← Book details Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 20

Sashe 13

Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce, tafiya zan yi, da ma don ke na zauna zan yi sati daya, amma ko yanzu ina iya tafiya wallahi ba ni da haufi a kanki Likita Amina". Amina ta yi murmushi, irin murmushin nan na jin dadin da dan Adam ke samu a zuciyarsa in an yi masa shaida ta gari. Aka kira shi a waya, ya daga ya wuce yana magana, bai ce komai ba a kan ba ta lambar wayar. Ji ya yi kamar wanda ya kira wayar ya taimake shi. Hajiya akwai rigima. Ya fada a ransa. Su duka basu san tanada lambar tasa cikin wayar ta ba. Da hannayenta biyu ta soma 'messaging' jikin Ameena, hankalinta ya tattara sosai a kanta, tana jin Hajiya na mata magana cikin lallashi. "Ki saki jikinki ki dinga gaya masa komai. Na ga alama kunyarki na da yawa. In aka ce abu lalura ai ta kori komai. Sannan mutum ne shi mai saukin kai. Idan kin ce ni ce Jakadiyarku idan na tafi ya ya za ki yi?" Amina ta ce, "Toh". Haka suka wuni tana ta bai wa Ameena treatments kala-kala. Sai da Hajiya ta matsanta mata sannan ta ci abinci, shi ma kadan, don hankalinta na kan Amina. Hirar ma ba sosai suke yi ba, Hajiya tana ta laziminta hankalinta kwance. Ba don ya roke ta da Allah da Annabi ba a kan ta cika satin yadda suka yi alkawari, da tafiya za ta yi. Haka nan ta samu zuciyar ta da yarda da Amina dari-bisa-dari, kaunarta ta lullube zuciyarta ganin yadda ta ke kula da Ameena bilhakki kamar ita ta haife ta. (Aka ce Mai Da wawa)! Da daddare da za su kwanta, ba yadda Hajiya ba ta yi da ita ba su kwanta a gadon su uku su sanya Ameena a tsakiya, Dr. Amina ta ki ta amince. Kan resting chair ta jefa filo ta kwanta, sai bacci. Washegari da safe kamar yadda ya saba in dai Hajiya na gidansa tun Aisha na raye kafin ya fita office sai ya duba ta, ya ga lafiyarta, ya tambayi ko suna da bukatar wani abu, to haka anan ma, in ya dawo kafin ya shiga nasa dakin ko na Laila sai ya ga Hajiya da Amina. To haka yau ma, da safen ya shigo suka karya kumallo shi da Hajiyarsa, ita tana can gefe tana bai wa Ameena quaker oat da ta dama mata. Hajiya tayi-tayi ta zo su ci abincin tare, ta ce ita ba ta jin yunwa. A ranta ta ce, 'banda abin Hajiya ina ni ina cin abinci akushi guda da Ma'arouf Ji-kas? In al'umma ta ji ai sai a sa ni a jarida'. Suna cin abincin shi da Hajiya jefi-jefi suna hira, ta gama ba ta 'oat' din ta shiga ba ta magunguna, ta gama ta yi mata allurai amma ba ta yi kuka ba saboda rashin zafin hannun Amina. Ta fiddo kayan aikinta ta soma yi mata thermotherapy . Ta gama ta koma 'electrotherapy' abin da bahaushe ke ce ma 'gashi', duk yana kallonta yana mamaki cikin ransa, karamar yarinya haka da ba ta fi shekaru ashirin da biyar ba ta samu ilmi mai kyau (at a very young age). In tana aikinta bata tunanin komai, don haka ta manta ma yana dakin, gabadaya hankalinta yana kan Ameena. Don haka ba ta san me suke cewa ba shi da uwarsa. Kwanansu biyar kenan, jibi Hajiya za ta koma Ji-kas, Amina har ba ta so ta tuna tafiyar dattijuwar nan ma abociyar ibada, hikima da tawali u. Ba karamin sabo suka yi cikin 'yan kwanakin nan ba, kamar uwa da 'ya, haka suka koma. Ana i-gobe Hajiya za ta tafi, ya shigo da azahar bayan ya fito daga office kenan wani abin farin ciki ya faru. Ameena na kan cinyar Dr. Amina tana mata messaging yana shigowa kawai sai ji suka yi Ameena ta bude baki ta ce Daddy! A sukwane ya isa gare ta, ya kama hannunta, farin ciki fal fuskarsa. Ga bakin da ya sake karkacewa bayan tafiyar masu maganin gargajiya ya koma daidai tun sanda ta soma ba ta thermotherapy . Ya dauki yarinyar daga cinyar Dr. Amina ya rungume ta. Idanunsa har kwallah suka tara, Hajiya sai hamdala ta ke yau Amina tayi magana baki ya bude. Amina ta sake cewa Daddy ina Mama? Ya kawar da kai daga gare ta da sauri yana mai kara rungume yarinyar a jikinsa. Hajiya ce ta samu kwarin gwiwar ce da ita, Amina, Mama bata nan, tayi tafiya mai nisa, ga wata Maman nan Daddy ya samo miki Da sauri shi da Dr. Amina suka dubi juna jin furucin Hajiya. Amina tayi nasarar ganin kwallar data cika idonsa ta kasa zubowa, sai ta ji tausayin su shi da yar tasa ya lullube ta. Ta maida kanta kasa ta saddar. Hajiya tayi murmushi ta ce. An godewa Allah, an godewa Dr. Amina! Hajiya ta dube shi, "Matar gidannan yaushe zata dawo ne? Tun washegarin zuwana tace min za taje umrah har yau ban kara jin duriyar ta ba? Cike da mamakin Laila na yadda ta iya yin wadannan kwanakin ba tareda ta kira Hajiya a waya ba alhalin ta san tana cikin gidan, ya jinjina kai. Bai dai ce komai ba, rashin mutuncin na Laila ya isa, a sanyaye ya ce da Hajiyar, "Na ke jin jibi za ta dawo, sati daya tace zata yi". Hajiyar bata dauka da zafi ba ita tace. "Allah ya kai mu, Allah ya dawo da ita lafiya yasa ayi karbabbiya, ni kuma tafiya gobe. Ya ya an gama shirya dakin nasu da kicin din?" "An gama tuntuni". "In ta dawo sai ka yi mata bayanin wace ce Dr. Amina da dalilin zamanta tare da ku. Hakkinta ne ka yi mata wannan bayanin tunda gidanta ne. A kare min mutuncin diya ta a gidan nan, ga ta nan amana na baku kai da matarka, in kuma aka yi miki ba daidai ba Amina ki kira ni ki gaya min, wayata kullum a bude take". Amina ta yi murmushi kawai. "Tattara kayan mu je na kai ku dakin naku". Dakin da aka shirya wa Ameena da 'patient' dinta Ameena yana nan a down-stairs na ginin da Ma'arouf da iyalinsa ke ciki. Wato wata matattakala ce zaka taka guda shidda ka sakko zaka tadda wani katon katafaren falon wanda ya kunshi dakunan da aka shiryawa yara, wanda duk ya fisu girma da kayatuwa shi Ma arouf ya zabar musu da kicin a cikinsa kamar yadda ta bukata. Hajiya ta yi musu addu'a, a washegari Akilu ya dauke ta suka yi Ji-kas. Sauki ya nuna sosai a jikin yarinya Ameena Ma'arouf cikin sati daya kacal, har wata 'yar kiba ta yi, kumatun nan ya yi luwai-luwai abin sha'awa, in ta gaji da kwanciya Amina kan sa ta a wheel-chair ta dan zazzaga falon da ita. Lokaci zuwa lokaci tana yi mata messaging don samar mata pain-relief akai-akai, kowanne treatment da lokacin da ta ware masa. Ranar juma'a ya kama za ta tafi gida, a ranar ne Laila ta dawo daga Saudiyya, abin da Ma'arouf bai sani ba shi ne, Dubai ta je ba Saudiyyah ba. Laila taje ganin likita ne a duba mata me ya hana ta samun ciki. Sun duba ta, sun ba ta magunguna da za su taimaka mata ta yi conceiving sakamakon mahaifarta mai rauni ce. Ta san in ta gaya masa gaskiyar inda za ta je ba zai lamunta ba, shi a kan karan-kansa ba ya fita (abroad) balle ya yarjewa iyalinsa, patriotism dinsa bai yarda da wannan ba. A ganin Ma arouf Ji-kas, duk abinda ake nema a kasar waje akwai shi a Nigeria mu muke down-grading albarkar da Allah ya yiwa kasarmu mai dimbin albarka. Sannan abubuwan da ke kansa sun fi karfin ya tsaya yana mata bin diddigi, ta san Saudi-Arabia shi ne waje na karshe da in ta ce za ta je ba zai hana ba. Shi ya sa ta yi masa wannan karyar. Amina ta shirya tana jiran shi ya zo ya yi mata umarnin tafiya, amma in ta daga ido ta dubi Ameena sai ta ji kamar ta fasa tafiyar saboda tausayin yarinyar da ta ke ji. Sun fara shakuwa sosai, domin zuwa yanzu Ameena Ma'arouf ta soma dawowa hayyacinta, hannunta na dama da kafarta ta dama su ne ba ta iya motsa su, kamar ba a jikinta suke ba. Tana magana jefi-jefi tana kiranta Aunty". Ba ta gaya mata za ta je gida ba, don kada ta damu. Ta gama yi mata duk abin da za ta yi mata yau. Har karfe sha biyu na rana bai shigo ba kamar yadda ya saba. Ta matsu ta isa ga Goggonta ta ga halin da ta ke ciki. Ga shi ta sa a ranta ita fa ba za ta iya kiran Ma'arouf Ji-kas ba, saboda kwarjinin da yake mata. Yana da wata irin haiba da ba kowa zai iya tunkararsa da magana kai tsaye ba. Ta zauna da jakarta a gefe ta yi tagumi tana kallon Ameena da ke bacci bisa lallausan gadonta. Kaunar yarinyar na kara mamaye mata zuciya, jira ta ke ya zo ta ba shi prescription na magungunan Ameena da yadda za a dinga yi mata messaging kafin ta dawo. Ba shi ya shigo ba sai karfe daya na rana. Ya shigo a gurguje don lokacin masallaci yayi, da sallama a bakinsa hadi da dan murmushi a kan fuskarsa, ya hada hannayensa biyu ya kai habar sa irin ban hakurin nan na Indiyawa. "Afuwan, jama a suka tsaida ni, muna tattauna wani muhimmin abu ne". Kanta a kasa ta ce, "Babu komai". Wannan karon ma ba ta yarda sun hada ido ba. Kanta ya na kasa. Ya zauna kadan a kan wani (center-table) da ke gefe. "Ya ya ku ka wuni?" "Fine. Alhamdulillah". Duk sai suka yi shiru. Matukar takura Amina ji ta ke ta takura, kamar ta mike ta ruga a guje ko ta roki kasar ta tsage ta shige. Ba su taba zama su biyu ba sabida koyaushe Hajiyarsa na shiga tsakaninsu ta zama Jakadiya, ga shi yanzu ta tafi, ta barta da wannan giant His Excellency Ma'arouf Habibou Ji-kas, Baban Amina. Wani mutum guda daya jallin jal a duniya da ko sunansa ba ta iya
Chapter 13 · 0% Book details