← Book details Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 26

Sashe 1

Taurin Zuciya Return Complete Hausa Novel · about 8 min read



TAღRIN ZღCIYA 💖🌺💍

( RETღRN )

( ROMANTIC LUV STORY )💋🔥

❤👑 ꪑꪖꪶꪶꪖƙỉ᭢ ꪖꪑꫀꫀꪹꪖꫝ ꪖꪉᦔꪮꪗꪶꪖꪗꫀ 👑❤
𝗔.𝗞.𝗔 𝐀𝐍𝐈𝐒𝐇❥ 🕊💞

Marubuciyar littafin
TAURIN ZUCIYA
EXILED PRINCE ( LOVE MEETS POWER )
TWO LIGHTS ( YAR JARIDA )
and now TAURIN ZUCIYA ( RETURN )

Dedicated to me first 😎💜👌 and all of Army 💜🕊

Wannan littafin sadaukawar ne ga Fatimah Zarah Musa , Khadija Sabi'u ( Nainarh Nkd's ) , ga sister di ta Walee 😄😄 , da wa kuma 🤔🤔🤔🤔 ? ? ? ? , tom su na dayawa gaskiya 😂😂
Amma zan so ku sani ina godiya sosai da irin gudun mawar da na ke samu da ga gare ku , comment , sharing , duk ina godiya , Allah ya saka 🙏🙏

GARGADI !!!!!!!!!!!!!!!

* ban yarda ba wani ko wata ta sauya min ko guntu a cikin abin da na rubuta ko ayi audio da shi , i dan kuma na fadin wani abu ba daidai ba a cikin littafin ku yafe mun , duk wanda ya zage ni kuma ko yayi mun mumuna fahimta to cen ta matse mishi ni ba ruwa na 😎😎 *

FOR MORE INFORMATION KU TABO WANNAN NUMBER +22798999753 WHATSAPP ONLY , Thanks 👍💕

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ️

BY : 𝔸𝑵Ɩ𝘚Η 👑❤ ( 🄼🄴🄴🅁🄰🄷 ...... ❦)

Wattpad : @bennybite

DOMIN SAMUN BOOK DI NA DA GA FARKO ZA KU IYA ADDING CHANEL DI NA TA WANNAN LINK

👇👇👇👇👇👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i

TAP THIS LINK TO JOIN MY WHATSAPP GROUP COMMETS SECTION

👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LWmuu0yv6C9DAhpdepDb4i

𝗧𝗔𝗣 𝗧𝗛𝗜𝗦 𝗟𝗜𝗞𝗘 𝗧𝗢 𝗝𝗢𝗜𝗡 𝗠𝗬 𝗣𝗢𝗦𝗧𝗜𝗡𝗚 𝗥𝗢𝗢𝗠

👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/LepRstkGv3sDf8Jj4Gm054

_________________✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦✦__________________

[ 🅿🅰🅶🅴̥ 1 ❤🔥 ]

BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

AFTER SOME YEARS 🤧

NA SAN A NAN KOWA ZAI TAMBAYE NI ME YA FARU DA WANNAN AHALIN TOM NI MA BAN SANI BA SABODA BA NA NAN BARE NA YI RAHOTO , AMMA DAI NA SAN BABY TA RASU SEVEN MONTH BAYAN RASUWAR BIBI WAJEN HAIHUWA DA ITA DA BABYN TA DUK SU KA KOMA GA ALLAH , A RANAR SAI DA RAYAN YA YI ZAUNE YA NA KUKA KAMAR KARAMIN YARO , KO ONE MONTH BA A YI BA DA MUTUWAR TA YA TAFI WATA MISSION HAR YA SHARE WAJEN GOOD EIGHT YEARS BABU SHI BA MAI KAMA DA SHI , NIHAL KUWA TA CI GABA DA KULA DA JUNIOR

A CIKIN SHEKARUN NAN TAKWAS DA RAYAN BA YA NAN ABUBUWA DAYAWA SUN FARU A CIKI HAR DA RASUWAR DADDY , ANIR KUMA YA TATTARA FAMILYN SHI YA KOMA UK DA SU , ANAS KUMA SU KA KOMA DUBAÏ TARE DA UMMA SU KA BAR NIHAL DA AYLAN KADAI A US BAYAN SHEKARA BIYAR DA KOMAWAR SU DUBAÏ ITA MA UMMA TA RASU

IDAN MU KA LEKO YARAN KUWA BAYAN LITTLE YA CIKA SHEKARA TAKWAS AYLAN YA FARA BA SHI HORON SOJA , BA ROKON DA NIHAL BA TA MISHI BA A KAN YA BARI YA KAI SHEKARA 15 AMMA FIR YA KI YARDA , BA YADDA ZA TA YI SAI SA MUSU IDO , TA NA JI TA NA GANI YA MEDA KARAMIN YARO KWARAREN SOJA , DA GA HARBIN BINDIGA HADA BOMBS , FADA DA MAKAMI HAR DA HANNU DUK SAI DA LITTLE YA KOYE SU KAFIN MA YA CIKA SHEKARA GOMA
BAYAN YA CIKA SHEKARA GOMA SHA BIYAR YA DAUKE SHI TARE DA JUNIOR YA KAI SU MILITARY CAMP SU KA FARA KARBAR HORON SOJA A TARE SU NA A HAKA HAR RAYAN YA DAWO DA GA MISSION DIN SHI , DA FARKO YA SO YA YI JA A KAN HUKUNCIN AYLAN NA KAI SU MILITARY CAMP HAR MA YA JE DAWO DA SU AYLAN BAI SANI BA , AMMA FIR LITTLE DA JUNIOR SU KA KI YARDA SU KOMA A BAR ZANCEN LITTLE FUSKAR MAGANAR MA BAI BAYAR BA DAN YANZU MISKILANCIN YA FI NA FARKO GA WATA ZUCIYA DA YA DAUKO , KO AYLAN YA KAWO MISHI ZIYARA BA YA KULA SHI KAMAR BA MAHAIFIN SHI BA
NIHAL DAI TA NA GEFE TA NA KALLO BA TA DA IKON YIN MAGANA , TA NA CEN TA NA FAMA DA IQBAL GA KUMA SABON BABY DA SU KA SAMO WANDA YA CI SUNAN VEDAD YA NA KAMA DA AYLAN SAI DAI KANANAN IDANUN GARE SHI SKY BLUE EYES IRIN NA MAHAIFIN SHI GA KUMA JARABAR UMMI GEFE DAN AYLAN YA BI YA SANGARTA TA KO YARINYAR PRESIDENT BA TA GWADAWA UMMI SANGARTUWA DAN DUK CIKIN YARAN SHI YA FI SON UMMI SAI VEDAD

BAYAN SHEKARUN UKU AYLAN YA NEMI TAKARAR SHUGABAN KASSAR US KUMA CIKIN SA'A YA LASHE PRIMARY ELECTIONS
TWO WEEKS BAYAN PRIMARY ELECTIONS , A KA DASA BOMB A CIKIN MOTAR SHI YA FITO DA GA HEADQUATER DIN SU MOTAR TA TASHI DA SHI A CIKI KO KASHIN SHI BA A SAMO BA KUMA HAR ZAMAN YANZU BA A SAMO WANDA YA YI WANNAN AIKIN BA
NIHAL HAR DOGUWAR SUMA TA SHIGA , SAI DA TA SHARE ONE YEAR CIKIN DOGUWAR SUMAR TA BA TA FARFADO BA
DUK WANI BINCIKE DA RAYAN ZAI YI SAI DA YA YI SHI AMMA BAI GANO WANDA YA YI HAKAN BA , BA YADDA YA IYA HAKA YA RUNGUMI SORRY YA CI GABA DA KULA DA YAR UWAR SHI , DA KUMA YARAN BIG BRO DIN SHI SPECIALLY VEDAD DAN A LOKACIN BA ZAI WUCE SHEKARA BIYAR YA YI DUK WANI KOKARI DA ZAI YI DAN GANIN BAI JI KADAICIN MAHAIFIN SHI BA

DUK ABUN NAN DA YA FARU LITTLE DA JUNIOR SU NA CEN A MILITARY CAMP BA SU FITO BA KO AN BA SU DAMAR TAFIYA GIDA SAI DAI JUNIOR YA TAFI SHI LITTLE BA YA TAFIYA A HAKA HAR SU KA CIKA SHEKARA 25 BAYAN YA KAMALA TRAINING DIN SHI
SU NA FITOWA KO RAYAN YA ZAMA PRESIDENT OF UNITED STATES BABU WANDA BAI YI MAMAKIN HAWAN SHI KUJERAR PRESIDENT LOKACI GUDA HAKA DAMA CIKIN DUHU YA YI AIKIN SHI GUDUN KAR A MISHI IRIN NA AYLAN
A HAKA YA MEDA LITTLE MILITARY CAMP INDA ZAI FARA KARBAR SABON TRAINING NA ZAMA THE GENERAL OF AMERICAN ARMY STAFF , JUNIOR KUMA HIS MARSHAL
BAYAN SHEKARA UKU YA FITO A MATSAYIN GENERAL OF AMERICAN ARMY STAFF A SHEKARA 28
IDAN AYLAN YA YI TAURIN ZUCIYA LITTLE YA CE MISHI BA KA SAN KOMAI BA , DAN RAYAN SAI DA YA FARA NADAMAR MEDA SHI MILITARY CAMP DA YA YI
HMMMM NI DAI ABUN DA NA SANI KENNAN YANZU BARI MU SHIGA LABARIN MU

▪UNITED STATE

( WASHINGTON DISTRICT DE COLUMBIA )

wani makeken gidan ne , wannan ya yi kadan a ce mishi makeke dan unguwa guda ce wannan gidan kofar shi ma kadai abun kallo ce
Tu da ga farkon layin gidan wasu jibga jibgan sojoji ko wane rike da manyan bindigu , su na tsatsaye kamar an dassa su a wajen fuskokin su a daure tamau kamar hadari

Da ga cikin gidan kuma harabar gidan ma kadai ta isa a gena madaidaicin gidan har ashirin dan ba karamin fili ba ne ni gaza ganin karshen shi ma na yi
harabar gidan Cike ta ke sojoji kowane rike da gun sai kai kawo su ke
A geffen dama wani makeken parking space cike da motoci 50 ma albarka dan na kassa kirga su , da ga gani kuma ba kananan motoci ba ne dan guda dai ma sai ta sayi gida sukutum , ko wace colour akwai har golden , grey , pink

Dan nesa kadan da parking space din wani Filin wassan ball ne mai mugun girma , geffen shi wata yar Runfa ce shake da chair kamar dai irin na Stadium , a bayan su kuma akwai wani closet dauke da ball kala kala , na football , basketball , handball , baseball da bat din su , gloves irin na box da wasu sanduna bakake

Ka na fitowa parking space wata doguwar hanya ce zagaye da ciyayi da flowers mai mugun kyau
Daguwar hanya ce , a kila ka yi tafiyar minti biyar kafin ka iso wani tanpasheshen building mai hawa uku Fari kal da shi , a hawa na ukun akwai wani katon balcony , idan ba ka hau ba ba ka iya ganin abunda ke cikin balconyn , duk wasu Windows na wajen na glass ne

Wata kofar ta glass na nufa wadda za ta sada ka da parlourn gidan
Ka na isowa bakin kofar wata wuta blue ta ke fitowa ta yi scanning da ga sama har kassa kafin kofar ta bude slowly da kan ta
Wani irin sanyi ne mai mugun dadi da kamshi zai fara kai ma ka karo kafin ka shiga cikin gidan ma

A hankali na daga kafa na shiga wajen nan na ga abun da ya fi karfin alkalami na , dan ya yi kadan ya fada muku abun da na gani , wannan wajen sai dai a kira shi da aljannar duniya baki daya ma

Komai na cikin wajen da ga sky blue da navy blue sai white colour abun ba karamin kyau ya kara mishi ba
( Ni dai ba zan iya fada muku abun da na gani ba gaskia 😴 ku bari idan mu ka tsunduma cikin labarin za ku ga yanayin gidan yawwa 😌🤙)
Chapter 1 · 0% Book details