← Book details Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 20

Sashe 9

Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya nuna mata wayar da za ta kira in tana bukatar wani abu. Hajiya kasa shiga bandakin ta yi, ta zauna bakin gado ta zuba tagumi tana mamaki, ba wai don ta raina muhallin da aka kawo ta ba, a'ah, mamakin canzawar Laila ta ke farat daya kamar wadda tunda aka haife ta cikin rayuwar da ta ke kenan. Ba ta yi mamakin karbar da ta yi musu ba, tunda da ma masu iya magana sun ce, da ka zama uwar Gwamna gara ka haifi matar Gwamna. Amma anya fisabilillahi ita din ta cancanci tarbar da ta yi mata? Ina ta kuskuro a kan yarinyar nan, da me ta rage ta tun bayan da ta hada aurenta da Ma'arouf? Na kulawar suruka ga surukarta? Da ta yi mata wannan tarbar da bakon da ba ka sani ba za ka yi wa? Lallai mulki akwai giya a cikinsa. Ta tuno rayuwarta da A isha Babar Amina, wadda nata dakin shine masaukinta, sai hawaye suka sakko mata shar-shar! Ta kwance habar zaninta tana sharewa. Ba za ta iya tafiya ta bar Amina a hannun wannan yarinyar ba, sai dai Baba Liman ya hakura da auren nata. Da wannan ta mike tsaye, sai ta ji jiri ya kwashe ta ya mayas, ta koma ta zauna da sauri tana fadin. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel'. Har ta ji komai na jikinta ya koma daidai. Ta shiga bayin ta dauro alwala ta samu wuri ta rama sallolinta a zaune, don ta kasa tsayuwar sabida bacin rai da motsuwar zuciya. Ta bude jakarta karama ta dauko (panadol) ta sha da ruwan da ke cikin firij. Bayan mintina goma ta ji karfin jikinta ya dawo, ta dauki Amina ta shiga bayi da ita, ta hada ruwa mai dumi ta tsarkake ta ta yi mata wanka fes, ta fito da ita ta shafe ta da mai, ta sanya mata kaya da sabuwar pampas, ta ja ta jikinta suka kwanta a gado, don huta gajiyar zaman mota da suka kwaso. Tana ta jan carbinta tana hailala. Fadi take cikin zuciyarta.... Allah ya sa ba zaben tumun dare ta yi wa Ma'arouf ba, don ta san halinsa kowanne hali yake ciki ba zai fada mata yana da damuwa a kan kowa ba balle iyalinsa. Sai dai ita ta ganewa idanunta. Karfe goma na dare ya shigo gidan a matukar gajiye. Ko ruwa bai sha ba, ko zama baiyi ba don ya huta, sabida zuwan Hajiya da Amina da ya tura a dauko su yau yana makale a ransa. Laila tuni ta kule a (bedroom) dinta ko dai ba ta yi bacci ba, to ta kashe fitila ta yi linkim a gadonta na alfarma, shigowarsa kawai ta ke jira. Da shigarsa falo ko zama a kujera bai yi ba ya kunna wayarsa ya kira Hajiya, shi kansa ya san da kyar zai same ta a waya daidai wannan lokacin, don da ta yi isha'i ta ke kashewa sai gobe kuma. Ya kira sau uku tana kashe. Ya shiga sauran dakunan da falon ya kunsa wanda dukkansu (self-content) ne, bai gansu a ciki ba. Ya kira direban da ya dauko sun. Da sauri Akilu ya daga. "Ka dauko Hajiya da Amina kuwa?" "Ranka ya dade na dauko su tun da yamma, na kawo su har falon uwargida". "To ya ya aka yi ban gansu ba? Duka dakunan nan, na sassan nan ba sa cikinsu". Akilu ya rasa me zai ce? Shi dai ya san ya damka su hannun uwargida, daga nan kuma ya fita, ya gama aikinsa. Jin Akilu bai ba shi amsa ba, ya gane ba shi da abin ce masa, tunda ya ce ya damka su a hannun matarsa. Shi sai a lokacin ma ya tuno da ita, sau tari yana mancewa ya ajiye mace a gidansa, sabida amfanin Laila kalilan ne a cikin rayuwarsa. Ita kanta ta san hakan, amma ba ta damuwa, to saboda Allah me zai dame ta? Duk wani burin 'ya mace ta same shi a rayuwarta har wanda ba ta taba mafarki ba. Me ye nata na shisshigi a inda ya nuna ba ya bukatarta? Da sauri ya juya ya shiga dakin nata. Ta kashe fitila mai haske ta bar mai duhu, koriya sharr, ta yi linkim cikin ni'imtaccen bargo a dankareren gadonta. Ita kanta katifar gadon tausa ta ke yi mata. Ya kunna fitila, dakin ya mamaye da haske. Ta dan fiddo kanta daga cikin bargon tana kallonsa, a zuciyart ta ce, "Yau ina da amfani, ga shi kuma ba za a samu abin da ake nema ba, hutawa nake son yi'. Don ita har ga Allah ta manta da wata Hajiya balle rami-ta-ki-gawar 'yarsa. Akasi ga tunaninta, abin da ya tambaye ta daban ne, cewa ya yi, "Ina Hajiya da Amina?" Ta dan baiwa kwakwalwarta aiki na wucin gadi, aikin tuno mata wadanda yake nufi da gaggawa. A take ta tuno mata, ta ji dan darr! Amma ta dake ta ce, "Na sa a raka su guest house". Ma'arouf ya tsura mata ido, ya kasa ko qiftawa, idanun nasa har wani kankancewa suke yi tsabar bacin rai. Ji yake kamar ya fizgo ta daga gadon ya jefa ta waje ta taga. Ya bude baki zai yi magana ya kasa. Babban burinsa a rayuwa kada ya daki mace har karshen rayuwarsa. Albarkacin uwar data kawoshi duniya ta raineshi har ya zama abinda ya zama. Amma a yau ba abin da yake son yi fiye da hakan. Hannayensa biyu har kyarma suke yi cike da kaikayi suna so ya basu damar yin abinda suke so, bai san sanda ya isa inda ta ke ba ya damko wuyan rigarta ya mikar da ita ba. Idanuwan Laila duk suka yo waje, domin shaka ce ba ta wasa ba, ta namijin da ya amsa sunan namiji. Saki uku yake so ya furta mata yana danne harshensa, yana lallashin zuciyarsa. Laila ta soma kakari tana rokonsa ya cika ta, muryar ba ta fita. "Kada ka yi kisa Ma'arouf, a'ah!" Wani bangare na zuciyarsa ke lallashinsa. Ya cika ta ta fadi a wajen rikicaaaa! Rike da wuyanta tana ta tari kamar wadda ta shaki tiyagas don wahala. Da sauri ya juya ya fita daga dakin, shi bai ma san ina ne hanyar sassan bakin ba. Jefa kafa kawai yakeyi, dafya fara nutsuwa ne ya kira Amos a waya yace ya zo ya raka shi inda aka kai mahaifiyarsa. Hajiya da Ameena sun dade da yin bacci, har sun soma minshari. Sun kashe fitilu baccin gajiya kawai suke yi. Ya kai hannu ya kunna wutar dakin, nan da nan dakin ya gauraye da haske. Da sauri ya isa gaban gadon ya russuna da gwiwoyinsa ya kama hannun Amina yana tattaba ta kamar wani abin ne ya same su na cutarwa. Hajiya ta bude ido ta ganshi cikin wani yanayi da ta kasa fassarawa. Ya kuma ki bude baki ya yi magana, so yake ya ce da ita. "Wace irin kara da kiyashi ki ka aura min haka Hajiya? Wace irin annobar mace ce haka ki ka kawo min cikin rayuwa ta?" Hajiya ta yi gyaran murya, don ta lura ba zai yi magana ba. Yana cikin bacin rai bayyananne wanda ta gane ba na komai ba ne, na masaukin da aka yi musu ne. Ta ce, "Ka zo ka kunna mana haske muna cikin bacci, ko me ye ba za a yi masa lamunin gobe da safe ba? Kai kanka a gajiye ka ke, ka je ka kwanta a bar wa gobe in Allah ya kai mu". Sai kawai ya mike ya ciccibi Amina, ya kuma samu bakinsa ya bude. "Taso Hajiya mu je". "Mu je ina a wannan dare? Ka yi hakuri ka barmu mu kwanta tunda dare ya yi, ni gobe zan juya Ji-kas, amma ina tantamar in ba da Amina zan juya ba. Don ni ban ga wata likita da ka yi min zance ba". "Amma kin ce min kwana uku za ki yi, me ya sa ki ka canza shawara? In ba ranki ne ya baci ba Hajiya, don Allah ki taso mu je na ajiye ku a inda hankalina zai kwanta. Ina jin motsinku. Kwata-kwata wannan ginin na baki ne, bakin ma na nesa". "Ai mu ma bakin ne, don kuwa gobe za mu juya". Ya gama fahimtar bacin ran Hajiya a kan kamilalliyar fuskarta. "Idan har za ki juya gobe Hajiya, sai dai in tare za ku juya Ji-kas". Hajiya ta tashi ta zauna sosai ta gyara zaninta. "Ni da wa kenan?" "Ita waccan yarinyar da ki ka aura mini. Ai na gaya miki auren ya yi gaggawa, daga ni har ke har Baba Liman ba mu san halinta ba, amma da yake kuna taya ni son siyasar da nake so ku ka kasa yin bincike akanta.... Don haka dukkanmu ke da laifi wajen aurenta...?." "Ya isa! Ya isa!!" Hajiya ta dakatar da shi, akalla ta samu ya amayar mata da bacin ransa yau. Ta ji sanyi a ranta, shi ma ko yayane ta san ya ji sanyi. "Ka yi mata uzuri, cikin mulki ta fada. Kuma ni ban raina inda aka ajiye ni ba. Me ye laifin wajen nan saboda Allah? Yi hakuri ka yafe mata in don ni ce, don Allah don Annabi". "Zan yafe mata only in kin taso mun koma cikin gida....". "Ba ka tausaya min doguwar tafiyar nan? Da nisa fa!" "Hajiya bari to in kai Amina sai in dawo in dauke ki". Hajiya ta yi dariya tana saukowa daga gadon, tasan kadan da aikinsa. "Me ya yi zafi? Mu je in hakan shi ne kwanciyar hankalinka. Amma tafiya ta gobe ba makawa, kuma tare da Amina". Bai ce komai ba, farin cikinsa Hajiya ta huce tunda har ta yarda ta biyo shi. Ya santa in ta yi fushi ba dama, shi kansa ya yi mamakin rashin daukar zafinta a kan Laila, don ba ta daukar raini. A ransa ya ce, 'Watakila don ita ta kawo abarta ne, ba ta da bakin korafi'. Dakin da ke kallon nasa ya bude musu. Wani hadadden bedroom na tashin hankali, komai da ke cikin dakin 'Royal colour' ne. Don haka da ya kunna fitilar dakin ya wadata da haske, sai ya zama kamar dakin shugaban kasa. Asali dakin shi ne nasa, guda biyu ne
Chapter 9 · 0% Book details