Sashe 4
Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Laila, na yaran da ma can na Amina ne tun mahaifiyarta na raye, yanzu da ta baro gadon asibiti ma nan aka dawo da ita. Ya rufe dakin A isha. Laila ta daga ido tana kallon irin tsarin da aka yi wa dakin. Daki ne na 'yan gata wanda aka kashewa dukiya ba kadan ba. Kamar na 'ya'yan Turawa, ga wani gadon yara mai matattakala ga (teddy Bears) nan da can, ga (computer game), ga duk wani nau'in wani abu da yaro mai gata zai bukata. Fentin dakin da komai da ke cikinsa (light blue and pink), toilet din kuwa ba a magana don kyau da ban sha'awa ko dakin dan shugaban kasa sai haka. Ta jinjina kai, wani bakin ciki ya kule ta. Ta sa hannu ta shafi cikinta, ita har yau ko kyankyaso bai shiga ba, da ta kawo su nan su ma ta rage takaici. Ta daga kai ta dubi Amina a gadonta tana kwance tana kallonta. Kyakkyawar yarinya mai kama da ubanta kamar ya yi kaki ya tofar. Tun safe ko ruwan shayi ba ta bata ba, ba ta canza mata (pampers) ba, ba ta dauko ta ta sanya ta a (wheel-chair) da Babanta ke sanya ta a ciki ya dan zagaya harabar gidan da ita ba, ko ta samu canjin iska. Ta karasa gaban yarinyar tana kare mata kallo a yatsine. "Ni ba zan iya wahalar da ubanki ke yi da ke ba, kakarki kanta ta gaji ta gudu shi ne ni za a hada ni da jangwam. Tashi ni su zo su wanke miki kashi". Ta danna kararrawar ma'aikatan gidan, nan da nan mutum biyu suka zo. Samari ne guda biyu masu share-share. "Ku dauke ta ku kaita toilet ku yi mata wanka, ku cire mata (pampers) din tun dakin bai soma wari ba". Matasan biyu suka kalli juna kamar masu yin shawara, ta galla musu harara. "Ko ba za ku yi ba ne?" Da sauri suka ciccibo yarinyar, daya ya riko kai, daya ya riko kafafu suka yi toilet da ita, suka tube ta suka cire pampers za su soma wanke ta. Kamar an jefo shi, Ma'arouf ne ya shigo babu zato babu tsammani. Ya yi (missing flight) dinsa ne mai zuwa Abuja ba da son ransa ba. Ashe da rabon zai ga bacin ran da bai taba shiga kwatankwacin sa ba. Cikin matsanancin mamaki ya dubi Laila. Muryar sa kamar ta wanda zai fashe da kuka. "Maza balagaggu ki ka sa su tsiraita 'ya ta haka Laila? 'Yar tawa kwalli daya? Laila ko auren kiyayya ki ka yi da ni ba za ki iya taimakawa mara lafiya marainiya ba? Kina nufin su sanya hannu a (private part) din diya ta? Ban taba dukan mace ba, bana fata in fara a kanki. Ki je duniya ce, kuma in gaya miki wannan yarinyar ta fi min komai da duk abin da na mallaka a duniyar baki dayanta. Ke ma mace ce, kuma za ki haifa, ba ki san ya ya kaddara za ta yi da abin da ki ka haifa ba kina raye ko ba kya raye". Kallo daya ya yi wa ma'aikatan suka saki (pampers) din da suke cirewa suka yi waje cike da addu'a a cikin zukatansu, kada Allah ya sa wannan ya zamo sanadin hanyar abincinsu. Su ma sun ji umarnin da aikin da aka sanya sun 'odd' to amma su me ye laifinsu? Salin-alin suka fice. Laila ta rasa abin cewa, ba ta taba tsammanin zai dawo ba sai bayan kwana uku kamar yadda sukayi dashi. Ta kulla a zuciyarta ko 'cangal' ba za ta yi wa yarinyar ba har ya dawo. Maganganun da ya gasa mata ba su ta zata ba, ta fi zaton dan banzan duka daga gare shi in tayi la akari da yadda ta lura yana son yarinyar. Da sauri ya nade hannun riga ya wanke Amina, da kansa ya yi mata wanka da soso da sabulu mai kamshi, ya nado ta cikin shawul ya fito da ita. Har zuwa lokacin Laila a tsaye ta ke bakin (toilet) ta kasa ko kwakkwaran motsi, tana kallo ya shafe Amina da basilin, ya sanya mata sabuwar (pampers) da sababbin riga da siket masu kyau, sannan ya yi waya kicin a kawo masa 'tea' da 'pancake'. Da kansa ya rika bai wa Amina har ta koshi ta ture. Jiki ba kwari Laila ta wuce, don ganin yadda ya baiwa banza ajiyar ta (ya yi kamar babu ita a dakin). Ya sumbaci Ameena a goshinta ya mayar da ita ya kwantar. Ya fito ya zauna a daya daga ni'imtattun kujerun falon. Ya kai hannun damansa ya dafe kansa dake sara masa, ji ya yi dan son da ya soma yi wa Lailar na decreasing gradually (raguwa a hankali). Zufa ta shiga karyo mishi da ya tuna kalamai na karshe na uwar Ameena. "Ka kara kula da Ameena, ba don na raina kulawarka gare ta ba. She will need extra more....!". "Yes! She need extra more A isha, kuma in har ina raye, sannan kudi suna da amfani za ta samu kulawa Aisha. Da gaske kula da 'ya mace sai mace. Na lura matar nan son kashe min Amina ta yi ko abinci ba ta bata ba har karfe daya na rana. Kuma ta sa maza su tozarta ta, ba don Allah ya dawo da ni ba!". Ya san muddin ya gaya wa Hajiyan Ji-Kas wannan abin, cewa za ta yi za ta dawo ta kula da jikarta, bayan yanzun ta fara samun nutsuwa a gidan mijinta. Hankalinta ya tsaya wuri guda, shi shaida ne akan hakan don ko jiya ta kira shi tace ya shirya musu tafiya umrah itada Baba Liman. Zai yi (finding solution) da kansa. Babu wanda ya fado masa a rai a wannan lokacin sai abokinsa Dr. Usman Turaki. Classmate dinsa ne, tare suka yi sakandire a Science College Dawakin Tofa. Sun shaku sosai, yanayin karatu ya raba su. Kowa da jami'ar da ya wuce da fannin da ya zaba. A take ya zakulo lambar Dr. Turaki ya danna masa kira. Ta jima tana kara kafin matarsa ta daga. Abin da ta ce shi ne, "Doctor is on call. A gida ya bar wayarsa". "O.k please da ya dawo ki ce ya kira ni da wannan number din, Ma'arouf Ji-kas ne". "Insha Allahu". Ta kara da cewa, "Sai Ji-kas, insha Allahu sai Ji-kas!". Murmushi ya yi, wanda bai shirya yinsa ba, wato matan aure ma ba a barsu a baya ba. "Na gode Madame. A gaida yara". "Za su ji. Allah Ya tashi kafadun Amina!!!". Ji ya yi kamar ta yi masa addu'ar Allah ya sanya shi a aljannah. Wato komai na dan siyasa ba ya buya, kamar kasawa ake a faranti Anna tallata wa, kowa ya san matarsa ta lalle ta rasu, kuma yana da 'ya mara lafiya. **** Dr. Turaki na komawa gida, abinci kawai matarsa Zainab ta bari ya ci, ta kasa bari ya yi wanka kafin ta isar da sakon Ji-kas. Amma ta boye azarbabi da murnarta na ta yi magana da Ji-kas, tauraron taurarin matasa na birnin Bauchin Yakubu. "Zan kira shi gobe da na shiga office". "Haba-Haba kai kuwa Baban Aadil, ka kira shi yanzu mana, mu ji mene ne, ka sani ko kujerar Makkah ce?" Ya tuntsire da dariya. "Zainab mai idon cin naira. Ki bari Allah ya ba shi kujerar, makkah kin je kin dawo insha Allahu". Ita dai Zainab ba haka ta so ba, ta so ya kira shi tana zaune ta ji kwaf! Ko samu ne. Tunda wasu mazan al adarsu ne boye samu wa matan su. Kamar yadda ya ce da matarsa, washegari yana shiga ofis ya bude tagogin ofishinsa, iska ta wadata, kan kujerarsa ya koma ya zauna. Ji-kas din ya fara kira. A lokacin yana bai wa Amina (golden morn) a kofi da cokali, ya dakata ya daga kiran Turakin. "Sai yanzu ka ga damar kira na? Na san tun jiya an gaya maka sakona. Har yanzu kana nan da halinka da na sani Usman?" Dariya ya yi, "tuba nake Yaa Maulaya!". Shi ma murmushin ya yi. Usman ya san ba ya son Yaa Maulaya din nan da mates dinsu ke gaya masa sabida ustazancinsa, ba ta kan wannan yake ba yanzu, don haka kai tsaye ya zarce da gaya masa makasudin kiran. "A kan 'yarka Amina ne. Mun bar gadon asibiti don dukkaninmu ba za mu iya ba, ni da Hajiya ta. Saboda wasu muhimman uzurirrika musamman ni da yanayin rayuwa ta ba na tsuguno ba ne a wuri guda. Don haka ina son hiring professional physiotherapist da za ta ci gaba da baiwa Amina (treatment) a gida, da kula da ita da komai nata bilhaqqi. Za ta baro asibiti ta zauna da Amina a gida, ta ci gaba da kula da ita tsawon shekara daya mu ga abinda Allah zai yi. Zan ninka mata albashin da ta ke karba a asibiti sau hudu a kowanne wata. Sai dai Turaki ba kowacce ba, shi ya sa ma na biyo ta kanka, ban bi ta kan likitocin Amina ba, ina son wadda akwai sanayya ta sosai a tsakaninku, ka yarda da ita, ka yarda da amanarta da ikhlasi. Mai tausayi da jin kai. Mata tsoro suke ba ni Turaki, in kana da kudin da za ka ba su babu mai zama da kai tsakani da Allah. Yau na firgita, na tsorata da al'amarin mata yadda ba ka zato Usman. Sun kuma karya min zuciya, sun kara sa ni kewar Asha. Mata irinta tsiraru ne a cikin al'umma". Dr. Turaki ya ja numfashi, zai so ya tambayi abokin nasa abinda ya firgita shi da matan, har suka yi breaking sai dinsa haka, sai ya ga hakan ba huruminsa bane. Babu wadda ta zo masa a rai sai likitar da ya raina da hannunsa, ya kwashe shekaru tare da ita, ya lakanci dukkan halayenta; Dr. Amina Mas'ud Shira. Dukkan suffofin da Ma'arouf ke so 'proffessional' din ta kasance da su Amina ce ta mallake su, a dai likitocin mataccen kashi da ya sani a duniya. Amma kafin nan, sai ya ce da abokin nasa, "To me zai hana ka kara aure Ma arouf? In ta gidan ta na da matsala?" Cikin girgiza kai kamar Turakin na