← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 26

Sashe 2

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali wata kyakyawar budurwa ta ke sauko wani stair mai mugun kyau zagaye da glass ba dan kar ku ce na yi karya ba da sai na ce stair din da kan shi na glass
Kyakyawa ce ajin farko fara kal da ita kamar ka taba jini ya fito da ga gani kassan renon madara da ice cream ne , ta na kama rai da rai da Aylan kamar an tsaga kara sai dai idanun ta tak irin na Nihal ne
Ta na sanye da mini skert dai'dai guyiwa pink colour , da wata t-shirt White colour da kadan ta wuce cibi ta daura wata jacket pink colour ita ma , ta saka wasu sneakers farare kal kamar ba kassa a ke takawa da su , ta na rataye da wata yar bag a shoulder hannu ta rike da wata dankareriar waya golden colour har wani shining ta ke , dayan hannun kuma ta na rike da wata coat Fara

Sai da ta gama sauko stair din ta na tafiyar kamar da ga saman ta jiyo Muryar wata mata ta na fadin " ke ke , ummi ina za ki je da wadanan kayan haka ? " ta fada da turanci

Cak budurwar nan ta tsaya ta daga kai sama ta na lumshe idanun ta a hankali kafin ta sake bude su slowly ta juya ta na kallon matar da ke tsaye a bayan ta

Ba kowa ba ce face Nihal , ta na sanye da wata Abaya sky blue colour mai mugun kyau ta yi Rowling veil din ta , ta na nan yadda ta ke ba abun da ya sauya na ta , sai dan shekaru da su ka ja dan gaskia yanzu an dan lattijantaka amma duk da haka ta na nan kamar yar shekara 20 don gaskia jikin ta ya na samun kula , har wani haske skin din ta ya kara ta zama kamar baturiya

" mummy , me kaya na su ka yi kuma da za ki tseda ni , zan yi late a wajen aiki " ummi ta fada ta na marairaice fuska

Tsuke fuska Nihal ta yi ta na nuna ta da yatsa ta ce " ke Ummi wlh ki kiyaye ni , maza koma ki canza min kayan nan "

Dan bubuga kafafun ta kassa ta yi cikin shagwaba ta ce " haba mummy ni fa ba yarinya ba ce da za ki ce sai kayan da ki ke so zan saka , shekara daye daye daye har 29 gare ni ina cikin ta 30 amma kullum kamar baby ki ke dauka ta , ya ishe ni haka "

Takowa Nihal ta yi ta tsaya dab da ita ta ce " Ummi ke fa ba yarinya ba ce yanzu har shekara 29 ba ki da saurayi tsayaye bare a yi zancen aure , na lura da ke da yan uwan ki duk ba ku son zancen , wai sai kun tsufa kun zama kamar ni za ku yi auren ne , kin san dai da wannan shekarun na ki da wuya ki samu mijin aure a nan kusa ba , ko yaron uncle Junaid da ya zo ganin ki sai da ki ka sakin mishi karnuka ya bar gidan ba shiri "

Da sauri Ummi ta katse ta da cewa " Mummy , Mummy , ya isa please ni na ce miki ina da bukatar mijin aure ne , I don't need man over me , it's never my priority , dan haka ki bar min zancen wani aure , amma kin san wani abu , duk ranar da Big bro ya yi aure , ni ma a yi nawa a ranar ai dama tare mu ka shigo duniya " ta kai karshen ta na yar dariya ta juya za ta bar wajen

Da sauri Nihal ta ce mata " ki dawo ki sauya kayan nan na ce miki " ta kai karshen da dan karfi

Ba tare da ta juyo ba ta daga mata hannu ta na fadin " sai na dawo Mummy , I love you " ta kai karshen ta na ficewa falon

Da kallo Nihal ta rakata har sai da ta bar wajen sannan ta yi dan karamin murmushi ta na girgiza kai ta juya ta koma inda ta fito

* MISALIN KARFE 9 NA YAMMA

Zaune mutanan gidan su ke cikin wani makeken dining room , dauke da wata dining table mai bala'in kyau fara kal mai kujeru 10 duk kujerun kuma farare ne
Table din shage ta ke da kayan cima , da ga snacks , fruits , juice , water , abinci kala kala
Cen na hango Ummi zaune saman chair din ta ta na faman latsa waya , ga wasu samari guda hudu , sai wani babban mutun da ke zaune ya na kallon su , kallon daya na yi mishi na gane Rayan ne
Duk da yanzu shekaru sun ja , ya dan lattijantaka , ga kuma kyasumba da ya tara amma har yanzu ya na nan yadda ya ke , har wannan murdaden jikin nashi

Cen kuma na hango wani kyakyawan sauri ya na zaune geffen daman Rayan
Kamanin shi sak Aylan , kamar an tsaga kara har wadanan sexy blue eyes sak iri daya , da wannan darck black curly hair din na shi kai har wannan murdaden jikin , ni da farko na zata Aylan din ne , tabass little ne wannan
A hankali ya dago kan shi ya kali Ummi da su ke fuskantar juna ya ce mata " Ummi je ki kira mummy har yanzu ba ta fito ba " ya fada kamar an yi mishi dole

Ko dago kai ba ta yi ba ta kale shi bare ta yi abun da ya ce mata
Shi dai ya tsare ta da wadanan sexy blue eyes din na shi babu ko kiftawa
Ya na shirin magana Rayan ya mike da saman chair din shi ya na fadin " ku bari jan je na kira ta " ya kai hannu ya na fara takawa ya fice dining room din

Ya na barin wajen wani saurayi da ke zaune geffen little ya ce " mutun sai son girma kamar dollar , wannan girman ka bar shi a headquater , a nan akwai wanda su ka girme ma ka "

Slowly little ya mike tsaye ya mika ma Ummi hannu ya ce " please come with me "

Ba musu ta mike tsaye sannan ta zagayo ta geffen shi ta daura hannun ta saman na shi su ka bar dining room din a tare
Ya rage su uku , junior da wasu samari biyu da su ka sunkuyar da kan su ban iya ganin face din su gaskia

Kai tsaye dakin da Nihal ta shiga da safe su ka nufa
Su na shigo part din ko , Rayan ya shiga bedroom din
Su na shigowa ya kali Ummi ya ce " yi shiru ki saurara " ya kai karshen ya na sakin hannun ta , su ka karaso bakin kofar bedroom din su ka yi tsaye

Bangaran Rayan kuma ya na shigowa bedroom din ya na sallama kassa kassa
Nan ya ga Nihal zaune bakin gado ta na rike da wata laptop ta na faman hawaye bibiyu kamar an bude fanfo

Slowly Rayan ya karaso ya zauna geffen ta ya sa hannu ya amshe laptop din ya ajiye geffen shi ya sa hannu ya talabo face din ta ya na fadin " Sister , wai sai yaushe wannan abun ne zai kare ? Ba ki gajiya kullum ki shigo daki ki yi ta kuka ke kadai "

A hankali wani siririn kuka ya kubce mata ta na fadin " yaya Rayan ba zan iya ba , na kassa wlh , why zai tafi ya bar ni , why mutuwa za ta min haka me na yi mata , ji na ke kamar na kashe kai na , na huta , rayuwa babu shi sam ba rayu ba ce a waje na , yanzu ya tafi ya bar ni har abada kenan "

A hankali Rayan ya kai hannun shi ya janyo ta jikin shi ya rungume ta ya na fadin " ya isa haka sister please , ki daina cutar da zuciyar ki , yanzu inda ya san halin da ki ke ciki ya ki ke tunanin zai ji , in su Ummi su ka gan ki cikin wannan halin me za ki ce musu "

Da sauri ta katse shi da cewa " su ma cikin wannan halin su ke , na san su na kewar Daddyn su sosai , amma na kassa maya gurbin shi a rayuwar su , na kassa rike amanar da ya bar min , ya ka ke tunani in ya San halin da Ummi ta ke ciki , ka fi kowa sanin ita ce sanyin idaniyar shi , ko cikin yaran mu ya fi son ta fiye da kowa ne , amma yanzu duba irin halin da ta dauko , Sallat ma sai na dinga sa ta a gaba ta na yi , na san ko da ya na raye , idan ya ga yadda ummin shi ta zama na san sai zuciyar shi ta buga , duk laifi na ne , na kassa ba su tarbiyar da ta dace , ya bar min abin da ya fi mishi komai daraja a rayuwar shi amma ni na watsar da ita , yaya Rayan ji na ke kamar na mutu ni ma na tarda shi in da ya ke "

A hankali little ya turo kofar dakin ya shigo ya na fadin " mummy ke ma tafiya ki ke son yi ki bar mu ? "
Chapter 2 · 0% Book details