Sashe 10
Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
nasa, ya barshi ne ya dauki smart din (British bedroom) don ba ya son abu mai daukar idanu. Hajiya ta ce, "A wannan ranar za mu yi bacci?" Ya karasa ya shimfidar da Amina a tsakiyar luntsumemen gadon, ya danna wani dan abu jikin gadon, fitilu shudaye na bacci suka maye gurbin masu hasken. Hajiya ta karasa ta kwanta kusa da Amina. Sai yanzu ne ya ji hankalinsa ya kwanta, wata nutsuwa ta shige shi. Suka yi sallama da Hajiya, ya juya ya fita ya jawo musu kofar. Ya shige nasa dakin ya rufe da mukulli, maimakon kwanciya bacci, wanka ya yi sannan ya daura alwala ya yi nafilfili masu dama, ya shigar da bukatunsa da godiyarsa ga Allah a bisa wannan jagoranci da Ya ba shi, ba don ya fi kowa ba sai don Ya zabe shi. Ya roke shi Ya ba shi ikon sauke hakkin talakawa da ke kansa, Ya ba wa Amina lafiya, Ya kara wa iyayensa tsawon rai su ci gaba da zama sanyin idaniyarsa, kuma fitilarsa masu haska masa rayuwa da ankarar da shi a duk lokacin da zai yi kuskure, da kauna ta fisabilillahi gare shi, wadda babu algus ko tasirin abin hannunsa a cikinta wannan sai iyaye. Ya yarda wanda duk zai so shi, ko ya girmama shi, ko ya rabe shi a wannan lokacin zai yi ne saboda dukiyar al'umma da ke hannunsa, ban da Hajiya da Baba. Ya ya kuwa za a yi ya bari wani ya nuna su da dan yatsa bai karya dan yatsan ba? Balle wata banza Laila, wadda ba don Hajiya ta nema mata afuwa da kanta ba, yau sai ta bar gidan gwamnati inya so a ce ya yi auren siyasar. Sai me? Ta ci albarkacin wadda ta fi kowa alfarma a rayuwarsa. Da wadannan tunane-tunanen barci ya dauke shi, amma rashin samun barcin da wuri bai sa ya kasa tashi sallar asuba a kan lokaci ba. Ma arouf Ji-kas kenan. ****