai kara ya ke ya na fadin su kyale shi , amma ina Vedad an samu mugun ta , shi dama Ash ina ruwan shi bai san ragowa ba ko kadan

da gudu Iqbal ya nufi bed din shi su na biye da shi su na bugun shi ya dauki dayan pillow shi ba ya shiga ramawa , ya na yar dariya shi da Vedad
Ash kuma ya na ganin su na dariya shi da Vedad ya daina bugun Iqbal ya koma saman bed din ya zauna ya na ci gaba da kallon su , su na wassan su kamar kananan yara
Chapter 16 · 0% Book details