← Book details Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 20

Sashe 16

Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Sai wane hange kike dashi? Don na lura bayan ilmin likitanci kinada ilmin zamantakewa da siyasa (sociology and political science). Ina barar karin idea Amina tayi dariya Your Excellency har nawa abin yake? Karambani ne kawai irin nawa koko ince gyara ne nayi muku, tunani na ne kawai nayi sharing da kai, wanda na tabbata zai zo daya dana jama a da yawa masu bibiyar ayyukan ku. Yace naji, ina son karin karambanin domin wannan din an yaba dashi sosai, mun kara samun magoya baya a dalilinsa fiye da zaton ki. So hurry up! Lokutana a kididdige suke Amina ta nisa Mai girma Gwamna a daga darajar albashin malaman makaranta, don Allah. A karawa iyayenmu yan pansho wani tagomashin, duba da cewa basu da wata hanya sai wannan ga tarin iyali, sunyi rauni basu da karfin nema ta wata hanyar karfin. Da wuya ka samu malamin makarantar dake da motar kansa wadda zai ce sana ar koyarwa ta samar da ita gareshi. Shiyasa kowa ya raina sana ar, matasa ke gudunta. A kalla ace an fitar da wani tsari da za a basu motoci nasu na kansu a dinga cire kaso daya bisa uku daga albashin su tsayin wasu adadin shekaru da za a kidaya zai ishe su gama biyan bashin. In akayi haka an taimake su. Fresh graduates zasu daina gudun koyarwa a jihar mu kuma zasu kara himma. Kayi amfani da scientific management theory wadda Frederick Winslow Taylor ya samar wajen kara himmar malaman makaranta wadda aka fi sani da Taylorism. Har ila yau, ka hada da human relation movement din ban ce a barta ba (Elton Mayor) . A dinga sanya al amuran education a gaba-gaba ba infrastructure and tourism kadai ba. Duk da nasan tourism din shine fuskarmu, amma malamai sune tushe kuma kashin bayan kowacce al umma. A dabbaqa muhimmancin ilmi kafin komai. Wannan tunanina ne amma fa. Kowa yanada damar yin nasa hangen, wannan na Amina ne Ya cure yatsunsa cikin na juna ya kaisu habar sa yana cigaba da kallonta, wani zubin ya girgiza kai wani zubin yayi murmushi har ta gama. Hatta yadda take zaro kalaman tana fadin su sala-sala abin a tsaya a saurare ta ne, banda sanyin muryarta da zazzaqan turancin ta. Abinda yace a karshe kawai shine. Noted! Daga ranar Amina ta zama wata mai baiwa gwamna shawara mai zaman kanta a cikin gida. Banbancin ta da (special advisers) shine ita bata da ofis kuma ba a bata albashi. In ya dawo ya shigo ganin Amina su kan tattauna al amuran siyasar sa. In al amura sun sha kansa sun sanya shi cikin damuwa sai ya samu kansa da gayawa Dr. Amina. Abin mamaki sai ta bashi mafita, wadda in ya bi sai ya ga ta bille dashi. Sannu a hankali shakuwa mai tsanani ta fara shiga tsakaninsu. Ma arouf ya soma jin Ameena sosai a ransa da ilahirin gangar jikinsa. In fita ya yi, Allah-Allah yake ya dawo gida ya tadda Ameena da Ameena. Sosai al amarin ya sauya salo a bangaren Ma arouf Jikas. Jin Amina yake wata mutum mai amfani da muhimmanci a gareshi. Watanni na nausawa al amarin na kara rikide masa. Tun Laila bata damuwa da yawan kebewarsu har ta soma darsawa zuciyarta kishi da zargi. Saboda in ya dawo kafin ya shiga ko ina a gidan sai ya fito daga dakin su, in zai fita su yake fara gani, al amarin nan ya soma damun ta, zaman Ameena tare dasu duk da hutu ne a gareta ya soma ci mata tuwo a kwarya. Ta fannin Ameena, bazan iya cewa ba. Kasancewar ta wata mace data dauki soyayya ta ninke a takarda ta adana a fayal ta sanya a karkashin gado, bata santa ba, bata mafarkin yin ta, don har gobe bata ga namijin da yayi daidai da rayuwar ta ba. A ganinta the best is yet to come! Duk da alkawarin da ta yiwa Goggo, don haka ga Amina, a yanzu ko zatayi aure zatayi ne domin Goggo, don farantawa Goggo. Bata taba darsawa ranta komai akan Ma arouf ba don hankalinta ma bai taba yin nisan kiwon kawowa ranta miji kamarsa ba. Balle tayi wani tunani shigen hakan akansa. Don haka mu amalar data ke yi dashi na shugaba da ma aikacinsa ne, (Oga, Boss, Ubangida da yaron sa) inji hausawa. Har gobe wannan girman nasa da kima da take gani yana nan cikin idanunta sai ma abinda ya karu. Saidai zuwa halin da ake ciki yanzu ta rage jin nauyin sa. Tunda yanzun tana iya tunkararsa da magana face to face suyi magana mai tsayi da ma ana. Watannin ta bakwai kenan tareda su tana aiki a gidan gwamnati ba tareda ta taba karbar ko sisi ba, bata kuma taba damuwa ba. Damuwar ta yanzun tana ga chanjin dake akwai cikin kwayar idanun Ogan ta.....!!!
Chapter 16 · 0% Book details