Sashe 18
Sanadin Kenan Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana nazari. Daga baya kuma ta fito ta gaya wa Goggo da ke kwabin meatpie a madafi (kicin). Goggo ta ce, "Ai sai ki yi sauri ki shirya Allah ya sa yarinyar lafiya ta ke". Nima tunanina kenan Goggo Tuni ta yi wankanta na safe dama, ta soma tattara 'yan komatsanta cikin 'handbag' dinta da ta zo da ita, don yanzu bata dauko babbar jakarta in za ta zo, suna maganar suka ji dirin mota a kofar gida. Ilya baya nan daga ita sai Talatu da Goggo, suka yi sallama ita da Goggo da Talatu ta fito. Akilu ya bude mata kofar motar ta shiga, kullum bata gajiya da rokonsa kan ya daina fitowa ya bude mata kofa, amma ya ki bari. Babu inda ake bincikarsu kamar koyaushe har suka tadda ginin da masu gidan ke ciki wanda shine a can karshen gidan. Dakinsu ta nufa kai tsaye da jakarta a hannu, ba kowa a dakin, ta karasa ta aje jakar gefe ta zauna kan resting chair tana taraddadi Allah yasa Ameena lafiya take. Ya yi knocking hade da sallama Amina ta amsa, ya murda kofar sannan ya turo Ameena cikin kekenta suka shigo tare. Ta daga kai ta dube shi, idan har ba gizo idonta yake mata ba har wata yar rama baban Amina yayi a idanunta cikin kwanaki biyun data yi bata ganshi ba. Tace a ranta watakila shine baya jin dadi. Ta karasa da sauri tana tattaba jikin little sai ta ji ya ce, "Ki yi hakuri, lafiya kalau fa, na sa an dauko ki da wuri, duk da nasan ba mu kadai ke da bukatar ki ba akwai pigeons (tantabarunki), wasu abubuwan yau na kasa ne, I m weak today!". Ta yi murmushi, "Babu damuwa. Tunda Ameena lafiya take. An ba ta magungunanta na safe?" "Na manta ban bata ba, rashinki a gidan ya dan maida ni upset, ga su ki ba ta". Ya mika mata ledar magungunan. Ta karba da sauri, ba tareda ta yiwa maganarsa wata fassara ba, bata dube shi ba take magana, tana kokarin kwance ledar magungunan hannunta har rawa yake. "Amma ka ga lokacin shan ya wuce ko? Ba haka muka yi da kai ba, kafin in yarda in fara bar maka amanar Amina". Ya yi murmushi, ganin yadda ta ke maganar kamar mai yi wa kaninta fada, ba karamin jin dadin maganganunta ya yi ba masu nuna kulawarta a kan Ameena, don haka cikin kwantaccen sauti ya ce, "Allah ya huci zuciyar Dr. Amina. Amma ina yin kokari fa, na cancanci a nuna appreciation ga kokarina, kula da Da sai uwarsa, da wanne zan ji? Ni ne messaging, ni ne ba da abinci a baki, ni ne amsa tambayoyin Amina a kan ina ki ka je, ni ne wanka da canza diapers, nine bada magani. Ni ne zagaye da yar ki a wheel chair, sannan gidan ya zama wani irin wawakeke (very wide) ba tareda ke ba. Dr. Amina, kin shaci fili cikin rayuwarmu da yawa cikin dan lokaci kalilan. Ban gane hakan ba sai a karshen satinnan da kika tafi kika barmu, gidan ya zamo incomplete. Ko mene ne sirrin?" Da sauri ta juya ta dube shi, don ta tabbatar daga inda kalaman data ke ji ke fitowa, tanaso ta amincewa kanta da gaske da Ma'arouf Ji-Kas ta ke magana ko waninsa? Ko kunnuwanta ke jin gizo? Wadannan basu yi kama da kalamansa ba, ba yau ta soma jin zantuttukansa ba these are odd, very different, sunyi nauyi da yawa cikin kunnuwanta, da gaske da Jikas din da fuskarsa ta karade fastoci da akwatunan talabijin da sauran kafofin yada labarai take magana. Shi din ne da gaske, ba wani mai kama dashi ba. Wannan Kyakkyawan Ma arouf din mai wadatar jini a jika, ma abocin kwarjini da cikar zati da kamala. Bata da amsar tambayarsa, batada kowanne sirri. Abin da ta sani kawai shi ne ba zai taba iya yin abin da mace za ta iya ba, kuma ya ce ya ji ya gani ya daukar wa kansa aikin da ba nasa ba, saboda matarsa shafaffiya da mai ce. Anya matar Jikas musulma ce mai zuciyar imani? Tausayin Ameena ya kara kamata. Ta kara jin son Goggonta, tana rokon Allah cikin zuciyarta ya bar mata ita (Goggo) su cigaba da rayuwa tare. Maraici babban kalubale ne ga rayuwar dan adam balle ga karamin yaro, wanda bai gama sanin kansa ba. Shi kuwa me ya yi masa zafi da dole sai ya zauna da wannan matar tasa? Wadda bata tausayawa jininsa kiri-kiri haka? Bai yi kama da ragwayen maza ba, wadanda matan su suka fi karfin su, dole akwai wani boyayyen al'amari cikin auren nasa. Amina ta nisa. taimaka min ka kwantarda ita, zamuyi gashin kashi . Ta gujewa waccan tambayar da ya yi mata kenan, don ba ta da amsarta. Zuciyarta raurawa take, bata taba jin kwatankwacin wadannan maganganun daga kowa ba, don haka she becomes agitated!. Ya ciro Amina daga keken ya kwantar da ita, ya samu wuri daidai kafafunta ya zauna, sai Dr. Ameena ta samu kanta da kasa yin gashin, ta koma wajen zamanta na dindin wato doguwar kujerar hutawa ta zauna, tana juya injin thermotherapy dinta a hannu. Kamar ance da ita ta dago ta dube su, ba kowa Ma arouf ke kallo ba har zuwa lokacin sai ita Ameena. Wani irin sanyi taji jikinta ya yi, ta maida kanta kasa ta sunkuyar. Can saman kanta ta tsinkayi sautinsa, raising pigeons is wonderful, (kiwon tantabaru abune mai ban mamaki) kin bawa Amina saura na Babanta, ina son yin babban kiwone irin naki, ki bani nima, in hada dana Ameena in cigaba da kiwonsu, they are progressing fiyeda tsammaninki Dr. Amina ta dan ciji lebe ta girgiza kai (showing resentment), "gaskiya BABAN ya yi hakuri, I so much love my pigeons! (ina son tantabaru na)". Sai bayan ta fadi hakan ne kuma taji a wani barin na zuciyarta kamar bata kyauta ba a karo na biyu. A zuciyarsa yace musu na biyu . Girgiza kai yayi, cikin mika wuya ga sabuwar rayuwar dake faruwa dashi, baida tsimi bai da dabara face karbar ta da hannu bibbiyu don samun nutsuwar zuciyarsa. Gabadaya jinsa yake a hargitse, wannan halittar dake gabansa, ita kadai zata sa ya samu nutsuwa. Hakan kuma bazai faru ba, ba tareda ya ja ta a jiki ya shiga rayuwarta ba. "Na yi hakuri da account number, ban kara tambaya ba. Yau watanni bakwai zuwa takwas kenan saboda gudun musun ki Dr. Ameena. Ban yi fushi ba, yau ma na sake neman wata alfarmar, a karo na biyu ban dace ba. To ban hakura ba, wannan karon ina so lallai, kuma rabin gabadayansu za ki bani, wato mu raba daidai, a gidan gona ta zan zuba su in hada da na Ameena. Ko saboda ni ba abin tausayi ba ne sai Ameena? Shi ya sa komai na roke ki ba za ki ba ni ba? Shin akwai abin tausayi a duniya ma irina?" Amina Ta dago ta kalle shi, so take ta hango ta inda za aji tausayin mutum kamarsa. Sosai ta ga ya zame mata abin tausayin a fannin da ba ta sani ba, Sai ta ji zuciyarta ta karye. "Kana da mita!". Abinda ta iya cewa kawai kenan. "Kina da tsiwa!". Ya mayar mata. Ta yi dariya har fararen hakoranta suka fito. Lokaci daya ta ji ba Tantabaru ba, za ta iya mallaka masa duk abin da ta mallaka in har hakan zai sa shi farin ciki. Muryarta ta yi kasa sosai a sanda ta ke cewa. "Wane bayani zan yi wa Goggo? Cewa zan kyautar maka da rabin abin da na gada daga mahaifina haka siddan, na rene su shekaru goma sha biyar ban taba baiwa kowa ba? A matsayinka na wa a gare ni zan ce da Goggo?" Murmushi ya yi, ya mike tsaye yana kokarin fita, "Matsayin da ki ka bani shi za ki gaya mata. Well, ban san matsayin da ki ka banin ba. Ba kuma yanzu nake son sani ba. Ni dai ta fanni na ban boye ba na gaya miki, kin shaci fili mai fadi a rayuwarmu ni da Ameena cikin dan lokaci kalilan". Da wannan ya karasa ficewa daga dakin. Amina ta yi dan jim! Na sakanni, sosai ta shiga duhu da maganganun Ma arouf, so take kwakwalwarta ta fassara mata su, sai kuma ta watsar da tunanin ta ci gaba da abin da ke gabanta. Bata son kwadayin sanin fassarar maganganun nasa, da tasirinsu ya katse ta daga abinda takeyi. Kai ita bata barin komai ya shiga cikin aikinta fa. Amma Baban Ameena na son ya kara kansa cikin ayyukanta karfi da yaji, ta hanyar baiwa kwakwalwarta zazzaffan aiki wanda ita ba ta shirya wa hakan ba. Misalin karfe takwas na daren ranar, suna zaune a falonsu shi da Laila, ta ci ado ta kashe dauri kamar mai shirin zuwa gasar sarauniyar kyau. Tana rike da tambulan na gilashi mai garai-garai cike da tataccen inibi mai sanyi, kurba take a hankali kafarta daya akan daya first-lady sosai, ba sai an tambaya ba. Kowannensu da abin da yake yi cikin falon kamar ba ma'aurata ba. Ita kallon talabijin ta ke yi, inda ake nuna ayyukan mijin nata a kananan hukumomi da kauyuka a Bauchi TV, wani alfahari na kara shigarta. Alfaharin cewa she s the only one that owned him. Lokaci zuwa lokaci ta kan yi murmushi. Shi kuwa na'ura mai kwakwalwa ce da takardu fal a gabansa, yana duba tsare-tsaren budget' na sabuwar shekarar da za a shiga wanda ma'aikatar kasafi da tsare-tsare (ministry of budget and planning) ta gwamnatinsa ta tsara ta fitar ta damka masa don ya sa hannu. Ya na dubawa ne a nitse yana gyare-gyare kafin ya sa hannun. Ya dago ya dubi Laila, wadda tunda ta dawo daga tafiyar da tayi ba ta tambaye shi ina little Ameena ba ko ya ya jikinta? Abin fa yana yi masa ciwo ba kadan ba. A ce tsakanin jininka da matar ka babu jin kai babu tausayi balle karah. Haushi ya kama shi ganin yadda ta wani cokalo dauri a gaban goshi, bakin nan ya sha jambaki jajawur ram! Jagira har kusa da kunne fuska ta sha foundation tayi haske kamar rana. Ya